BABBAN furodusa Ali Bulala Gusau ya koma aikin sa na yau da kullum a yau Juma’a, 30 ga Yuli, 2021 – kwanaki huɗu kacal bayan kuɓutar sa daga hannun ɓarayi masu garkuwa da mutane.
Mujallar Fim ta ba ku labarin yadda ɓarayin su ka tare Ali da matar sa da ‘ya’yan sa huɗu a hanyar Gusau zuwa Sakkwato a ranar ta biyu ta Babbar Sallah, wato 22 ga Yuli, inda su ka tafi da shi cikin daji su ka tsare shi.
Ɓarayin sun ƙyale iyalin nasa sun tafi, amma shi sai su ka riƙe shi a matsayin garkuwa da shi.
A hirar da ya yi da wakilin mu a ranar da ya kuɓuta, furodusan ya bayyana yadda aka yi ya kuɓuta bayan ‘yan’uwan sa sun yi karo-karo sun tara kuɗin fansa naira miliyan 5, wanda aka kai wa ɓarayin kafin su sako shi.

A yau furodusan ya tura hotunan sa biyu a guruf ɗin uwar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa, wato MOPPAN, tare da saƙo mai cewa: “Alhamdu lillahi! Yau Juma’a na koma bakin aiki na bayan kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane! Allah tsare dukkan jama’a daga shiga wannan iftila’in ! Na gode da addu’ar ku. Naku, Ali Bulala Gusau.”
‘Yan fim da dama sun yi wa Ali fatan alheri, tare da addu’ar Allah ya kiyaye gaba.