HUKUMAR Daraktocin gidan talbijin na Tozali ta naɗa Kakakin Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), darakta kuma jarumi, Malam Al-Amin Ciroma, matsayin Janar Manajan tashar talbijin ɗin da ke Abuja.
A lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim, bayan ya ba da sanarwar naɗin nasa a Facebook cewa ya kama aiki, Ciroma ya ce ya na neman addu’a daga ‘yan’uwa, masoya da kuma abokan arziki.
Ya ce, “Abin da zan ce game da sabon aiki ko muƙamin da aka ba ni shi ne, neman dacewa wajen Allah da kuma addu’ar ‘yan’uwa, masoya da abokan arziki, saboda babban nauyi ne da ke buƙatar kyakkyawar natsuwa da sadaukarwa.
“Babban abu ma shi ne amana. To, ka ga duk san da aka ba ka amana, tilas ka yi tsayin daka, kada a samu matsala ta kowace fuska. Idan ka yi, ka kuma samu dacewa, sai Allah ya shigar maka cikin lamarin. Abin da na ke fata kenan.”
Ciroma ya ci gaba da cewa, “Na kama aiki kai-tsaye, wato a yau Litinin, 3 ga Maris, 2024, ranar da aka tabbatar min da muƙamin. Ka san da ma kuma an saba da aikin, ba wani abin a je a dawo ba ne.”
Da wakilin mu ya tambaye shi wane albishir zai yi wa abokan sana’ar sa ‘yan Kannywood game da muƙamin da ya samu, sai ya ce, “Albishir ɗin da zan yi wa ‘yan’uwa na a Kannywood shi ne su ɗauka cewa ‘Tozali TV’ nasu ne, domin akwai damarmaki da yawa da za su iya amfana da shi ta hanyoyi da yawa. Don haka, su taya mu da addu’a, shawarwari, sannan su sani ‘Tozali TV’ tasu ce!
“Daga ƙarshe kuma abin da zan ce game da ‘TOZALI TV’ shi ne, tasha ce wadda ta ke taka muhimmiyar rawa wajen taɓo kowane ɓangare na rayuwa, saɓanin wasu tashoshin da za ka iske daga nishaɗi sai nishaɗi.
“A nan Tozali, ba ɓangaren yaɗa labarai da ya shafi al’umma da babu. Sannan ta kere sa’o’in ta da dama wajen samun farfajiyar haskawa, tunda ana kama mu a manhajar DSTV da Go-TV da Startimes da Canal-Plus, har ma da yanar gizo.
“Don haka ‘Tozali TV’ ta na sahun gaba a dukkan ɓangarori.”
Shi dai Ciroma, ƙwararren ɗan jarida ne wanda ya taɓa riƙa muƙamai daban-daban, waɗanda su ka haɗa da Editan jaridar Leadership Hausa da kuma Janar Manaja na gidan talabijin na Farin Wata duk a Abuja.
![]()







