MASHA Allah! Fitaccen jarumin Kannywood Mustapha Musty da matar sa Ghadir Mahmud Shareef sun samu ɗan fari.
Ghadir, wadda ake wa laƙabi da Soha, ta haifi santalelen yaro a yau a birnin Kano.
Idan kun tuna, an ɗaura auren Mustapha da Soha ne a ranar Lahadi, 29 ga Nuwamba, 2020 a gidan Alhaji Ibrahim D.O. da ke Titin Jakara, kusa da Goron Dutse, Kano, a kan sadaki N50,000.

A hirar da ya yi da mujallar Fim a ranar ɗaurin auren, Musty ya ce sai da su ka kwashe shekara 13 su na soyayya kafin su yi aure.
A lokacin, jarumin ya bayyana irin farin cikin da ya ji game da ranar, inda ya ce: “Gaskiya ina cikin farin ciki saboda wannan rana ce da na daɗe ina jiran ta kusan aƙalla shekaru goma sha uku; sai a wannan rana Allah ya ƙaddara zuwan ta, ka ga ai farin ciki ba zai misaltu ba.”
To yanzu dai an samu sabon farin ciki na haihuwa.
Allah ya raya wannan yaro a bisa tafarkin Manzo (s.a.w.), amin.
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com
![]()







