• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 24, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abban mujallar Fim ya zama angon Jamila

by DAGA WAKILIN MU
June 5, 2021
in Ranar Murna
0
Abban mujallar Fim ya zama angon Jamila
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DUKKAN godiya ta tabbata ga Allah (SWT). Kamar yadda mu ka sanar da ku za a ɗaura auren editan mujallar Fim, wato Abba Muhammad, da sahibar sa Jamila Ibrahim Dassi, cikin yardar Allah an ɗaura auren kamar yadda aka tsara.

An ɗaura auren a ranar Juma’a, 4 ga Yuni, 2021 da misalin ƙarfe 1:40 na rana, bayan an idar da sallar Juma’a, a masallacin Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da ke Unguwar Dosa, Kaduna, a kan sadaki N70,000.

Ɗimbin jama’a da su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da ‘yan siyasa kamar su tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi, Honarabul Mukhtar Isah Hazo (baban amarya), Dakta Auwal Abdullahi Aliyu (waliyyin amarya, ɗan majalisa mai wakiltar Zariya da Kewaye, Honarabul Ahmad Muhammad Chokali, ɗan majalisar Jihar Kaduna mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Sanga, Honarabul Halliru Gambo Dangana, da sauran su.

Daga hagu zuwa dama: Hon. Ahmad Chokali, ango Abba, mahaifin amarya Hon. Muktar Isah Hazo, Hon. Halliru Sangada, Dakta Auwal da sauran jama’a a wurin ɗaurin auren

A ɓangaren iyayen ango akwai mahaifin ango, Malam Muhammad Aliyu Giɗaɗo, da Malam Shehu Mu’azu (wakilin ango), Malam Lawal Muhammad Giɗaɗo, Malam Yakubu Aliyu Giɗaɗo da Malam Nasiru Muhammad Giɗaɗo.

Sauran manyan baƙi da ‘yan fim sun haɗa da Alhaji Kabiru Assada, Malam Rabi’u Yunus Agege, Malam Aliyu A. Gora II, Malam Shafi’u Usman Namaigero, Mista Akintunde Adebayo, Isah Bawa Doro, Ɗayyab Maiɗa’a, Ibrahim Al-Imash, Ahmad Yariman Tiga, Abdulrahmna Ɗan Gwal, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Lawal Mai Atamfa, Nafi’u Bigi, Muhammad S. Yaro, Ibrahim Baba Iro, Muhammad Busra, Hamza Isah Ahmad, Mubarak Sa’id, Ibrahim Sani, Abdurasheed Muhammad, Abdullahi Abu Uku, Nuhu S. Aliyu, Usman A.A. Rasheed, A.A. Rasheed Kabala, Adamcy Khan, Auwal Yahaya DG, Ibrahim 2-Effects Isma’il I.E.C., Rabi’u Gamji, Salisu Dage, Yusuf Muhammad, Ibrahim Ɗanguziri, Modibbo Muhammad, da sauran su.

An ɗaura auren Abba da Jamila

Kafin ranar ɗaurin auren dai an gudanar da shagulgula kamar haka:

* Ranar Ƙauyawa (Ƙauye Day) – Litinin, 31 ga Mayu inda amarya da ƙawayen ta su ka yi shiga irin ta ‘yan ƙauye, su ka ci dambu da su magaryar da sauran kayayyakin gargajiya;

* Wankan Amarya (Bridal Shower) – Talata, 1 ga Yuni, inda aka yi biki, shi ma na amarya da ƙawayen ta;

* Gasar ƙwallon ƙafa – Laraba, 2 ga Yuni, wadda aka yi a filin wasa na Ahmed Musa Neighbourhood Centre da ke Sabon Hanya, unguwar Kamazo, Kaduna. 

Ango da mahaifin sa, Malam Muhammad Aliyu Giɗaɗo, a wurin ɗaurin auren

An buga gasar tsakanin ‘yan gidan ango da ‘yan gidan amarya, inda aka tashi 3-3. 

Ango da abokan sa sun halarci wurin, haka ita ma amrya da ƙawayen ta;

* Kamu – Alhamis, 3 ga Yuni, inda aka yi biki a gidan su amarya da ke Legistilative Quarters, Kaduna. An fara bikin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, inda ango da amarya su ka shiga filin taron, aka umarce su da su zauna a inda aka tanadar masu.

Abba, Jamila da mahaifin amarya Hon. Muktar Isah Hazo jim kaɗan bayan an ɗaura auren

Da farko an buɗe taro da addu’a, daga nan kuma aka shiga abin da ya tara jama’a a wurin. An kira amarya da ango tsakiyar fili don su taka rawa a gaban ‘yan’uwa da abokan arziki. Bayan sun koma sun zauna kuma, sai aka kira Ɗanladiyo Mai Atamfa tare da Nafeesa Yahaya Maiyaƙi, su ka nishaɗantar da taron da waƙar da su ka yi wa ango da amarya.

An ci gaba da shagali har zuwa ƙarfe 8:00 na dare, inda a wannan lokaci ne aka sallami kowa. 

Mahaifiyar amarya, Hajiya A’isha, tare da ango da amarya da kuma waliyin amarya, Dakta Auwal Abdullahi Aliyu jim kaɗan bayan an ɗaura auren

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci bikin sun haɗa da Dakta Auwal Abdullahi Aliyu, Ibrahim Al-Imash, Musa Mairabo, Isah Bawa Doro, Agga Bawan Mata, Murtala Darakta, Salisu Dage, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Muhammad S. Yaro, Muhammad Busra, Ibrahim Baba Iro, Hamza Isah Ahmad, Ahmad Yariman Tiga, Nafeesa Yahaya Mai Yaƙi, A.A. Rasheed Kabala da sauran su. 

* Ɗaura Aure – Juma’a, 4 ga Yuni. Bayan an ɗaura auren da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, an yi bikin Ranar Iyaye Mata (Mothers Day). Da misalin ƙarfe 7:00 na yammna kuma aka ɗauki amarya zuwa ɗakin mijin ta da ke unguwar Kinkinau, Kaduna.
 Mu na fatan Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

Mahaifiyar amarya, Hajiya A’isha, tare da amarya da ango da kuma ƙanwar amarya, Maryam Ibrahim a wajen shagalin kamu
Daga hagu: Bawan Mata, amarya Jamila, ango, Isah Bawa Doro da Murtala a wurin bikin kamu
In ba ku, ba gida…: Ƙawayen amarya a wurin shagalin kamu
Ɗanladiyo Mai Atamfa da Nafeesa Yahaya Maiyaƙi na nishaɗantar da taro
Ango a tsakiyar abokan sa a ranar kamu

Loading

Tags: Abba MuhammadAbba Mujallar FimFim Magazinehausa filmsHausa weddingJamila Ibrahim DassiKannywood
Previous Post

Mabiya miliyan 1: Daso ta shiga ƙwaryar manya a Instagram

Next Post

Cewar Sani Sule Katsina: Zamani ne ya rusa kasuwancin Kannywood, ba Afakallah ba

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Cewar Sani Sule Katsina: Zamani ne ya rusa kasuwancin Kannywood, ba Afakallah ba

Cewar Sani Sule Katsina: Zamani ne ya rusa kasuwancin Kannywood, ba Afakallah ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!