• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yanzu babu girmamawa a Kannywood, inji jaruma

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
January 20, 2020
in Labarai
0
Amina Abdullahi ta shafe kusan shekara 25 a harkar fim

Amina Abdullahi ta shafe kusan shekara 25 a harkar fim

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA tsohuwar jaruma a Kannywood, Amina Abubakar, ta bayyana cewa yanzu masana’antar finafinan Hausa waje ne maras tsafta.

Jarumar ta faɗi haka ne a lokacin wata zantawa da ta yi da mujallar Fim inda ta kwatanta harkar fim a yau da yadda ake yin ta a da.

Ita dai Amina, ta shafe kusan shekara 25 ta na harkar fim. Ta fara tun ana wasan daɓe, zuwa dirama a gidan talbijin na CTV Kano, zuwa fim ɗin bidiyo har zuwa shirin ‘Kwana Casa’in’ na gidan talbijin na Arewa24.

A tattaunawar ta wakilin mu a Kano dangane da halin da harkar fim ta samu kan ta a ciki a yanzu, Amina ta ce, “A lokacin baya harkar akwai taimakon juna da ganin girman na gaba, ta yadda ko furodusa ko darakta idan akwai wanda ya ke gaba da shi to ya na girmama shi ne, ba zai kalli kan sa a matsayin darakta ba.

“Kuma duk lokacin da mu ka fita aiki za ka ga wajen zaman maza daban, na mata daban; kuma idan mace ta je da lulluɓi to har a gama aikin ta na tare da abin ta.

“Sannan babu maganar bambanci wajen abinci, duk haɗuwa ake yi a abinci iri ɗaya, wani lokacin ma matan da su ke wajen su ne za su dafa abincin.

“Amma yanzu abubuwa duk sun canza, babu wani mai girmama wani sai dai idan kai ake yayi sai a zo ana girmama ka, ana kamun ƙafa da kai.”

Jarumar ta ƙara da cewa, “Sam wannan ɗabi’ar babu ita a lokacin da aka kafa harkar fim. Daga baya ne aka shigo da ita.

“Wannan ya sa a yanzu rigingimu su ka yi yawa a masana’antar, aka kasa magance su, saboda babu mai ganin girman wani, kowa da inda ya sa gaba.”

Daga ƙarshe, Amina ta yi kira ga ‘yan fim da su dawo da kyawawan ɗabi’un da aka san harkar fim da su tun farkon kafuwar ta, domin wannan shi ne zai sa a samu ci-gaban da ake buƙata a masana’antar gaba ɗaya.

Loading

Previous Post

An kai agaji ga Umaru Ɗan Ɗanduna da Shata ya waƙe

Next Post

Kalmar ‘Kannywood’ ta shiga ƙamus ɗin Oxford

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Malam Sunusi Shehu Daneji (a dama) a cikin 2009. A hagu, ƙamus ɗin Oxford

Kalmar 'Kannywood' ta shiga ƙamus ɗin Oxford

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!