• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Kano ta sha alwashin za ta kare martabar harshen Hausa

by DAGA MUHAMMAD RANO
December 10, 2020
in Labarai
0
Nura M. Inuwa ya na karɓar kyautar karramawa daga hannun Dakta Gawuna

Nura M. Inuwa ya na karɓar kyautar karramawa daga hannun Dakta Gawuna

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
* An karrama Nura M. Inuwa da Falalu Ɗorayi
 
 
GWAMNATIN Jihar Kano ta jaddada ƙudirin ta na cigaba da zaƙulo managartan hanyoyi da za su kare martabar harshen Hausa.
 
Mataimakin Gwamnan jihar,  Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, shi ne ya bayyana haka a wajen taron kammala gasar kacici-kacici tsakanin manyan makarantun gaba da sakandare da ke faɗin Jihar Kano kan harshen Hausa, wanda Ƙungiyar Ɗaliban Hausa ta Nijeriya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Muryar Hausawan Duniya ta shirya.
 
Mataimakin gwamnan ne ya ɗauki nauyin shirya gasar, kuma an gudanar da taron a Jami’ar Bayero, Kano.
 
A jawabin nasa, Gwuna ya bayyana harshen Hausa da cewa ya yi fice a cikin harsunan duniya.
 
Ya nanata burin sa na ci gaba da bada gudunmawar sa wajen kare martabar harshen da bunƙasa shi ta hanyar shirya irin wannan gasar.
 
Gawuna ya ce gwamnatin jihar, a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta maida hankali wajen samar da  ilimi tun daga tushe.
 
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta samar da shirin ta na ilimi kyauta kuma dole domin samun al’umma mai nagarta.
 
Daga nan mataimakin gwamnan ya taya waɗanda su ka samu nasara murna tare da kira ga ɗalibai da su maida hankali ga karatun su domin samun cigaba.
 
Su Tijjani Asase, Falalu Ɗorayi da Nura Ɗandolo a wajen taron
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban jami’ar (VC), Farfesa Sagir Adamu, wanda Farfesa Hafizu Miko ya wakilta, ya yaba da ƙoƙarin Dakta Gawuna bisa kulawar sa ga cigaban ilimi a jihar.
 
Wakilin mujallar Fim ya shaida mana cewa a yayin gasar dai Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) ce ta zo ta ɗaya, sai Jami’ar Bayero da ke biye mata a matsayin ta biyu, inda Kwalejin Nazarin Harkokin Shari’a ta Kano ta zo ta uku.
 
A taron, an karrama babban mawaƙi Nura M. Inuwa da fitaccen darakta kuma mashiryin diramar ‘Gidan Badamasi’ ta tashar Arewa24, Falalu A. Ɗorayi, da lambar girmamawa sakamakon irin gudunmawar da su ke bayarwa ga cigaban harshen Hausa.
 
A ƙarshe, mawaƙan Kannywood sun nishaɗantar da jama’ar da su ka halarci taron, ciki har da Nura M. Inuwa da Nura Ɗandolo da kuma wasu mawaƙan hip-hop da ake kira Fresh Emir.
 
Taron ya samu halartar jaruman Kannywwod irin su Tijjani Asase, Umar M.S. Jigirya, Murtala Karabiti, Ado Ahmad Gidan Dabino, Ɗandolo da sauran su.

Loading

Previous Post

Buhari ya rantsar da Yakubu a matsayin Shugaban INEC a karo na biyu

Next Post

Mawallafin jaridun Leadership da A Yau, Sam Ndah-Isaiah, ya rasu

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Marigayi Mista Sam Nda-Isaiah

Mawallafin jaridun Leadership da A Yau, Sam Ndah-Isaiah, ya rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!