LITTAFI: Kula Da Kaya…
MARUBUCIYA: Aunty Sadiya Kaduna
KAMFANI: Maizar Publishers & Printing Press, Zaria
SHEKARA: 2017
SHAFUKA: 152
FARASHI: N250
ISBN: Babu
MAI SHARHI: Lawan Muhammad PRP
AUNTY Sadiya Kaduna marubuciya ce da ta dad’e ta na rubutu. Ta rubuta littattafai masu d’an dama. Ita ce mawallafiyar mujallar ‘Marubuta’ da ta fara fita a shekarun baya.
Littafin ‘Kula Da Kaya…’ ya na bada labarin wata budurwa ce, Khadija, wadda aka had’a ta auren zumunci da d’an’uwan ta Sadik, duk kuwa da ba ta k’aunar auren nasa.
A dalilin haka ta dinga musguna masa ta hanyoyi da dama da su ka had’a da k’azanta, rashin tattali, da uwa-uba nuna masa k’iyayya. Tilas ta sa ya auro wata matar (Wafik’a) inda ya k’wace mata miji.
A hankali auren Khadija ya mutu, ta koma wa wani matashin likita, Dakta Abdurrahman (da ya tab’a nuna ya na son ta). Sai dai a gidan Dakta ma wani abin mamaki, Khadija ta samu sab’ani da shi saboda ba ya k’aunar tara ’ya’ya. Ba a dad’e ba auren ya rushe, rigima kuma ta ci gaba a gida domin Khadija na son komawa gidan tsohon mijin ta, Sadik.
WARWARAR JIGO
– An nuna rashin tattalin miji da kula da kai na iya sa wata ta shigo daga waje ta k’wace ragamar miji, kamar yadda ya faru ga Khadija.
– Auren son zuciya babbar illa ne ga mata, kamar yadda Khadija ta auri Dakta ta gamu da matsalar da ta fi ta gidan Sadik.
Zubi Da Tsari
An zubo labarin ne bisa lambobi har 26 tare da take a wasu lambobin. Tsarin labarin ya samu tangard’a a wasu wuraren, musamman wajen rufe labari ko k’ark’arewa. A zahiri bai kamata littafin ya k’are a haka ba.
SALO
An yi amfani da salo sassauk’a a labarin, ta yadda Hausar littafin ba za ta wahalar da mai karatu ba. Taurarin labarin sun taka rawar da ta dace, musamman Alh. Sani da Hajiya Ladi (iyayen Khadija). Garuruwan labarin sun dace da yanayin sa.
K’A’IDOJIN RUBUTU
An kiyaye k’a’idojin rubutu yadda ya kamata, musamman alamomin rubutu; sai dai a wasu wuraren ana yanke jimla a kai ta sakin layi na gaba. Misali, a shafi na 5 littafi na 1, wurin da Khadija ke gaya wa Asma’u k’iyayyar ta da Sadik. Kamata ya yi maganar ta k’are a sakin layi na 1.
KURAKURAI
- Littafin babu lambar ISBN, wadda ta na da matuk’ar amfani ga littafi.
- Khadija ba ta da takamaimiyar halayya a labarin; wani wurin a nuna mai addini ce, wani wurin a nuna mai k’arya ce.
- Idan Khadija na nuna halayyar k’azanta da rashin d’a’a ga miji don ba ta son sa, me ya sa ta ci gaba da yin halayyar a gidan wani mijin?
- Bai kamata Khadija ta koma gidan Sadik ba domin dai da ma ba ta son sa, sai dai idan saki uku ya yi mata ta yi auren kashe wuta da Dakta.
- Duk zaman lafiyar da Wafik’a ke yi da mijin ta sai ga shi an kashe ta a labarin ba laifin tsaye ba na zaune. Da alama Khadija ce gwanar marubuciyar!
Duk da haka, marubuciyar ta yi k’ok’ari. A gaida Aunty Kaduna.