• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Rarara: Zan tsaya takarar Majalisar Tarayya a 2023

by DAGA EL-ZAHARADEEN UMAR
October 25, 2021
in Labarai
0
Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara)

Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHAHARARREN mawaƙin nan kuma ɗan siyasa, Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara), ya bayyana cewa lallai maganar da ake yawo da ita ta batun tsayawar sa takarar zama ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Bakori da Ɗanja da ke Jihar Katsina gaskiya ce.

Rarara da kan sa ya  tabbatar wa da mujallar Fim haka a Katsina a wata zantawar da ta yi da shi a kan wasu batutuwa da su ka shafi waƙoƙin sa, musamman waƙar da ya ce talakawa ne su ka biya kuɗin yin ta da kuma batun tsayawar sa takara.

Ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu akwai batun sabuwar waƙar da ya yi wadda talakawa su ka biya kuɗi domin bayyana ayyukan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Ya ce kwanan nan zai tsunduma zagaya jihohin Nijeriya domin nuna irin ayyukan da ya gano Buhari ya yi.

Ya ce, “Idan Allah ya sa na kammala wannan aikin da ke gaba na, to zan tsaya takarar ɗan Majalisar Tarayya na Ƙananan Hukumomin Bakori da kuma Ɗanja. Idan kuma wannan aiki ya sha gaba na, sai kuma a duba batun nan gaba.”

A cewar Rarara, ya yi niyyar gano ayyukan Shugaban Ƙasa guda 90 amma sai ya gano 900,000 wanda ya ke ganin aikin ya na da yawa, amma dai idan ya samu damar kammala wannan aikin zai dawo kan batun yin takarar sa wanda tuni ya fara yawo a gidajen siyasa.

Rarara ya bayyana cewa zaɓen shugabannin siyasa da aka gudanar a makon jiya a Katsina ya yi masa kyau, kuma ya yi yadda ake so, saboda haka ya na fatan wannan zaɓen zai taimaka wajen ƙara samun nasarar jam’iyyar su ta APC a zaɓe mai zuwa.

Bugu da ƙari, mawaƙin ya yaba da irin tsarin da aka bi wajen samar da shuwagabannin, ya ce abin ya yi matuƙar burge shi, kuma a Nijeriya babu inda aka yi abin da ya dace kamar Jihar Katsina.

Ya ce hatta Shugaban Ƙasa ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Aminu Bello Masari a kan haka.

Rarara ya ce, “Idan ka duba da kyau, tun daga zaɓen shuwagabanni na matakin rumfuna da ƙananan hukumomi da na jiha babu wanda ya ce bai yarda da tsarin da aka bi ba, saboda haka wannan shi ne ake kira shugabanci. 

“Masari ya yi matuƙar ƙoƙari wajen haɗa kan ‘yan jam’iyyar APC a Jihar Katsina.”

Loading

Tags: Aminu Bello MasariAPCBakoriDanjaDauda Kahutu RararaHouse of RepresentativesMajalisar Wakilai ta Tarayyamawakan hausaShugaba Muhammadu Buharisiyasatakarazabe
Previous Post

Zuwa ga Adam A. Zango: Ina aka kwana da marayun ka na Zariya?

Next Post

‘Yan sanda na binciken yadda jarumi ya harbe mai shirya fim da bindiga a lokeshin

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Lokeshin ɗin shirya fim ɗin 'Rust' inda aka yi kisan

'Yan sanda na binciken yadda jarumi ya harbe mai shirya fim da bindiga a lokeshin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!