A DAREN jiya Allah ya yi wa mahaifin fitacciyar marubuciya Hajiya Zuwairiyyah Adamu Girei rasuwa a Yola, Jihar Adamawa.
Alhaji Adamu Girei ya rasu ne a Babban Asibitin Gwamnatin Tarayya a Yola bayan gajeren rashin lafiya da ya yi.
Dattijon mai shekaru 93 ya rasu ya bar ‘ya’ya 30 mata 20 maza 10.
Daga cikin ‘yan’yan nasa akwai ita Zuwairiyyah wadda ta na ɗaya daga cikin marubutan shirye-shiryen dirama na ‘Daɗin Kowa’ da ‘Kwana Casa’in’ da ake nunawa a tashar talabijin ta Arewa 24.
An yi jana’izar sa a safiyar yau a Masallacin Juma’a da ke cikin Jimeta, Yola.
Ana ci gaba da zaman makokin a gidan marigayin da ke rukunin gidajen gwamnati, wato GRA a cikin Jimeta.
Allah ya jiƙan sa, kuma ya bai wa iyalai da ‘yan’uwa haƙurin jure wannan babban rashi.
![]()







