A ranar 31 ga Agusta, 2017, a garin Saint Andrews na yankin Sukotland a kasar Birtaniya, an gudanar da wani taro a kan tasirin labaran shararren littafin nan mai suna ‘Dare Dubu Da Daya’ ga al’ummar duniya. Taron ya tara manazarta daga sassa na duniya, wadanda su ka hada da gabatar da makaloli. Farfesa Abdalla Uba Adamu, Mataimakin Shugaba (Vice-Chancellor) na Budaddiyar Jami’ar Nijeriya, (National Open University of Nigeria, NOUN), wanda fitaccen masanin adabin Hausa ne, shi ne kadai manazarcin da ya halarci taron daga nahiyar Afrika. Ya gabatar da makala a taron mai taken “We Are Not in Baghdad Anymore”. Bayan taron, AHMED ABBA ABDULLAHI na Sashen Hausa na gidan rediyon BBC ya yi hira da shi a London a ran 4 ga Satumba, inda Farfesan ya bayyana masa gudunmawar da ya bayar a taron. Ga hirar kamar yadda wakilin Mujallar Fim, IRO MAMMAN, ya rubuto ta daga faifan hirar:
BBC HAUSA: Farfesa, wace irin makala ka gabatar a taron na St. Andrews?
FARFESA ABDALLA: Makala na gabatar a kan yadda Abubakar Imam ya dauki labarai guda tara daga labaran ‘Dare Dubu Da Daya’ ya mayar da su zuwa Hausa. Kuma in na ce ya mayar da su zuwa Hausa, ba wai fassara su kawai ya yi ba, a’a, ya narkar da su ne; ya zamanto cewa idan ka karanta labaran na ainihi, sai kuma ka zo ka karanta wanda ya rubuta a ‘Magana Jari Ce’, ba za ka tab’a cewa ga daga inda aka samo wadancan labaran ba.
BBC HAUSA: Wato ya dauke su ya maida su nashi, ta yadda ba za a iya tantancewa ko fassara su aka yi ba?
FARFESA ABDALLA: K’warai da gaske. Shi kan sa ya fadi haka a cikin labarin da ya rubuta na tarihin rayuwar sa cewa maigidan sa, Rupert East, shi ne ya gaya masa ya ce da shi, “Ka nuna gwaninta a fassarar ka kamar yadda wanda ka ke fassarowa daga shi shi ma ya nuna gwaninta a yaren sa.”
BBC HAUSA: To amma Farfesa, wadanne ne daga cikin wadannan labarai tara? Ko za a iya fada mana wasu daga ciki saboda masu sauraren mu wadanda su ka karanta littafin?
FARFESA ABDALLA: Akwai “Kwadayi Mabudin Wahala”, akwai “Labarin Manomi Da San Sa Da Kuma Jakin sa”, da kuma “Babu Wahalalle Sai Mai Kwadayi”, da kuma “Alheri Danko Ne, Ba Ya Faduwa K’asa Banza”. Wadannan su ne kadan daga cikin wadanda ya dauko guda tara.
Alhaji (Dr) Abubakar Imam, OBE
BBC HAUSA: Shin akwai bambancin narkarwa da ake magana da kuma kamar yadda akan ce an baddala labari? Ko duk abu daya ne?
FARFESA ABDALLA: E to,ai baddalawa ne. Saboda an juya shi, an canja masa nau’in shi daga yadda ya fito a da, an dawo da shi wani nau’i na daban. Misali, yadda za ka dauka ka canja shi, ka canja sunayen, ka canja wuraren, ka canja akidar, ka canja kuma karshen labarin, ka canja manufar labarin, jigon labarin, farawar labarin da direwar sa. Duk wannan abin da Alhaji Abubakar Imam ya yi ne, ya caccanja, saboda haka ya baddala din kenan, ya riga ya narkar.
