SHAHARARREN mai zane, marubuci kuma mawaƙi a Kannywood, Kamal Y. Iyan-Tama, ya yi rashin mahaifin sa a ranar Lahadi, 3 ga Fabrairu, 2024.
Allah ya ɗauki ran Malam Yunusa Abdullahi Barebari Ɗanbatta (Magaji) da misalin ƙarfe 7:30 na dare a gidan sa da ke Unguwar Mata, Malumfashi, Jihar Katsina, sakamakon rashin lafiya.
Ya yi ciwo a tsaitsaye, ya na harkokin sa; kwanciyar jinyar da ya yi ba ta wuce ta kwana takwas ba.
An yi jana’izar sa a gidan sa da misalin ƙarfe 9:00 na safe.
Dattijon, mai kimanin shekara 77, ya rasu ya bar matar sa ɗaya da ‘ya’ya 11. ‘Ya’yan su ne; Binta (Mamano Mardiya), Kamal Y. Iyantama, Shamwilat, Zainab (Hassana), Hajara (Hussaina), Bilkisu (Barrister), Khadija (Pretty Nanawo), Asma’u (Ma’u), Murja (Janaat), Ummu Salmah da Abdallah (Abba Auta).
Marubuta da sauran masoya sun taya Kamal alhinin rashin mahaifin sa, inda su ka yi ɗora ta’aziyyar su a Facebook.
Allah ya rahamshe shi, amin.
![]()







