• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙasidar European Champions League

by DAGA FARFESA SALISU SHEHU
November 18, 2020
in Marubuta
0
Farfesa Salisu Shehu

Farfesa Salisu Shehu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Da Sunan Allah Shi ɗaya,
Zan fara bayani bai ɗaya. 
 
Rabbu Kai tilo ne Kai ɗaya,
Ba kama a gare Ka gaba ɗaya.
 
Duk halittun ƙas da samaniya,
Kai ne Ka yiwo su gaba ɗaya.
 
Rabbana saita mini zuciya,
Nai bayani ba wata zamiya.
 
Nai salati na yo tahiya,
Ga abin ƙaunar mu gaba ɗaya. 
 
Al-Bashiru aminin duniya, 
Ka ji mai ceton mu gaba ɗaya. 
 
Ni nufi na zan yi matashiya,
Ga shababu su bar sharholiya. 
 
Wataƙila a yo mini tambaya, 
Kan batun me za ka matashiya? 
 
Kan batun ƙwallon Birtaniya, 
Wofin banza na Pirimiya. 
 
Ko batun ƙwallo na Sipaniya, 
La Liga abin hauragiya. 
 
Ga Juventus can ta Italiya,
Waɗansu kan ta su ke ta hayaniya. 
 
Masu son ta su ce mata gimbiya,
Ba karatu sai dai tankiya.
 
Wasu har azumi fa su ke niyya, 
Don sadaukarwa ga Sipaniya, 
 
Ko su yo yankar ƙurbaniyya, 
Zallar ƙaunar Barceloniya. 
 
David Beckham tuni ya riya, 
Ba ya son ummah Islamiyya.
 
Haka ma Chelsean Birtaniya, 
Ba su son jinsin Ifrikiyya. 
 
Ga su Manchester Britaniya, 
Team ne biyu  ‘yan gabar tsiya. 
 
Masu son su a nan Najeriya, 
Ba su son juna gabar tsiya. 
 
In su na musun Manchestiya
Ka ga mamakin hauragiya.
 
Huruwar hanci da ta jijiya, 
Ga bankaura da hayaniya. 
 
Sun mance nasihar gaskiya, 
Sunnar Manzo Bahanifyya. 
 
Duk Musulmi kaf baki ɗaya, 
‘Yan’uwan juna ne bai ɗaya. 
 
Ya shababu ku zo duka bai ɗaya,
Ga nasiha kukan kurciya.
 
Kui riƙo da tafarkin gaskiya, 
Garkuwa kenan ga hayaniya. 
 
Duk samarin wannan nahiya, 
Mui ta himma ba hauragiya. 
 
Na tuno gargaɗi na mazan jiya, 
Zungur su Sa’adu abin biya.
 
“Mu dai ilimi mu ka tambaya, 
Ko a London ko a Arebiya”. 
 
Ya shababu ku lura da duniya,
Mai bugarwa ce tamfar giya.
 
Lokacin da mutum ya ji lafiya, 
Ba ya komai sai ɓarnar tsiya. 
 
Balle kuma in ya ga dukiya, 
Ta taru irin zinariya.
 
Sai ka gan shi ya na ta fahariya,
Ga hululu da yin sharholiya. 
 
Sai ya rinƙa zuwa Birtaniya, 
Old Trafford can a Sitadiya. 
 
Wani ko ya nufanci Italiya,
Inter Milan ‘yan hauragiya.
 
Ko ya zo shi ya ƙirƙiri ƙungiya,
Shi ya ke yanke mata cibiya. 
 
Yai ta kan renon ta da dukiya, 
Har ta kai wata ‘yar hamshaƙiya.
 
Maimakon ya yi zakkar dukiya, 
Ko ya yo sadaka mai jariya.
 
Amma sai dai ya yi tutiya, 
Wai ya na da zaratan ƙungiya. 
 
Ya Allah kai mana kariya, 
Daga bin sha’awowin zuciya
 
Kar mu faɗa ruɗun duniya, 
Mui ta bankaura da hayaniya.
 
Tabbatar mana tsarkin zuciya,
Mui ta addini bisa gaskiya. 
 
Nai salati na yo tahiya, 
Ga Aminu Rasulun gaskiya. 
 
Nai yabo kuma na yi ta godiya, 
Ga Alimu Ilahun gaskiya.
 
‘Yan Manchester United su na murnar ci 5-0 a kan kulob ɗin RB Leipzig a gasar Champions League da aka buga a ranar 28 ga Oktoba, 2020
Farfesa Salisu Shehu malami ne a Jami’ar Bayero, Kano
 

Loading

Previous Post

Bashir Abu Sabe ya zama jagoran marubutan Arewa

Next Post

Mai ƙarar Rahama Sadau ya haƙura

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Rahama Sadau

Mai ƙarar Rahama Sadau ya haƙura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!