Inda ma ya fi fitowa sosai shi ne “Labarin Wani Mutum Da Sa”. A karshen labarin na ainihin, wani basarake ne ya samu matar sa ya yi mata dukan tsiya. Amma a yadda Abubakar Imam ya fassara shi ko kuma ya baddala shi, sai ya zamanto cewa duk wani magana na cin zarafin mata ya fitar da shi, ya watsar da shi. Saboda haka idan ka duba za ka ga cewa Abubakar Imam ya fi kyautata wa mata saboda a cikin labarin ma bai ma dauki matar ya kawo ta cikin labarin ba. Amma a na ainihin a karshe maigida ne ya samu matar sa ya kakkarya ta, ya yi mata dukan tsiya, saboda wani zakara ne ya ce da shi, “Ni ko in da ni ke da wannan matar, dukan tsiya zan yi mata,” kuma ya yarda ya dauka din, ya yi mata dukan tsiyan. To, ka ga ya nuna an wulakanta mata, ba a ba su mutuncin su ba. Amma shi Abubakar Imam bai kawo ma wannan ba. To, ka ga ya baddala labarin daban da na gaskiyar.

BBC HAUSA: To, kamar shi wannan littafi na ‘Dare Dubu Da Daya’ ko ‘Alfu Laila Wa Laila’, wane irin tasiri kenan za a ce ya yi a adabi na Bahaushe?
FARFESA ABDALLA: To, babban tasirin sa dai shi ne nuna gwanintar yadda ake baddala abu. Wannan ita ce kai-tsaye babban tasirin da zai yi. Sannan na biyu, akwai wani abu da mutane da yawa watakila ba su fahimta ba ko kuma ba su sani ba: babu wani littafi na Bahaushe da ya yi kamar ‘Magana Jari Ce’. Ko za ka ce gaskiya ne abin, wato kirkira ne, ko baddalawa ne ko ma dai menene, babu littafin adabin Bahaushe da ya ke da tasirin da ya yi kamar ‘Magana Jari Ce’ wajen nuna sarrafa labari da wajen kuma nuna akidar Bahaushe.
Kuma a yanzu haka wannan littafin, ‘Magana Jari Ce’, shi ne kadai a iya sani na littafin da aka fassara shi zuwa Larabci, aka fassara shi zuwa Polishanci. Saboda a yanzu haka a Egypt, a University of Cairo, an samu wani tsohon Farfesa ya dauki littafin ‘Magana Jari Ce’, tun daga littafi na 1 har na 3, duk labaran ya fassara su. To, ka ga abin mamaki shi ne, kamar wannan labaran da mu ka yi magana daga Larabci su ka taho, su ka shigo Hausa, yanzu sai su ka sake ficewa su ka koma Larabcin!
BBC HAUSA: A Hausa din na san an yi finafinai a kan shi.
FARFESA ABDALLA: E, an yi wasan kwaikwayo. Kuma an yi ma na rediyo. Ko mu na so, ko ba mu so, ko an yarda ko ba a yarda ba ya zama abin da ake ce wa classic, wato zakaran gwajin dafi. Wanda ya zamanto shi ne ya fito da martabar Bahaushe ko ya fito da rayuwar Bahaushe a cikin labari.

Ba yadda za a yi ka karanta ‘Magana Jari Ce’ ka ce daga Jamus aka dauko labarin ma, ko daga Indiya ko daga kasar Larabawa. Yanzu misali, ita kan ta akun kuturun daga Indiya aka dauko ta! Kuma shi ma yadda ya tsara labarin aku din, da farko ta zamanto kamar a ce ita ce matashiyar labarin, haka aka dauko a wancan labarin da ake kiran sa ‘Tutinama’, shi ma haka aka dauko labarin akun. Kuma ita ma sihirtacciya ce; wato enchanted su ke cewa, saboda ta na magana, ta na komai da komai. To, a karshen labarin Tutinama din, wanda aka yi amfani da aku, sai ita akun ta riga ta tashi ta yi sama ta b’ace.
To, amma ka ga a ‘Magana Jari Ce’, da aku kuturu namu na Kano ya yi nasara, sai aka maida shi Waziri. To, ka ga yadda ya dire labarin; har ya haihu ya samu da, sannan aka ci gaba da labarin.
