• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An tara naira miliyan 14 a taron ƙaddamar da littattafan Fatima Ibrahim Abba Gana

by DAGA ABBA MUHAMMAD
January 10, 2022
in Marubuta
0
Fatima Abba Gana a wajen taron ƙaddamar da littattafan ta a Kaduna shekaranjiya

Fatima Abba Gana a wajen taron ƙaddamar da littattafan ta a Kaduna shekaranjiya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN tara aƙalla naira miliyan 14 a wajen taron ƙaddamar da wasu littattafai biyu na marubuciya Hajiya Fatima Ibrahim Abba Gana shekaranjiya Asabar, 8 ga Janairu, 2022 a Kaduna.

Marubuciyar ta rubuta littattafai biyu na hikaya masu suna ‘Raƙiba’ da ‘Karima’, waɗanda kamfanin buga littattafai na Gidan Dabino, Kano, ya wallafa. Yayin da ‘Raƙiba’ na da shafi 447, ‘Karima’ kuma na da shafi 87.

A taron, wanda aka gudanar a Hotel Seventeen, an bayyana cewa babban mai ƙaddamarwa, Talban Bauchi, Alhaji Tahir Ibrahim Tahir, wanda bai samu damar halarta ba, ya aiko da saƙon zai bada naira miliyan 5 a kan kwafe biyar-biyar na littattafan.

Littafin ‘Raƙiba’ da na ‘Karima’

Mataimakin babban mai ƙaddamarwa, Alhaji Shamsudeen MD Yusuf (Bulaman Zazzau), ya aiko da saƙon ya bada naira miliyan 2, sannan ɗaya daga cikin manyan baƙi, Alhaji Umaru Ƙwairanga (Sarkin Fulanin Gombe), shi ma bai zo ba amma ya aiko da saƙon zai bada naira miliyan 1.

Wasu da su ka ƙaddamar da littafin su ne tsohon Ministan Wutar Lantarki, Dakta Muhammed Wakil (naira miliyan 2), Alhaji Abubakar Sadiq Abubakar (Lihiddan Gusau) wanda kwamishina ne a hukumar RMFC da ke Abuja (naira miliyan 1), sai kuma tawagar wasu jami’ai daga Hukumar Talbijin ta Ƙasa (NTA) da su ka halarci taron a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Muhammad Kudu Abubakar, sun bada N50,000.

Bugu da ƙari, Alhaji Muhammed Ibrahim Kuchi ya bada N100,000, Shugaban Bankin Taj, Hamid Joɗa, ya bada N100,000, Hajiya Aisha Musa ta Bankin Wema ta bada N100,000, yayin da Sarkin Mawaƙan Dutse, Alhaji Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa), ya bada N20,000 lakadan.

Sai dai mujallar Fim ta lura da cewa yawancin kuɗaɗen da aka bayyana bayarwa duk na alƙawari ne, wato waɗanda ake sa ran za a biya daga baya, domin kuwa tsabar kuɗi da aka tara ba su fi N400,000 ba.

Mai sharhi kan littattafan dai shi ne Farfesa Ibrahim Yakasai, wanda ya yi bayani kan abin da kowane littafi ya ƙunsa, kuma ya jinjina wa marubuciyar bisa ƙoƙarin da ta yi. Haka kuma ya nuna wasu wurare inda aka samu kurakurai a littattafan.

Bugu da ƙari, ya yi nuni da cewa akwai muhimmanci littafin ya samu shiga a wajen masu karatu, don haka ya kamata mutane su nema su karanta.

Shugaban kwamitin shirya ƙaddamarwar, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shi ma ya yi jawabi kan littafin da kuma ƙoƙarin marubuciyar.

Marubuciyar littafin ta yi jawabin godiya ga mahalarta da ‘yan kwamitin shirya taron cikin harshen Hausa da Turanci, inda ta yi fatan Allah ya maida kowa gida lafiya.

Taron ya yi armashi matuƙa, musamman yadda aka tsara shi, sannan Ala ya gabatar da wasu sanannun waƙoƙin sa irin su ‘Bakan Dabo Sankano’ da ‘Jami’a Gidan Ban-kashi,’ sannan kuma ya yi wa marubuciyar wata sabuwar waƙa ta musamman.

Mahalarta taron sun haɗa da Ado Gidan Dabino, Aminu Ala, Muhammad Kudu Abubakar, Abubakar Yusuf Ladan, Hajiya Binta Abba Gana, Hajiya Halima K/Mashi, Mariya Durumin Iya, Bilkisu Yusuf Ali, Hauwa Lawan Maiturare, Ummi Abba Gana, Mudan Gidan Dabino, da sauran su.

Daga hagu: Hauwa Lawan Maiturare, Mariya Durumin Iya, Fatima Abba Gana, Ado Ahmad Gidan Dabino, Bilkisu Yusuf Ali da Halima K/ Mashi a wurin taron

Ita dai Hajiya Fatima Abba Gana, wadda ‘yar Kanuri ce daga Jihar Borno, an haife ta a Kaduna. Ta samu digirin Ƙididdigar Kuɗi daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Ta yi aiki a wasu bankuna.

Ita ce babbar ɗiyar fitaccen ma’aikacin rediyo da talbijin ɗin nan, marigayi Alhaji Ibrahim Abba Gana, wanda ya yi aiki a gidan rediyon BBC, FRCN da gidan talbijin na NTA, sannan fito a matsayin Waziri a cikin diramar ‘Magana Jari Ce’ da tashar NTA ta riƙa nunawa a shekarun baya; a taron an ma gabatar da wani guntun bidiyo mai nuna tarihin mahaifin nata da aikin wasan kwaikwayo da ya yi.

Fatima, wadda mazauniyar Abuja ce, memba ce a ƙungiyar marubuta ta Alƙalam da ke da Kaduna.

Mahalarta taron
Aminu Ala ya na gabatar da waƙoƙi
Marubuciya Fatima Abba Gana ta na jawabin godiya

Loading

Tags: Adabin HausaAdo Ahmad Gidan DabinoAminu Alabook launchFatima Ibrahim Abba GanaHalima K/MashiHauwa Lawan MaiturareKungiyar AlkalamMagana Jari CeMariya Durumin IyaMuhammad Kudu AbubakarNTATahir Ibrahim TahirUmaru Kwairanga
Previous Post

Mun yi tunanin abin ba zai yiwu ba, inji Tagwayen Asali bayan sun auri ‘yanbiyu

Next Post

Ta’aziyyar Muhammadu Ɗan Sanyinna (Raba-Gardama)

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Marigayi Alh. Mamman Raba-Gardama. Hoto daga: Abdulaziz Abdulaziz

Ta'aziyyar Muhammadu Ɗan Sanyinna (Raba-Gardama)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!