INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa mahaifiyar darakta a Kannywood, Hafizu Bello, rasuwa.
Mahaifiyar, Gwaggo Hasiya, ta rasu ɗazu a Kano bayan ta yi fama da rashin lafiya.
Hafizu Bello da kan sa ya tabbatar da rasuwar a saƙon tes da ya turo wa da mujallar Fim inda ya bayyana cewa za a yi jana’izar ta gobe Lahadi da misalin ƙarfe 9 na safe a gidan ta da ke Gyaɗi-Gyaɗi daura da Gadar Lado.
Allah ya jiƙan ta, amin.
![]()







