• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Dinar aure: An yi wa jarumin Kannywood Jamilu Kochila ruwan naira

by ABBA MUHAMMAD
August 3, 2025
in Ranar Murna
0
Dinar aure: An yi wa jarumin Kannywood Jamilu Kochila ruwan naira
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A DAREN jiya a Kaduna masoya suka yi wa jarumin Kannywood Jamilu Adamu Kochila babbar kara a wurin dinar auren da ya yi.

Da ma al’ada ce a Kannywood duk jarumin da zai yi aure babban burin sa ya yi dina ta kece raini, domin a nan za ka ga kusan kowa a masana’antar ya hallara.

A nan sai ba a bar Kochila a baya ba.

Bayan ɗaura auren sa da kuma walima da aka yi tun da fari, sai shirya ƙasaitacciyar dinar a babban ɗakin taro na Ahmed Musa Neighbourhood Centre da ke Yakowa Express Way, Unguwar Kamazo, Kaduna.

Tun kafin isowar ango da amarya, ɗakin taron ya cika maƙil, inda jarumai mata suka nuna wa abokin sana’ar nasu kara, domin kusan dukkan tsofaffi da sababbin jarumai sun halarci bikin.

Hadiza Kabara, Wasila Isma’il, Fati Ladan, Maijidda Ibrahim da Hadiza Maikano a wurin dina

Haka kuma manyan mutane, maza da mata sun halarta, wanda hakan ya nuna cewa jarumin yana da kyakkyawar alaƙa da mutane.

Ango da amaryar sa Sa’adatu sun shigo ɗakin taron da misalin ƙarfe 10:15 na dare. Daga nan kuma sai aka fara gudanar da abin da ya tara mutane.

Bayan an buɗe taron da addu’a, sai aka buƙaci aminin ango da aminiyar amarya da su zo su ba da taƙaitaccen tarihin aminan nasu.

Daga nan aka kira uban taron, Alhaji Yerima Shettima, wanda ya kasance shi ne uban ango da ya fito ya sanya wa sababbin ma’auratan albarka.

Alhaji Yerima Shettima da matar sa tsohuwar jaruma a Kannywood, Hajiya Fati Ladan

Yerima ya ce, “Ina roƙon Allah (s.w.t.) ya sa albarka a cikin wannan aure. Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba. Muna roƙon Allah ya dauwamar da zaman lafiya a tsakanin su.”

Mawaƙiya Hajiya Hadiza Maikano ta nishaɗantar da taron da waƙoƙin ta masu daɗi.

Umar MB na nishaɗantar da taro

Sai kuma aka shiga fagen ba da gudunmawa ga ango da amarya. Mutanen ango sun nuna masa ƙauna, domin an tara masa kuɗi kimanin N13,040,000.

Hajiya Shafa Wali ita ce wadda ta fara buɗe fagen ba da gudunmawar, inda ta ba da N3,000,000 ga ango, tufafi kala 20 ga amarya, ta kuma ba DJ N500,000, MC N500,000.

Sai kuma ɗan ƙwallon Nijeriya Ahmed Musa ya ba da N5,000,000, Alhaji Baballe Na-Abba N2,000,000, Alhaji Abdulfatah Murtala N1,000,000, Momee Gombe N1,000,000, Teema Makamashi N500,000, Hajiya Farida Musa Jauro dala 400.

Abdullahi Shehu, Ahmed Musa tare da ango da amarya a wurin dina

Kamar yadda mai gabatarwa, Alhaji Jibril Sulaiman (MC Big Boy), ya ce, wannan ya fi duk wani raye-raye da za a yi a nan wajen.

Daga nan kuma mawaƙa irin su Umar M. Shareef, Umar MB da Auta Waziri suka cigaba da nishaɗantar da taron.

Fati Ladan, Wasila Isma'il da Mansura Isah a wurin dina

Wasu daga cikin waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Yerima Shettima, Alhaji Yakubu Lere, Alhaji Rabi’u Rikadawa, Alhaji Yusuf Dingyaɗi, Alhaji Baballe Na-Abba, Alhaji Abdulfatah Murtala, Alhaji Abdul Amart, Alhaji Ahmed Musa, Alhaji Shehu Abdullahi, Manjo Nura, Mista Ɗanjuma Don J, Hajiya Fati Ladan, Mansurah Isah, Maijidda Ibrahim, Hadiza Kabara, Fati Washa, Fati S.U. Garba, Teema Yola, Fanan Buzuwa, da Madam Korede.

An tashi daga taron da misalin ƙarfe 12:45 na dare.

Loading

Tags: auredinaJamiluKochilaKannywood
Previous Post

Jarumi a Kannywood, Jamilu Kochila da Sa’adatu sun zama ɗaya

Next Post

Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta yi aure

Related Posts

Marubuci kuma furodusa Zubairu Musa Balannaji zai yi aure a ranar Lahadi
Ranar Murna

Marubuci kuma furodusa Zubairu Musa Balannaji zai yi aure a ranar Lahadi

December 26, 2025
Darakta Aminu Saira ya yi walimar buɗe gidan da babu mai irin shi a Kannywood 
Ranar Murna

Darakta Aminu Saira ya yi walimar buɗe gidan da babu mai irin shi a Kannywood 

December 20, 2025
Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa
Ranar Murna

Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

December 14, 2025
Darakta a Kannywood, Balarabe Murtala Baharu zai yi bikin auren da ɗan sa ranar Asabar
Ranar Murna

Darakta a Kannywood, Balarabe Murtala Baharu zai yi bikin auren da ɗan sa ranar Asabar

December 3, 2025
Shekaru 10 da aure: Ba wanda ya taɓa jin kan mu tsakani na da mata ta – Adam M. Adam
Ranar Murna

Shekaru 10 da aure: Ba wanda ya taɓa jin kan mu tsakani na da mata ta – Adam M. Adam

December 3, 2025
Aure: Ahmad Yariman Tiga ya zama cikakken mutum
Ranar Murna

Aure: Ahmad Yariman Tiga ya zama cikakken mutum

November 28, 2025
Next Post
Jaruma Rahama Sadau ta yi aure

Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta yi aure

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!