SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai da Ɗabi’i ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana dalilin da ya sa hukumar ta fara aikin sabunta rajistar ‘yan fim ɗin Hausa.
Haka kuma ya gargaɗi masu amfani da YouTube wajen tura finafinai da waƙoƙi.
A jiya Litinin ne, 18 ga Janairu, 2021 hukumar ta ƙaddamar da aikin yi wa ‘yan fim da su ka shigo cikin masana’antar ta Kannywood rajista domin su samu damar gudanar da ayyukan su cikin kwanciyar hankali wajen bin dokokin da gwamnatin jihar ta gindaya na shiga harkar fim.
Shugaban ya bayyana wa mujallar Fim cewa: “Hukumar ta fara sabunta rajistar ne tare da bai wa waɗanda ba su yi wannan rajistar ba dama domin hukumar ta tantance su sannan ta ba su izinin fara yin harkar finafinai a Jihar Kano.
“Sannan hukumar ta bijiro da wasu tsare-tsare waɗanda ba a gani a baya ba.
“Tsarukan sun haɗa da sanin adadin yawan mutanen da su ke cikin wannan sana’a, sannan a san su waye su, daga ina su ke, saboda yanayin da ake ciki.
“Kano gari ne babba kuma wannan sana’a babba ce, saboda matasan da su ke cikin ta masu ɗimbin yawa ne waɗanda su ka zo daga mabambantan garuruwa, wasu ma har da ƙasashe. Ganin haka kuma ba zai yiwu a zuba idanu a bar ta sasakai ba. Ka san su waye su ke yin ta, ba ka san tsarin da za su yi ta ba.
“Sannan kuma idan za su shigo ya za su shigo; in ma za a ce wani an kore shi, ya za a kore shi ko a hana shi? Da sauran su.
“Don haka ganin wannan abin ya sa gwamnatin Jihar Kano, ƙarkashin jagorancin gwamnan Jihar Kano, ya ƙaddamar da wannan tsari da kan shi a shekarar 2019, wanda kuma a ƙarshe abin ya ci gaba da tafiya cikin nasara kamar yadda ku ke gani.”

Shugaban ya ja hankalin musamman ‘yan fim masu amfani da manhajar YouTube su ke guje wa wannan doka da su sani cewa akwai hukunci da aka tanadar a kan su.
Ya ƙara da cewa hukumar tasa ta haɗa kai da masu tura finafinai na Jihar Kano kan “yadda za su daina tura irin waɗancan finafinan waɗanda jaruman cikin su ba su da rajista, sannan kuma ba a kawo shi mun tace ba.
“Duk kuwa wanda ya yi hakan akwai doka wacce za ta zamana cewa ta hannun-ka-mai-sanda ce, duk kuma wanda ya bijire to da alama ba ya son ma’amala da mutanen Kano.”
Afakallah ya shawarci ‘yan masana’antar da su zamo masu girmama doka, ya ce ɗan fim “ya girmama kan sa da kuma sana’ar sa domin sana’a ita ce mutum kamar yadda jama’a ke samun taro da kwabo a cikin ta har ma da samun rufin asiri. Sannan kuma su sani cewa duk abin da ake yi ana yi ne don kan su ne.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa tsofaffin jarumai da dama su na ta zuwa hukumar domin sabunta rajistar tasu tare da yi wa sababbin shiga rajista.
Za a ɗauki tsawon makwanni biyu ana aikin rajistar.

Allah ya sama Rarara da alkhairi ya ra masa arziki. masu cewan riya ne yake yi ai duk don basu da zuciyan taimakon bayin Allah ne shiyasa su ke fadin hakan.