A YAU ma masu sana’ar finafinan Hausa sun yi wani taro na musamman domin yin addu’o’i ga fitacciyar jaruma Zainab Musa Booth wadda ta rasu a makon jiya.
Hajiya Zainab ta rasu ne sakamakon rashin lafiya a ranar 1 ga Yuli, 2021, a Kano.
Ita ce mahaifiyar jaruman nan biyu, wato Maryam Booth da Amude Booth.
Mutuwar ta ta girgiza ‘yan fim matuƙa.
Ɗimbin ‘yan fim sun yi taron addu’ar a yau a harabar Social Welfare da ke Fagge.

A taron, an yi addu’o’i tare da jawabai kan kyawawan halayen marigayiyar.
Idan kun tuna, ‘yan fim sun yi irin wannan taron a shekaranjiya Alhamis a Kano domin addu’ar kwana bakwai da rasuwar jarumar.













![]()







