BABBAN furodusa Alhaji Sani Sule Katsina ya ɗora laifin durƙushewar kasuwancin finafinan Hausa a kan sauyawar zamani da rashin bin zamani da ‘yan fim su ka yi da farko.
A cewar sa, laifin ba na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da shugaban ta Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah) ba ne kamar yadda wasu su ke iƙirari. Maimakon haka ma, hukumar ta taimaki industiri ta hanyoyi daban-daban, inji shi.
Idan kun tuna, a ranar Alhamis da ta gabata, 3 ga Yuni, 2021, mujallar Fim ta wallafa hira da shugaban riƙo na ƙungiyar ƙwararru ta masu shirya fim ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, Alhaji Salisu Mohammed (Officer), inda ya bayyana cewa Afakallah ne ke yin amfani da hukumar sa ya na daƙile cigaban masana’antar shirya finafinan.
Amma a martanin da ya yi kan wannan batu, Alhaji Sani Sule Katsina, wanda ya na daga cikin manyan masu shirya finafinai kuma shi ne shugaban ƙungiyar ‘Kannywood Distribution Network’, ya ce ba haka abin ya ke ba.
A zantawar sa da mujallar Fim a ofishin sa da ke Kano, Alhaji Sani ya kawo wasu dalilai da ya ce su ne su ka jawo wa Kannywood koma-baya amma mutane irin sa su na ƙoƙarin ganin an magance su don a gudu tare a tsira tare.
Ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano mai ci yanzu ta bai wa Kannywood gudunmawa ɗari bisa ɗari domin cigaban ta.
Shugaban ƙungiyar ya ce, “A tunani na, ina ganin ba abin da ya haɗa taɓarɓarewar kasuwancin fim da Hukumar Tace Finafinai. Yanayi ne da zamani ya zo ya cinye wancan tsohon kasuwancin. Kuma mu tun tuni ba mu hango cewa wannan za ta faru ba ballantana mu je mu karɓo wannan abu mu fara amfani da shi, ba mu yi ba har sai da abin ya ci ƙarfin mu sannan mu ka tashi.
“Kusan in ce yanzu abin ya ci ƙarfin mu ne, shi ya sa mu ka yi farga mu ka fara hoɓɓasan tashi daga yanda mu ka tsinci kan mu zuwa cusa kan mu cikin jerin masu tafiya da zamani.
“Wanda kuma ba fim ya ke yi ba ba zai iya bada hukunci daidai ba, amma mu da mu ke sa kuɗin mu mu ke fim kuma mu ke badawa sannan mu ke kasuwancin sa, mu mu ka san ya za a yi ya ake yi.”
Ya bada misali da kan sa, da ya ce, “Ni da man tun tuni na daɗe da hango cewa hakan za ta kasance, shekaru masu tsawo wannan kasuwar ta sidi tuni za ta mutu. Shi ya sa na yi tsalle na faɗa harkar gidan talbijin, kuma ba abin da za mu ce sai godiya ga Allah.”
Amma Alhaji Sani ya yi gargaɗin cewa zuwan soshiyal midiya ya fara durƙusar da harkar talbijin ɗin ma. Ya ce, “Duk da kallon da ake yi wa wannan ɓangare na talabijin, shi ma fa yanzu ya ja baya saboda yanayin zamani da ya zo na soshiyal netwok; wasu abubuwan ma ka na zaune za ka duba a waya ka kalla.
“Gaskiyar abin shi ne kawai mu yarda da zamani ya zo, mu amshi zamani ko kuma a yi a bar mu, amma kar mu ɗauki laifun mu na rashin tunani da rashin tunanin mu na hangen nesa mu ɗora wa wani. Don ba mu da hujja da hurumin da za mu kare kan mu, sai mu ɗauka mu ɗora wa wani laifi.”
A cewar sa, akwai ma inda Afakallah ya taimaki masana’antar. Ya ce, “Idan ma adalci za mu yi, Hukumar Tace Finafinai ta taimaka wajen farfaɗo da wani ɓangaren kasuwancin da da ba a yi, inda ta zaunar da ‘yan ‘downloading’ da su ke satar kayan mu su je su na saidawa, aka zo hukumar ta zaunar da su ta nuna masu aibun abin kuma ta haɗa mu da su domin kasuwanci, su na karɓar kayan mu su na saya su na biya, duk da cewa ba za a iya hana wannan sana’a ta ‘dowloading’ ba don su ma su na ci su na sha da sana’ar.
