KAMAR yadda ya saba yi a duk shekara, a bana ma Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Ilimin Harsuna na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ya shirya taron ƙara wa juna sani. Taron na bana an shirya shi ne kan abin da ya shafi harshen Hausa.
An buɗe taron a yau tare da taken “Daidaitacciyar Hausa da Ƙa’idojin Rubutu’.
Wannan shi ne karo na 5 da sashen ya shirya taron, wanda Farfesa Ibrahim Muhammad Malumfashi ke jagoranta.
Taron, wanda aka sa za a gudanar da shi daga ranar Alhamis, 14 ga Nuwamba zuwa Lahadi, 17 ga Nuwamba, 2019, an fara gudanar da taron ne a yau Juma’a, 15 ga Nuwamba, 2019 a ɗakin karatu na jami’ar da ke Titin Tafawa Ɓalewa, cikin garin Kaduna.

Dakta Mu’az na Sashen Larabci na KASU ne ya buɗe taron da addu’a da misalin ƙarfe 10:51 na safe. Daga nan sai Malumfashi ya gabatar da jawabin maraba inda kuma ya gabatar da manyan baƙi.
Ya bayyana cewa daga cikin manyan manazartan da aka gayyata har da gogaggen masanin nan a fannin nazarin harshen Hausa mazaunin Ingila, Farfesa Graham Furniss, to amma bai samu damar halarta ba, ya dai aiko da saƙon bada haƙuri.
Daga nan aka buɗe fage, manazarta su ka fantsama cikin gabatar da ƙasidu, waɗanda su na da dama, kuma masu nuni da yadda ake rubutu da Hausa da yadda ƙa’idojin rubutu su ke.
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 1:20 na rana da nufin cewa gobe za a ɗora daga inda aka tsaya.
Manyan malamai da manazartan Hausa da ‘yan siyasa da ɗalibai sun halarci zaman na yau.

Manyan sun haɗa da Farfesa Abdullahi Ashafa, wakilin mataimakin shugaban jami’ar ta KASU, Dakta Aliyu Isa Sulaiman, Farfesa Muhammad Dauda Bagari Azare, Farfesa Hamisu Miko Yakasai, Farfesa Bello Sa’id, Farfesa Mukhtar Yusuf, Farfesa Imam Abdulkarim, Alh. Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), Dakta Aliyu Idris Funtua, Farfesa Halliru Ahmad Amfani, da Honarabul Ibrahim Sulaiman Dabo.
![]()







