MAJALISAR zartarwa ta ƙasa ta Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta kafa wasu kwamitoci guda biyu don ci gaba da tabbatar da nagartar masana’antar Kannywood.
Kwamitocin, na ladabtarwa mai mutum 14 da kuma kwamitin tattara kuɗaɗe da ziyarar aiki mai mutum 14, an ɗora masu alhakin tabbatar da ɗa’a da kuma bin ƙa’idoji a cikin al’amurran wannan masana’anta ta fim.
Samar da waɗannan kwamitocin wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa mutunci da ƙa’idojin sana’a na masana’antu.
Shugaban MOPPAN na ƙasa, Alhaji Habibu Barde, ya jaddada muhimmancin waɗannan kwamitoci, inda ya bayyana cewa samar da su ya dace kuma zai bai wa MOPPAN damar bayyana nasarori da gudunmawar da ta samu a masana’antar.
Membobin kwamitocin kamar yadda babban sakataren MOPPAN, Malam Salisu Mu’azu, ya gabatar, su ne kamar haka:
- Kwamitin Ayyuka na Ladabtarwa na Ƙasa:
- Mohammed Kabiru Maikaba – Shugaba
- Ahmad Alkanawy – Memba
- Shu’aibu Yawale – Memba
- Hajiya Balaraba Ramat – Memba
- Magaji Mijinyawa – Memba
- Hajiya Rashida Adamu (Mai Sa’a) – Memba
- Hauwa Edita – Memba
- Dakta A. S. Bello – Memba
- Bala Mu’azu Kufaina – Memba
- Hajiya Fatima Lamaj – Memba
- Muhammed Gumel – Memba
- Salisu Officer – Memba
- Maikuɗi Cashman – Sakatare
2. Kwamitin Ayyuka na Tara Kuɗi da Ziyara:
- Ado Ahmad Gidan Dabino, MON – Shugaba
- Bello Achida – Memba
- Asma’u Sani – Memba
- Haladu Muhammed – Memba
- Al-Amin Ciroma – Memba
- Ibrahim L. Ibrahim – Memba
- Umar Gombe – Memba
- Ahmad Hashim – Memba
- Tijjani Faraga – Memba
- Jamila Nagudu – Memba
- Maijidda Abbas – Memba
- Falalu Ɗorayi – Memba
- Nasiru Gwangwazo – Memba
- Ibrahim Amarawa – Sakatare
A cikin sanarwar da Malam Al-Amin Ciroma, Sakataren Yaɗa Labarai na MOPPAN, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta zayyana sharuɗɗan nassoshi na kwamitocin.
An ba su alhakin tsarawa da aiwatar da duk ayyukan da aka amince da su don bunƙasa cigaba da nasarar ƙungiyar.
Haka kuma kwamitocin su na da hurumin zaɓar duk wani mutum da ya dace da nasarar aiwatar da ayyukan su.
MOPPAN ta ci gaba da jajircewa wajen inganta ƙwararru da ƙa’idojin tabbatar da ɗabi’a a cikin masana’antar shirya finafinai ta Nijeriya.
Ta ce: “Kafa waɗannan kwamitocin alama ce mai muhimmanci a ƙoƙarin mu na ci gaba da tallafawa da haɓaka masana’antar ga duk masu aiki.”
![]()







