• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Murnar sauya Sarki: Rarara zai raba motoci da kujerun Makka

by DAGA ISAH BAWA DORO
March 19, 2020
in Labarai
0
Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero (a hagu), da Dauda Kahutu Rarara (a dama)

Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero (a hagu), da Dauda Kahutu Rarara (a dama)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
SABODA shauƙin cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da maye gurbin sa da Aminu Ado Bayero, fitaccen mawaƙin nan Dauda Kahutu (Rarara) ya saka gasa inda zai raba kujerun Makka da Umara da motoci, da kuɗaɗe kyauta ga waɗanda su ka yi nasara.
 
Rarara ya bayyana haka ne a wani saƙon bidiyo da ya fitar a shafin sa na YouTube.
 
Ya ce ya saka gasar ne don nuna farin ciki game da naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano da gwamnatin jihar ta yi.
 
Rarara mawaƙin siyasa ne wanda ke bin gwamnatin da ke kan mulki.
 
Ya ce a ƙa’idojin shiga gasar ana so duk wani mawaƙin Hausa da ya ke Nijeriya ko wajen ta da ya yi sabuwar waƙa ga sababbin sarakunan Kano guda biyar, wato na Kano da na Bichi da na Ƙaraye da na Sarkin Gaya da na Rano.
 
A ƙa’idojin, ana so kada waƙar ta wuce minti biyar, sannan ya kasance a cikin minti biyar ɗin nan mawaƙi zai yi wa kowane sarki waƙar sa, cikin salo da zai burge kowace fada, da kuma su kan su sarakunan.
 
Wata ƙa’idar ita ce tilas ne duk mawaƙin da zai shiga gasar ya kasance ya na da rajista da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano. 
 
Bugu da ƙari, mutum 50 kacal za a zaɓa zaba a matsayin zakarun gasar.
 
A cewar sa, a ranar da za a fidda zakarun kowane mawaƙi zai zo da waƙar sa a rubuce kuma ya rera ta a gaban manyan baƙin da za su halarci taron, cikin su har da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
 
Rarara ya bayyana cewa ya tanadi farfesoshin nazarin harshen Hausa da za su zama alƙalan gasar.
 
Ga jerin sunayen kyaututtukan da zai ba waɗanda su ka yi nasara:
 
Na 1: Mota
Na 2: Mota
Na 3: Kujerar Makka
Na 4: Kujerar Makka
Na 5: Kujerar Umara
Na 6: Kujerar Umara
Na 7: Keke Napep
Na 8: Keke Napep
Na 9: Babur
Na 10: Babur.
 
Sauran mawaƙan 40 kuma kowannen su za a ba shi kyautar N100,000.

Loading

Previous Post

Bankin CBN zai bada lamunin biliyan 22 don tallafa wa manishaɗinta

Next Post

Annoba, ibada da addini a arewacin Nijeriya

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Sama: Musulmi na sallah a Legas. A ƙasa: ƙwayoyin cutar 'Coronavirus'

Annoba, ibada da addini a arewacin Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!