ALLAH ya yi wa mahaifin furodusa a Kannywood, Alhaji Abubakar Musa, wanda aka fi sani da Abubakar Anka, rasuwa.
Malam Musa Haruna Namairi ya rasu ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9:00 na dare a gidan sa da ke shiyyar Magaji a cikin garin Anka, Jihar Zamfara.
An yi jana’izar sa a ranar Asabar, 10 ga Agusta, da misalin ƙarfe 10:00 na safe a gidan sa.
Marigayin mai kimanin shekara 129 a duniya ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Dattijon ya rasu ya bar ‘ya’ya 2, duk maza, da jikoki 33.
Allah ya jiƙan shi da rahama.
![]()







