• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za a rufe rajistar taron ranar Marubutan Hausa ta Duniya ranar Alhamis

by MUKHTAR YAKUBU
October 20, 2025
in Marubuta
0
Za a rufe rajistar taron ranar Marubutan Hausa ta Duniya ranar Alhamis

Karl Tapales | Getty Images

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Kwamitin shirya taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya na bana ya ce za a rufe rajistar halarta taron saboda an riga an kai adadin mutanen da ake buƙata domin gudanar da taron cikin tsari da aminci.

A game da hakan ne kwamitin ya tsaida ranar Alhamis mai zuwa a matsayin rana ta ƙarshe ta kammala rajista.

Sakataren Kwamitin Shirya Taron, Dakta Abdulrahman Aliyu, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da raba wa manema labarai a yau

Ya ce daga wannan ranar babu wanda zai ƙara iya yin rajista ko canza bayanan rajistar sa da aka riga aka kammala.

Aliyu ya ce wannan matakin ya zama dole ne saboda kwamitin ya fara shirin samar da ingantattun abubuwan more rayuwa da jin daɗin mahalarta taron, domin tabbatar da cewa taron zai gudana bisa tsarin da ake gudanar da taruka na ƙasa da ƙasa.

Haka kuma ya ce kwamitin ya tanadi wurin kwana mai inganci ga dukkan mahalarta da suka yi rajista a kan lokaci; abinci da sha mai kyau da tsafta, da kuma tsarin taro na zamani da zai bai wa kowa damar koyo da musayar ra’ayi da hulɗa da ƙwararru daga sassa daban-daban na duniya.

Ya ci gaba da cewa. “Taron Ranar Marubuta Hausa na Duniya, 2025, wanda za a gudanar a Jihar Jigawa, na da nufin ɗaga martabar harshen Hausa da marubuta, tare da haɗa su da sabbin fasahohi da dabarun da ake amfani da su a duniya wajen rubutu, fassara, da ilimin harshe.”

Kwamitin yana yaba wa duk wanda ya nuna sha’awa ko ya riga ya yi rajista, tare da neman afuwar waɗanda ba su samu damar kammala rajista ba.

A cewar sa, wanda ke sha’awar zuwa taron bai yi rajista ba zai iya halarta, amma ba za a ba shi masauki da kayan da suka shafi taron ba.

Loading

Tags: Ranar Marubuta
Previous Post

Ƙwararren marubucin fim, Adamu Ibrahim Kabala, ya kwanta dama

Next Post

KILAF 2025: Za mu ci gaba da ƙarfafa wa matasa gwiwa don samar da finafinai masu nuna al’adun mu – Abdulkareem

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
KILAF 2025: Za mu ci gaba da ƙarfafa wa matasa gwiwa don samar da finafinai masu nuna al’adun mu – Abdulkareem

KILAF 2025: Za mu ci gaba da ƙarfafa wa matasa gwiwa don samar da finafinai masu nuna al'adun mu - Abdulkareem

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!