ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Arewacin Nijeriya (AFMAN) ta fara aiwatar da wani gagarumin shirin sake wa kan ta fasali.
Shirin ya haɗa da sake tsara tsarin shugabanci a matakin ƙasa da jihohi, tare da tsawaita wa’adin shugabannin riƙon ƙwarya da shekara guda domin tabbatar da ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ake buƙata.
An cimma wannan matsaya ne a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ƙungiyar wanda aka gudanar ranar Talata, 9 ga Yuni, 2026, a hedikwatar AFMAN da ke Zoo Road a Kano.
Taron, wanda ya samu halartar manyan shugabannin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Shugaban AFMAN na Ƙasa, Alhaji Salisu Mohammed Officer, ya mayar da hankali ne kan hanyoyin sake gina ƙungiyar domin ta dace da buƙatun zamani da kuma cigaban masana’antar Kannywood.
A jawabin sa na buɗe taron, Alhaji Officer ya jaddada muhimmancin haɗin kai da kuma aiwatar da gyare-gyaren da za su mayar da AFMAN ƙungiya mai ƙarfi, tasiri da amfani ga membobin ta da al’umma baki ɗaya.
Bayan tattaunawa mai zurfi, kwamitin ya amince da gudanar da cikakken nazari kan tsarin ƙungiyar, manufofin ta da hanyoyin gudanar da ayyukan ta, da nufin samar da sabuwar AFMAN da za ta iya fuskantar ƙalubalen da masana’antar shirya finafinai ke fuskanta a wannan zamani.
Daga cikin manyan ƙudirorin da aka amince da su akwai tsawaita wa’adin shugabannin riƙon ƙwarya na ƙasa da shekara guda, har zuwa lokacin da za a kammala sabon tsarin shugabanci da ake shirin samarwa.
Haka kuma, kwamitin ya amince da cike gurabe shida da suka rage babu masu riƙe da su a cikin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa, domin cika adadin shugabanni goma sha uku da kundin tsarin ƙungiyar ya tanada.
A wani mataki na sake fasalin shugabanci, an amince da sake duba da sake tsara shugabannin AFMAN a dukkan jihohin Arewa, tare da sabunta wa’adin kwamitocin riƙon ƙwarya na jihohi da shekara guda yayin da ake ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da aka tsara.
Domin tabbatar da ingantaccen aiki a matakin jihohi, kwamitin ya ɗora wa Sakatare Janar na AFMAN, Alhaji Sani Sule Katsina, da Sakataren Yaɗa Labarai, Malam Mahmood Mukhtar Daneji, alhakin tantance ayyukan shugabanni da sakatarorin jihohi tare da gabatar da shawarwari kan maye gurbin waɗanda ba su gudanar da ayyukan su yadda ya kamata ba.
Har ila yau, taron ya amince da samar da gajerun saƙonnin wayar da kai domin ilimantar da al’umma kan matsalolin da suka haɗa da rashin tsaro, shaye-shaye a tsakanin matasa, lalacewar tarbiyya da kuma rashin ɗa’a a harkokin siyasa.
Kwamitin ya yanke shawarar riƙa gudanar da taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa a ƙarshen kowane wata, ko dai ta hanyar taron zahiri ko na yanar gizo, domin tabbatar da ci gaba da bibiyar ayyuka da kuma aiwatar da shawarwarin da aka yanke.
Bugu da ƙari, an bai wa Shugaban Kwamitin Amintattu (BoT) na AFMAN, Malam Abdullahi Sani Abdullahi, alhakin sa ido da bayar da shawarwari kan yadda za a aiwatar da shirin sake fasali da sake tsara ƙungiyar har zuwa lokacin da za a kammala shi.
A ƙarshe, Kwamitin Zartarwar ya yi kira ga dukkan membobin AFMAN da su rungumi sulhu, haɗin kai da fahimtar juna domin cigaban ƙungiyar da kuma bunƙasar masana’antar shirya finafiinai ta Arewa.
An rufe taron cikin nasara, inda Shugaban Ƙungiyar ya yaba wa mahalarta bisa gudunmawar da suka bayar wajen samar da muhimman shawarwari da ake sa ran za su kawo sabon sauyi da cigaba a tafiyar AFMAN.
![]()







