BABBAN furodusa a Kannywood, Alhaji Abdul Amart Mohammed, ya ɗauki nauyin tafiyar jaruma Muhammad zuwa ƙasar Saudiyya domin neman magani da a kullum take buri da kuma fata.
Sanin kowa ne cewa jarumar ta daɗe tana fama da ciwon sankarar nono.
Haka kuma ta jima tana neman agaci daga gwamnatocin tarayya da na jihohi da sauran ƙungiyoyi da sauran jama’a domin ceto rayuwar ta daga halin da ta samu kan ta a ciki.
Gwamnatin Jihar Kano ta taɓa ba ta tallafin miliyoyin naira, haka ma ɗaiɗaikun mutane sun taimaka mata.
A yanzu dai Allah ya kawo mata ƙarin agaji ta hanyar Abdul Amart wanda sananne ne wajen taimakon jama’a, musamman ‘yan’uwan sa ‘yan fim.
Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta jinjina wa Abdul Amart kan wannan babban hoɓɓasa da ya yi.
Halisa ta sanar da duniya wannan abin farin cikin a Facebook, inda ta ce: “Ina miƙa godiya ta ga Allah Maɗaukakin Sarki, mai kowa mai komai, mai amsar addu’ar bayin sa da ya cika mini buri na ta hannun bawan sa Abdul Amart. Ya ce, ‘Halisa zo ki tafi Madina’. Sai na fashe da kuka don daɗi. Allah ya faranta maka. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ya taimake ka a dukkan harkokin ka. Allah ya buɗe maka ƙofofin rahama da arziki marasa adadi. Allah ya jiƙan iyayen ka, ya kare yaran ka, ya albarkaci zuriyar ka, ka ci gaba da kasancewa jagora na alheri a rayuwar mu.”
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin damfarar miliyoyin naira da wani mai suna Bashir ya yi wa Halisa Muhammad a kan zai taimaka mata ta tafi ƙasar waje domin neman magani.
Kwanan nan tsohuwar jarumar ta yi wani dogon rubutu a soshiyal midiya mai tayar da hankali dangane da halin da take ciki da kuma yadda ta duƙufa wajen neman mafita.
Saƙon nata yana dauke da cewa: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Assalamu alaikum. Na samu bayani daga EFCC cewa ana cikin bincike kuma ana ci gaba da gudanar da shi bisa ƙa’ida. Sun shaida mini cewa binciken zai ɗauki lokaci, don haka na rungumi haƙuri da tawakkali.
“Ina roƙon al’umma su ci gaba da yi mana addu’a da fatan alheri. Abin da ake nufi da haka shi kenan kuɗi na ya tafi, shi kenan treatment ya ƙare. Hasbunallahu wa nimal wakil.
“Ni baiwa ce daga cikin bayin Allah da ke fuskantar wata babbar jarabawa ta rashin lafiya, ciwon da ya ɗaure ni, ya raunata jiki na, ya girgiza zuciya ta. Ga ciwo ga zalunci.
“Ina da buri guda ɗaya kawai a rayuwa: Na je Madina. Na ziyarci fadar Shugaban Halitta, Annabi Muhammad (SAW), na ga Rawdah mai albarka, na roƙi Allah da ido na cike da hawaye gani a fadar masoyi na Annabin rahma sallallahu alaihi wa sallam, gida mai tsarki, na zubar da hawaye na a gaban ƙabari mai albarka, na faɗi damuwa ta ga ni a fadar Allah mai rahama mai jinƙai. Wannan shi ne burin da ya rage mini. Burin da nake ganin zai sa ni nutsuwa. Burin da nake ganin zai zama sauyin damuwa ta da lalura ta. Hakan shi ne waraka ta in shaa Allah.
“Na san akwai waɗanda idan suka ji kuka na, sai zuciyar su ta karaya. Ina roƙon ku al’umma, ku taimaka mini da addu’a da abin da za ku iya, domin cika mini buri na. Don Allah ku taimaka mini na cimma wannan buri nawa, na je Madina kafin ƙasa ta rufe mini ido hawaye na ya ƙare.
“A baya ma ku kuka taimaka mini, yau ma na kawo kuka na wajen Allah, na kawo kuka na wajen ku. Ku taimaka mini, don Allah. Ku share mini hawaye, Allah zai share naku. Ku sa ni dariya, Allah zai sa ku farin ciki.
“Allah ya saka muku da mafificin alkairi. Allah ya hana ku ganin irin waɗannan jarrabawar a rayuwar ku.”
Sakamakon wannan taimako da Abdul Amart ya yi wa Halisa, Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta yaba masa.
A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren ƙungiyar, Dakta Mohammed I. Gumel, ya ce: “A madadin shuwagabanni na ƙasa da na jihohi da kuma kafatanin mambobin MOPPAN, ina miƙa jinjina da miƙa godiya marar adadi ga Dr Abdul Amart jagoran Kannywood. Saboda taimako da nuna tsantsar kulawa, ƙauna, tausayawa da kuma jiɓintar al’amarin ‘yar’uwa Hajiya Halisa Muhammad.
“Wannan taimakon nasa ba shi ne na farko ba, da ma ya sha yi mata da kuma kuma yi wa duk wani ɗan Kannywood da buƙatar hakan ta taso masa. Wasu mun sani, wasu ba mu sani ba.
“Hakan ta sa muke alfahari da kai kuma muke tinƙaho da dukiyar da Allah ya ba ka. Allah ya saka maka da alkhairan sa.
“A ƙarshe, ina maka fatan cin gajiyar wani hadisin Manzon Allah (SAW) da na ji malamai suna hakaitowa cewa, ‘Duk wanda ya zama sanadiyyar yaye baƙin ciki bawa a nan duniya, to Allah zai yaye masa baƙin ciki ranar tashin kiyama.’
“Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta wa Halisa, kuma mu ma ka faranta mana.
“Allah ya sa ka daɗe kana yi. Allah ya jiƙan mahaifan ka. Allah ya ƙara kuma ya dauwamar da arzikin ka. Mashaa Allah.”
![]()







