• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya da Sarkin Musulmi sun amince wa Rahma Abdulmajid ta shirya fim kan Nana Asma’u ‘yar Shehu Ɗanfodiyo

by ALI KANO
November 26, 2025
in Labarai
0
Gwamnatin Tarayya da Sarkin Musulmi sun amince wa Rahma Abdulmajid ta shirya fim kan Nana Asma’u ‘yar Shehu Ɗanfodiyo

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, da Hajiya Rahma Abdulmajid

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Ma’aikatar Sana’a, Masana’antu da Zuba Jari ta Tarayya tare da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, sun amince wa Hajiya Rahma Abdulmajid ta shirya wani fim kan rayuwa da tsatson fitacciyar malama kuma marubuciyar nan, Gimbiya Nana Asma’u ‘yar Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

Rahma, wadda ita ce Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Rediyo da Watsa Labarai a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, za ta yi fim ɗin a ƙarƙashin kamfanin Script Plus Limited.

Ana sa ran fim ɗin zai hasko rawar abar yabo da gudunmawar da Nana Asma’u ta bayar a Daular Usmaniyya wajen cigaban ilimi, ƙarfafa mata da kuma ilimin addinin Musulunci.

A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da ranar 21 ga Nuwamba, 2025, Sarkin Musulmi, ta hannun Sakataren Majalisar Masarautar Sakkwato, Alhaji Sa’idu Muhammadu Maccido, ya isar da izinin majalisar ga aikin fim ɗin ga Rahma Abdulmajid.

Takardar ta ce: “Mun yi farin cikin jin cewa kun ɗauki nauyin shirya fim kan Nana Asma’u ‘yar Usman Ɗanfodiyo, wadda ga mutane da dama ita ce ainihin misalin mace Musulma a Afirka… Majalisar Masarauta na isar da amincewar ta ga wannan aiki tare da ba ku damar fara shi kamar yadda kuka nemi izini.”

Majalisar ta nemi a dinga ba ta rahotanni lokaci zuwa lokaci da kuma damar shiga nazarin ƙarshe na fim ɗin kafin a ƙaddamar da shi.

Ita ma Ma’aikatar Masana’antu, Sana’a da Zuba Jari ta Tarayya, ta hannun Sashen Dokokin Kasuwanci, ta tabbatar da amincewar ta ta wata wasiƙa mai shaida, dangane da neman rajistar wannan aiki a matsayin alamar kasuwanci (trademark).

Babbar Furodusar  fim ɗin, Rahma Abdulmajid, ta ce hangen nesan aikin ya wuce Arewa, domin al’adun sa masu yalwa za su ƙara haɗin kai da wanzar da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.

Ta ce: “Wannan labari ne mai muhimmanci na jagoranci, ban-gaskiya da ilimi wanda ya shafi dukkan ‘yan Najeriya.

“Ta hanyar fito da tushen ilimi da halayyar kirki da manyan mutane irin su Nana Asma’u suka kafa, muna ƙoƙarin amfani da wannan kyakkyawan tarihi domin ƙara haɗin kai da wanzar da zaman lafiya tsakanin Hausa-Fulani da sauran ƙabilu a Arewa da kuma ƙasa baki ɗaya.

“Rayuwar Nana Asma’u na bayar da hujjar tarihi mai ƙarfi cewa ilimin mata ya taɓa daɗewa yana cikin al’ada da darajar addini a Arewa, ba wani abu ne da aka shigo da shi daga waje ba.”

Loading

Tags: Alhaji Sa'ad Abubakar IIIDaular UsmaniyyafimNana Asma'uRahma AbdulmajidSakkwatoSarkin Musulmi
Previous Post

Hajiya Zainab, mahaifiyar jarumin Kannywood Isah A. Isah, ta rasu

Next Post

Mawaƙi a Kannywood, Ahmad Yariman Tiga zai angwance a ranar Juma’a 

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Mawaƙi a Kannywood, Ahmad Yariman Tiga zai angwance a ranar Juma’a 

Mawaƙi a Kannywood, Ahmad Yariman Tiga zai angwance a ranar Juma'a 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!