• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

2027: Ƙungiyar siyasar Tinubu da Uba Sani ta naɗa mawaƙi Jamilu Ɗan Masu Kuɗi muƙamin shugaban nishaɗantarwa

by ABBA MUHAMMAD
June 9, 2026
in Labarai
0
2027: Ƙungiyar siyasar Tinubu da Uba Sani ta naɗa mawaƙi Jamilu Ɗan Masu Kuɗi muƙamin shugaban nishaɗantarwa

Daga hagu: Jamilu Ɗan Masu Kuɗi yana karɓar takardar kama aiki daga hannun Dakta Abdulmumini Aminu Zaria

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na ƙungiyar Tinubu/Uba Sani Mobilisation Network ya naɗa fitaccen mawaƙin siyasa kuma mazaunin Kaduna, Jamilu Sa’idu (Ɗan Masu Kuɗi), a matsayin Shugaban Sashen Nishaɗantarwa na Midiya (Head of Media Entertainment) na ƙungiyar.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa naɗin yana da nasaba da yaƙin neman babban zaɓen shekarar 2027 da za a yi a Nijeriya.

A cikin takardar naɗin da ke ɗauke da kwanan watan 8 ga Mayu, 2026, ƙungiyar ta bayyana cewa an zaɓi Jamilu ne bisa la’akari da ƙwarewar sa a fannin sadarwar zamani, ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma jajircewar sa wajen yaɗa manufofin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da tallata nasarorin gwamnatin Gwamna Uba Sani.

Takardar ta ƙara da cewa naɗin zai fara aiki nan take, inda aka umurci sabon shugaban sashen da ya riƙa karɓar umurni da shawarwari daga jagoran harkokin jihohi na ƙungiyar domin tabbatar da nasarar ayyukan sa.

A matsayin sa na shugaban sashen nishaɗantarwa a ɓangaren midiya, Jamilu zai jagoranci amfani da masana’antar nishaɗi wajen wayar da kan jama’a kan manufofi da shirye-shiryen ƙungiyar.

Haka kuma, zai taimaka wajen tattara magoya baya ta hanyar nishaɗi, yaƙi da yaɗuwar bayanan ƙarya, da kuma haskaka nasarorin gwamnatocin jam’iyyar APC a matakan tarayya da jihohi.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta buƙaci sabon shugaban sashen da ya miƙa takardar amincewar sa da wannan naɗi ga Sakatare Janar na ƙungiyar cikin mako guda bayan karɓar takardar naɗin.

Da yake taya shi murna, jagoran Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na ƙungiyar, Dakta Abdulmumini Aminu Zaria, ya bayyana fatan cewa Jamilu Ɗan Masu Kuɗi zai yi amfani da gogewar sa da tasirin sa a fagen nishaɗi wajen ƙara ƙarfafa manufofi da ayyukan ƙungiyar, tare da yi masa fatan alheri a sabon muƙamin da aka ɗora masa.

Loading

Tags: Dakta Abdulmumini Aminu ZariaJamilu Sa'idu Ɗan Masu KuɗiTinubu/Uba Sani Mobilisation Network
Previous Post

MOPPAN ta yaba da shirin rajistar inshorar lafiya ga ’yan Kannywood

Next Post

Ali Nuhu ya sama wa yaron sa Nazifi Baƙo aiki a Gwamnatin Tarayya

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Ali Nuhu ya sama wa yaron sa Nazifi Baƙo aiki a Gwamnatin Tarayya

Ali Nuhu ya sama wa yaron sa Nazifi Baƙo aiki a Gwamnatin Tarayya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!