• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, May 15, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Bikin yaye ‘yan fim da aka horas ya bar baya da ƙura

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
December 15, 2019
in Labarai
0
Wani sashe na 'yan fim 450 da aka yaye a taron

Wani sashe na 'yan fim 450 da aka yaye a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

YAU kimanin shekara biyu kenan da gwamnatin Jihar Kano ta shirya wa masu gudanar da harkokin sana’ar su a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood taron sanin makamar aiki domin su samu ilimi a dukkan ɓangarori na sana’ar tasu. An shafe tsawon wata guda ana bayar da horon a ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.

 Mutane 450 ne su ka samu horon.

 Tun daga wancan lokacin ne kuma su ke ta jiran a ba su takardar shaidar karatun da su ka yi, wanda aka yi ta saka rana ana ɗagawa. 

 Dalilan da aka rinƙa bayarwa na sanya ranar taron ana ɗagawa bai wuce na cewa gwamnan Kano da kan sa ya ke so ya sanya ranar kuma ya miƙa takardun shaidar ga waɗanda su ka samu horon ba.

 Bayan ɗaukar lokacin, daga baya aka aje ranar 14 ga Disamba, 2019 domin bayar da takardun. 

An yi shirye-shirye masu yawa domin karrama ‘yan fim ɗin, wanda hakan ya sa aka yi ta samun maganganu masu karo da juna dangane da yadda taron zai gudana, domin kuwa surutai sun yi ta yawo a cikin’ yan fim na cewa an yi kyakkyawan shiri na miƙa takardun tare da bayar da wani tallafi ga waɗanda su ka samu horon kamar yadda ake bai wa sauran masu sana’o’i jari na kuɗi ko kayan aiki da gwamnatin jihar ta ke yi.

 An yi taron a Gidan Gwamnati a ranar da aka aje.

 To sai dai abin ya zo wa da ‘yan fim ɗin da bazata, inda shirya taron aka yi aka gama lami, domin kuwa taron ya jefa ‘yan fim cikin wani sabon tunani da kuma da-na-sani. 

Babban abin da ya karya armashin taron dai shi ne rashin halartar gwamna tare da sauran manyan baƙi da aka shirya za su je wajen, domin kuwa duk wani babba da aka tsara zai halarci wajen to wakili ya turo. 

 Sannan kuma taron an shirya za a fara shi ƙarfe 10 amma sai da ka shafe wuni guda ana zaman jira, kuma haka aka bar mutane cikin yunwa da ƙishiruwa. 

Tsohon Editan mujallar Fim, Sani Maikatanga (a hagu), ya na karɓar satifiket ɗin sa. A dama, Alh. Afakallah ne.

Babbar matsalar da mutane su ka yi kuka da ita a wajen kuma aka tafi ana ƙorafi a kan ta ita ce, an tara mutane 450 za a ba su takardun shaida, amma sai wasu shafaffu da mai guda biyar kaɗai aka bai wa, su ko sauran aka ce masu su tafi ofishin Hukumar Tace Finafinai su karɓi nasu bayan an tashi daga taron.

 Ga mari ga tsinka jaka, can ɗim ma da su ka je sai su ka ga wasu ‘yan kaɗan aka bai wa. Da dama ma wasu sunan su a  cikin jerin sunayen waɗanda su ka samu horon, yayin da wasu kuma aka ce satifiket ɗin nasu bai kammala ba saboda komfuta ta samu matsala. 

Ba a yi la’akari da cewar wasu daga nesa su ka taho domin karɓar shaidar ba, tare da tunanin samun wani tallafi daga gwamnati, amma sai su ka tsinci kan su cikin mawuyacin yanayi na rashin samun takardar shaida da kuma tallafin da su ke sa ran za su samu.  

Duk wannan ya sa mutane su ka yi ta ƙorafi bayan an gama taron. 

Da mujallar Fim ta tuntuɓi shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Isma’ila Na’abba (Afakallah), sai ya ce, “Ai maganar tallafi an gama bai wa su masu fim ɗin tallafi, domin duk wanda aka ba shi ilimin da zai gudanar da sana’ar sa ai babu wani tallafi da ya kai bada ilimi kyauta.”

 Duk da haka dai ‘yan fim ɗin sun ci gaba da yin ƙorafi tare da nuna cewar kawai dai an tara su ne, kuma aka yi amfani da taron nasu domin kawai a cimma wata manufa ta siyasa. 

Loading

Previous Post

Dalili na na buɗe ‘Sadauz Home’ – Rahama Sadau

Next Post

Yadda ‘yan Kannywood su ka zama ‘yan kallo a bikin BON Awards 2019

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Mahalarta na kallon 'yan rawar ƙoroso a Coronation Hall, zauren bikin 'BON Awards 2019' a Kano

Yadda 'yan Kannywood su ka zama 'yan kallo a bikin BON Awards 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!