BBC HAUSA: Farfesa, ga shi ka na magana game da batun irin gwaninta da shi marigayi Abubakar Imam ya nuna a wurin rubuta wannan littafi, amma sai na ji wasu na suka, su na cewa wadannan labarai ba kirkirar sa ba ce, kawai dai shi kamar fassarawa ya yi. Amma kuma ga shi ka nuna ba fassarawa ya yi ba. Me za ka ce ga masu wancan ra’ayi da ke nuni da cewa ba wata gwaninta ce ya yi ba, kowa ma na iya yin abin da ya yi?
FARFESA ABDALLA: To, ra’ayi dai ba gaba ba ne, ko? Kowa na da nasa ra’ayin. Kuma ra’ayi riga ce, kowa nasa zai sa. Tabbas, akwai masu wannan tunanin cewa ai babu wani abu da ya yi abin da ake kira original, wato kirkirar kan sa, kawai an dai dauka ne an ba shi ya yi. To, amma ba fa fassara ya yi ba. Sauran al’ummatan da mu ka yi nazari da su a St. Andrews University su fassara aka yi kai-tsaye, kalma da kalma aka dauka aka fassara zuwa wani yare. Saboda in da zai dauki na gasken da da yawa daga cikin abubuwan da ya fassara ba za su fassaru ba a rayuwar al’ummar Hausawa, ba su fahimci darussan da su ke ciki ba. Wanda yake ka tuna fa tun a shekarar 1937 aka yi wannan. To, wannan shekarun da ka yi wannan kusan za a ce shekara tamanin kenan, a lokacin aka yi wannan. Kuma duk abin da ya rubuta a lokacin, duk abin da aka baddala a lokacin za ka ga cewa babu wani bambanci da wancan lokacin da wannan lokacin. Babu wani abu da ya fada a wannan lokacin wanda ya ke ba rayuwar Hausawa ba ce. Kuma babu wani abu da ya dauko a cikin baddalawar tasa ya nuna cewa akwai wani abu na kishin-kishin na wata al’umma in ba Hausawa ba. Wannan gwanintar kadai ma ya isa a sara masa.
BBC HAUSA: Farfesa, me ya sa duk da wadannan labarai tara da Abubakar Imam ya tsakuro daga wannan littafi, akwai sauran labarai kamar irin su “Ali Baba and the Forty Thieves” da su “Aladdin’s Wonderful Lamp” da sauran abubuwa, ban sani ba kamar shi Ali Baba da b’arayi arba’in da fitila, me ya sa wasu ba su dauko irin wadannan labaran su yi koyi da shi marigayi Abubakar Imam ba, su ci gaba daga inda ya tsaya ba?
FARFESA ABDALLA: To, ai wanda su ke cewa ba abin da ya yi su kuma sai su yi mu gani, ko ba haka ba? In sun ce ba abin da ya yi, bai iya ba, yanzu an ba su dama, ka ba su kalubale, sai su dauko wancan labarin! Amma shi ya zauna ya dauki labaran da ya ke ganin cewa su na da wani darasi mai muhimmaci ga rayuwa. Kar ka manta, a lokacin ana neman littattafan da za a ba wa mutane su karanta a makarantun firamare da sakandire, saboda bokon bai yawaita ba, ana neman abubuwan da za a karanta. Saboda haka dole a samo labarai masu hikaya, labarai masu nuna rikon addini, labarai masu nuna kyakkyawar rayuwa. Shi ya sa ya tsamo wa’annan. Yanzu in ka ce za ka bada labarin “Alibaba da |arayi Arba’in”, ba a so a ji labarin b’arawo kwaya daya, ina kuma arba’in? Ka ga shi ya sa bai ma kula da wannan ba.

Kuma ba wai na ‘Dare Dubu Da Daya’ kawai ya tsaya a kai ba, a’a, ya dauko na Turawa ma da yawa daga Jamus, duk su ma ya baddala su. Misali, kamar labarin “Kalala Da Kalalatu” ai labarin Jamus ne. “Labarin Sarkin Busa” shi ma daga Jamus aka dauko shi.
BBC HAUSA: Ka ga wadannan abubuwa ne wadanda idan ba irin ku masana da su ka yi bincike a kai ba, da yawa wasu za su dauka labarai ne kawai shi ya zauna ya rubuta, kuma ba wai daga wasu wuraren ya aro ya baddala ya maida su nashi ba.
