ƊIMBIN jama’a sun ci gaba da yin tururuwa zuwa gaisuwar mahaifiyar darakta Hafizu Bello, Gwaggo Hasiya Sidi Ishaq, wadda Allah ya yi wa rasuwa da misalin ƙarfe 6 na yamma a ranar Asabar, 8 ga Nuwamba.
An yi jana’izar ta a gidan su da ke Gyaɗi-Gyaɗi, kusa da Gadar Lado, a cikin garin Kano.
Gwaggo Hasiya ta rasu tana da shekaru 84 a duniya, kuma ta rasu ta bar ‘ya’ya shida da jikoki masu yawa.
Daga cikin ‘ya’yan ta akwai darakta Hafizu Bello, wanda ya kasance fitaccen darakta a Kannywood.
‘Yan fim da suka halarci jana’izar ta sun haɗa da Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, furodusa Sani Sule Katsina, darakta Bala Anas Babinlata da sauran ‘yan fim masu yawan gaske.
Da fatan Allah ya jiƙan ta, ya bai wa iyali da ‘yan’uwa haƙurin juriyar wannan babban rashin da aka yi.
![]()