“Ka ga wannan wani abu ne da hukumar ta zo mana da shi na cigaba.
“Shi ya sa shi ɗan’adam ba a iya masa. Maimakon a yi ma abin kallon alheri, ka gani ka yi godiya, sai kuma ka gani ka kushe.”

Alhaji Sani ya yi hannun-ka-mai-sanda da ya ce, “Duk da dai ban ɗora wa wani laifi ba, wanda ba ya harkar bai san ta ba. Amma mutum ya na cikin mu ba ya sa kuɗin sa, dole ya ce waɗannan abububuwan saboda bai san ya ake ciki ba.”
Bugu da ƙari, babban furodusan ya bayyana irin faɗi-tashin da furodusoshi irin sa su ke yi tare da Hukumar Tace Finafinan wajen ganin an farfaɗo da gidajen kallo na gargajiya domin dawo da martaba da al’adar da aka fara mantawa da ita na zuwa gidajen kallo domin kallon finafinan Hausa.
Ya ce hakan na faruwa ne “baya ga irin muƙamai da gwamnatin ke bai wa ‘yan masana’antar domin tunawa da cewa su ma su na da irin gudunmawar da za su bayar wa al’umma.
A cewar sa, “Wannan ma abin alfahari ne ga duk wani ɗan Kannywood, wanda a baya so aka yi a kori ‘yan fim daga jihar ma gaba ɗaya.”
Ya bayyana cewa a irin ci gaban da su ka samu da tallafi a ƙarƙashin hukumar, “gwamnatin Kano ta fitar da zunzurutun kuɗi domin ɗaukar wasu daga cikin mu a yi masu horo kan dabarun gudanarwa da inganta sana’ar fim don samun ƙwarewa a sana’ar.”
Ya yi wa Salisu Officer da masu tunani irin nasa matashiya da cewa, “Ya kamata a ajiye duk wata dangantakar siyasa da bambancin siyasa, mu tsaya mu fuskanci gaskiya.
“Duk mai kishi kamata ya yi ya tsaya wajen ganin ya za a yi a samu cigaba, ya ga ya za a yi gwamnati ta taimaka, ba wai ya yi faɗa da ita ba ya ruguza dangantakar da mu ke da ita ba.
“Ko mutum ya so ko bai so ba, ko siyasa ta ja ya rufe idon sa, irin gudunmawar da Hukumar Tace Finafinai ta bada kusan kaso 90 a cikin 100 shi ya ke riƙe masana’antar.
“Kuma idan ka haɗa wannan gwamnatin da waɗanda su ka shuɗe, ba wacce ta ke kula da ‘yan fim da ba su gudunmawa kamar wannan.”
Sani Sule ya yi kira da a faɗaɗa hanyar kasuwanci a soshiyal midiya ta hanyar shigar matasa cikin ta gadan-gadan, inda ya ce, “Zan yi amfani da wannan damar in yi kira ga yaran da mu ke da su a cikin wannan masan’anta masu basira da su dinga buɗe shafuka a yanar gizo ko samar da wata manhaja da za a dinga ɗora finafinai domin su ma a zo a dama da su ta hanyar karɓar finafinan sauran abokanan sana’ar su da ba su da basira irin tasu su na sawa su ma su na ƙaruwa da su ta yadda za su koma su ƙara yin wani aikin tare da taimaka wa matasa da rage zaman banza da ke kai matasa shiga wani hali na Allah-wadai.
“Ba na mantawa, a lokacin da mu ka shiga wani hali a wannan masana’anta, zuwan YouTube ya taimaka matuƙa wajen farfaɗo da masana’antar. Duk da cewa ba a samun abin da ake tsammani na riba, amma dai YouTube ya taimaka matuƙa wajen jawo hankalin matasan mu, sannan ya samar wa da mutane hanyar cin abinci, musamman yadda ake shirya finafinai masu dogon zango.”