FARFESA ABDALLA: Shi ma bai fadi haka ba sai da aka zo za a rubuta tarihin rayuwar sa. Amma tunda daga lokacin da ya rubuta, har ya gama rubutun sa bai bayyana ina ya samo abin ba. Bayan shi ma akwai wadanda su ka yi irin wannan. Kamar misali labarin ‘Iliya Dan Maikarfi’, shi ma ba labarin Hausa ba ne. Amma shi wannan ba ma baddalawa ba ne, shi kai-tsaye fassara ne. Ai waka ce, ba wai labari ba ne ma! Waka ce ta wani jarumin su, ana kiran shi Ilya Muromets.
BBC HAUSA: To, Farfesa, ban sani ba a wurin wannan taro da ka gabatar da wannan makala taka, yaya su ka karb’i wannan yunkuri da shi Abubakar Imam ya yi? Su na ganin ya b’ata labarin ne ko kuma ya gyara shi?
FARFESA ABDALLA: A’a, ai su na ganin ya inganta labarin, ya bada wani fanni, wanda ya ke duk cikin mahalarta taron babu wani wanda ya kalli wannan fannin ko kadan. Hasali ma shi mai bada jawabin farko – wani Farfesa ne, wani Bajamushe, kuma wanda a yanzu haka dai a duniya shi ne kan gaba wajen nazari a kan ‘Dare Dubu Da Daya’ – wallahi ya yaba. Ya ce bai tab’a jin cewa an yi irin wannan baddalawar na ‘Dare Dubu Da Daya’ ba. Gaba daya rayuwar sa a kan ‘Dare Dubu Da Daya’ ta ke. Amma bai san an baddala ba saboda babu wanda ya tab’a fitowa a taron duniya ya ce ga abin da Abubakar Imam ya ke yi. Ana ta yin maganganu a kan Abubakar Imam, amma duk maganganun da hirarrakin a cikin mu ne a nan Kano, Zariya ne, Kaduna ne, a Nijeriya dai mu ke yi. Amma wannan shi ne karo na farko da aka fitar da abin aka kai shi wata duniya aka hadu da sauran mutane da su ma sun yi irin wannan a al’ummatan su. Sai aka ga ashe shi Abubakar Imam tashi gwanintar ta dara ta kowa.
BBC HAUSA: Farfesa, zan maida mu baya kadan. Shin wanene ainihin wanda ya rubuta wannan littafi ko ya kirkiro wannan labari na ‘Dare Dubu Da Daya’, da har yanzu ya samu karb’uwa a ko’ina a duniya?
FARFESA ABDALLA: Wato idan ka ce ga wanda ya rubuta shi zai yi wahala. An yi ittifakin cewa labarai ne aka tattaro su, aka harhado su, amma dai aka samu wani wanda har yanzu ba a san sunan shi ba ya hada su wuri daya, har su ka zama ‘Dare Dubu Da Daya’. ‘Dare Dubu Da Daya’ labari wanda ya ke kowane dare ana bada labari guda daya. Saboda kafin gari ya waye a ce za a kashe matar da ta ke bada labarin. Kamar yadda kowa ya sani, akwai Sarki da in ya auri mace, bayan ya sadu da ita, sai ya kashe ta. Haka ya rika yi har sai da ya kashe duk ’yan matan garin. Sai ya gaya wa Wazirin sa a je a nemo, to shi Wazirin ya na da ’ya’ya guda biyu mata, ya na ta tsoron ya fada wa Sarki ya na da ’ya’ya guda biyu, ya san kashe su za a yi.
