• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An kai agaji ga Umaru Ɗan Ɗanduna da Shata ya waƙe

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
January 17, 2020
in Labarai
0
Alh. Umaru Ɗan Ɗanduna lokacin da aka kai masa ɗauki

Alh. Umaru Ɗan Ɗanduna lokacin da aka kai masa ɗauki

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
FITACCEN direban nan wanda Alhaji Mamman Shata ya waƙe, Alhaji Umaru Ɗan Ɗanduna, ya samu tallafin kayan abinci da kuɗin cefane daga wani bawan Allah.
 
Hakan ya biyo bayan wata hira da aka yi da ɗan jarida kuma marubuci Ibrahim Sheme a gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya na Kaduna kan fitacciyar waƙar nan ta Shata mai taken “Umaru Ɗan Ɗanduna Na Gwandu”, inda a ƙarshen hirar ya bayyana halin rashin lafiya da tsohon direban ya ke ciki.
 
To, sai wani bawan Allah wanda ya na ɗaya daga cikin dattawan Arewa ya tausaya wa Alh. Umaru Ɗan Ɗanduna bayan ya saurari hirar, kuma ya bada agajin kuɗi  N100,000 gare shi ta ta hanyar Sheme. 
 
Nan da nan Sheme ya tura marubuci kuma ɗan jarida Maje El-Hajeej Hotoro ya sanar da Alh. Umaru taimakon da aka yi masa, da sunan wanda ya bayar da kuɗin. 
 
Alh. Umaru ya yi murna ƙwarai da gaske tare da godiya ga wannan bawan Allah, wanda ba ya so a bayyana sunan sa.
 
Bisa shawara da Alh. Umaru da iyalin sa, sai Sheme da Maje su ka kasa wannan kuɗi gida biyu – tare da amincewar wanda ya bada kuɗin – su ka kashe N50,000 wajen saya wa Alh. Umaru kayan abinci domin akwai buƙatar su. 
 
A ranar Juma’a, 17 ga Janairu, 2019 aka kai kayan tallafin da kuma kuɗin inda aka miƙa su a gare shi a gidan sa da ke unguwar Gwanar Jaba a cikin garin Kano.
 
Wakilin mujallar Fim, wanda tare da shi Maje ya sawo kayan aka kai, ya ruwaito cewa kayan sun haɗa da buhun shinkafa, taliya, makaroni, man girki, sabulun wanka da na wanki, da sauran su.
 
Haka kuma an ba Alh. Umaru tsabar sauran kuɗin hannu da hannu.
 
A lokacin da ya ke karɓar agajin, tsohon direban ya ƙara yin godiya ga Allah dangane da wannan gudunmawa da aka ba shi, sannan ya ƙara gode wa mutumin da ya yi masa agajin.
 
Daga ƙarshe, Alhaji Umaru ya gode wa duk waɗanda su ka yi ɗawainiya don ganin saƙon ya isa gare shi.
 
Alh. Umaru Ɗan Ɗanduna tare da kayan agaji da aka kai masa
A nasa ɓangaren, shi ma Ibrahim Sheme ya ce: “Ina addu’ar Allah ya  saka wa wannan bawan Allah da alheri, kuma ya ba Alh. Umaru Ɗan Ɗanduna lafiya da nisan kwana, amin.
 
“Haka kuma ina addu’ar Allah ya jiƙan Alh. Mamman Shata, wanda a bayyane ta ke cewa duk da yake ya bar duniya amma har yanzu mutane su na cin arzikin sa ta hanyoyi daban-daban.”
 

Loading

Tags: agajidattawan ArewadirebaIbrahim ShemeKwanar Jaba KanoMaje El-Hajeej HotoroMamman ShataRediyon Tarayyar Nijeriya na KadunaUmaru Dan Danduna Na Gwandu
Previous Post

Ina matan Kannywood ke samun kuɗi su na zarya a ƙasashen waje?

Next Post

Yanzu babu girmamawa a Kannywood, inji jaruma

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Amina Abdullahi ta shafe kusan shekara 25 a harkar fim

Yanzu babu girmamawa a Kannywood, inji jaruma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!