ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN) ta bayyana cewa 2025 ta kasance shekara mai cike da tarihi, nasarori da kuma cigaban masana’antar shirya finafinan Hausa.
Cikin wata takarda da MOPPAN ta fitar fitar da sunan rahoto kan Shekarar ‘Yan Kannywood ta 2025, ƙungiyar ta ce:
“Shekarar 2025 ta zo da ƙalubale da dama, amma duk da haka ta kasance shekara mai albarka wadda ta ga yawaitar finafinai masu inganci, da kuma fitowar sababbin fasahohi da salo a masana’antar Kannywood.
“Masu shirya finafinai sun nuna jajircewa da sadaukarwa wajen samar da finafinai masu ilimantarwa, nishaɗantarwa da kuma isar da saƙonni masu amfani ga al’umma.”
A cewar MOPPAN, “An samu cigaba mai kyau a fannin labari, ɗaukar hoto, shirya fim da kuma kula da ƙa’idojin sana’ar fim, wanda hakan ya taimaka wajen ɗaga darajar Kannywood a matakin Nijeriya, Afrika da ma duniya baki ɗaya.”
Ƙungiyar ta bayyana finafinai biyar da suka fi ɗaukar hankali a shekarar, kamar haka:
- KAKANDA: Fim ɗin da furodusa Dakta Ahmad Sarari tare da Malam Khalid Musa suka rubuta, fim ne mai ingantaccen labari, salo na zamani da kuma tsari mai ƙarfi, wanda ya ja hankalin masu kallo sosai.
- MANYAN MATA: Fim ɗin furodusa Abdul Amart, wanda ya fito da darajar mata da rawar da suke takawa a cikin al’umma, ya samu karɓuwa sosai daga masu kallo.
- GARWASHI: Fim ɗin furodusa Umar UK, wanda ke nuna gwagwarmaya da juriya a rayuwar ɗan’adam, ya nuna ƙwarewa ta musamman a fannin rubutu da aiwatarwa.
- LABARI NA: Fim ɗin darakta Malam Aminu Saira, wanda ya nuna hazaƙa da zurfin tunani a tsarin labari da kuma jagoranci.
- WATA SHIDA: Fim ɗin furodusa Hayatuddeen Yakubu, wanda aka shirya bisa littafin Kamilu Ɗanhausa, ya samu karɓuwa a cikin gida da kuma ƙasashen Afrika, tare da nuna ƙarfin labarin Hausa a duniya.
Rahoton ya ambaci ‘Mai Martaba’ wanda Prince Aboki ya shirya kuma ya jagoranta a matsayin fim mafi shahara a shekarar. Fim ɗin ya samu nasarori masu yawa tare da ɗaga darajar Kannywood a idon duniya.
Haka nan MOPPAN ta yaba da gudunmawar da shugaban ta, Alhaji Shehu Hassan Kano, bisa jagoranci da ƙoƙarin sa na haɗa kai da kuma bunƙasa sana’ar fim.
Ta miƙa godiya ga dukkan furodusoshi da sauran ‘yan Kannywood bisa biyayya da goyon baya ga ƙungiyar.
MOPPAN ta roƙi Allah ya saka wa kowa da alheri, ya kuma nuna mana shekarar 2026 cikin kwanciyar lafiya.

![]()