To sai daya daga cikin su, Shaharazad, ta ce, “Kai ni wurin shi. Kar ka damu. Babu abin da zai faru.” To, daren farko kafin a kai ta wurin shi din sai shi uban nata, Waziri, sai ya ba ta labari, ya ce, “Ba na son rayuwar ki ta yi kamar matar da ta ke cikin wannan labarin.” Wannan labarin shi ne na wani dan kasuwa da jaki da kuma san sa, wanda shi ma Abubakar Imam ya dauko shi a matsayin labari na farko, wanda Waziri Aku kafin ya zama Waziri ya gaya wa Musa, ya na shirin ya fita, ya hana shi fita yaki. Shi kuma uban wannan yarinya ya yi mata nasiha ne da cewa, “Akwai fa wani abu da zai faru gare ki idan fa ki ka je wurin mutumin nan.” To shi ne fa daren farko. A dare na biyu aka kai ta wurin sa. Dare na yi sai ta hau ba shi labara. Haka tai ta ta yi, wanda sai ta kai wani matsayi da ya ke ya son ya ji me ya faru sai ta ce, “Sai gobe.” Sai ya ce to a bari sai gobe. Har aka yi kwana dubu da daya! Kwana dubu ne dai, amma a nasa da daya ne, saboda akwai na farko wanda ba a juya shi a cikin labarin da ita ta bayar ba. A karshe, ta ce, “Ni fa na zo karshen duk labaran da na ke da su.” Saboda haka ta saduda sai abin da ya yi. To, a lokacin shi kuma soyayya ta shiga zuciyar sa, sai ya ce, “Ai zan aure ki.” Shi kenan, ka ji yadda abin ya kare.”
Babu wanda zai ce da kai ga wanda ya rubuta littafin nan. Amma tasirin sa a duniya ya na da yawa. Ba na jin akwai littafi da ya ke da tasiri kamar sa. Har encyclopaedia aka yi masa, ‘Encyclopaedia of One Thousand and One Nights’. Saboda haka ya na da tasiri, ba za ka iya ce ga wane, ga wane wanda ya yi shi ba. Kuma kar ka manta, a kasar Hausa din ai Abubakar Imam ba shi ne ya fara fassara shi ba, in ma fassarawa ka ce. Akwai wani mutum ana kiran sa Frank Edgar, da shi da wani wai shi Malam Mamman Kano. To, Frank Edgar shi tatsuniyoyi ya ke nema, ya tattaro tatsuniyoyi, wurin shekarar 1911 ya ke tattaro tatsuniyoyi, sai a cikin tatsuniyoyin da ya ke tattarowa sai ya ga wasu ba na Hausa ba ne ma, ya ga karara ba su maganar rayuwar Hausawa, sai ya ce, “Wadannan tatsuniyoyin daga ina ku ka same su?” Sai su ka ce, “Daga ‘Alfu Laila Wa Laila’.” To, sai ya ware su daban, sai ya fassara su; ana gaya masa, ya na fassara su, a haka ya tattara ya yi abin da ke ce wa ‘polio’ – rubutun hannu – na duk wadannan labaran na ‘Alfu Laila Wa Laila’ din. Da aka buga na 1 da na 2, a lokacin ko wane abu ne ya faru? bai ci gaba da na 3 da na 4 da na 5 ba, sai Malam Mamman Kano ya ci gaba da na 3, na 4 da na 5. To amma kuma daga na dayan har na 5 din an tsaya ne a dare na 169. Kuma Hausar da aka yi, irin Hausa ce ta da, wacce ba ta da tsari yadda aka dai san Hausa a yanzu.
A shekarar 2013 Farfesa Ibrahim Malumfashi, wanda gaba dayan digirin sa na uku a kan ‘Magana Jari Ce’ da kuma irin yadda Abubakar Imam ya fassara labaran, da shi da wani ana kiran sa Bukar Mada da kuma wani Haruna Danladi, su uku su ka hadu a Facebook su ka ga cewa kamata ya yi littafin nan na shi Frank Edgar din a sake maimaita fassarar, wato a ingantacciyar fassara. Su ka hadu dai su ka samu kudaden da za su samu, sai su ka fassara su zuwa dare na 35, sai su ka yi sabon littafin, mujalladi na farko. Yanzu sun fito da shi, ya na kasuwa ana saida shi. Ka ga ‘Dare Dubu Da Dayan’ an sake yin shi.
To, amma shi Abubakar Imam a lokacin da ya ke aiki a kan ‘Magana Jari Ce’, bai ma waigi fassarar da Frank Edgar ya yi ba. Shi daga na Larabcin ya fassara, saboda ya iya Larabcin.
![]()







