SHUGABAN ƙungiyar ƙwararru ta masu shirya fim ta kara ƙasa (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), reshen Jihar Kano, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya bayyana ƙudirin sa na haɗa kan masu harkar fim da kuma kawo gyara don cigaban masana’antar tasu.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim a game da cigaban da ya samar tun daga lokacin da su ka kama shugabancin ƙungiyar tsawon sama da rabin shekara zuwa yanzu.
Shi dai Gidan Dabino, an rantsar da su ne a matsayin shugabannin ƙungiyar a wani taro da aka yi a ɗakin taro na Kannywood TV da ke Tudun Yola, Kano, a ranar Laraba, 27 ga Afrilu, 2022.
Gidan Dabino ya ce: “To, idan ka duba a baya ana ɗan samun kamar zaman doya da manja da wasu ɓangarori, ni kuma abin da na ɗauka idan duk ana masana’anta ɗaya, kowa ɗan’uwan juna ne. Ba za a ce babu wani abu na ƙyashi ko hassada ya shiga tsakani ba, amma dai abin da na ke gani shi ne a taru a yi aiki tare, don mu zama kamar uwa ɗaya ne. Saboda haka, ban zo da niyyar ko na nemi kuɗi ba, na zo ne saboda don an matsa mini na yi shugabancin saboda ana ganin kamar zan iya wani abu, to shi ya sa na zo. Don haka ni na ɗauka kowa uwa ɗaya mu ke, ko wanda ba ma shiri da shi zan iya kiran sa mu zauna mu tattauna a kan wannan masana’antar, ko waɗanda su ke ganin shugabancin ya yi musu ba daidai ba, to a gani na duk ɗaya mu ke.
“Don zan iya tunawa lokacin da aka ba ni shugabancin Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa reshen Jihar Kano, na ga akwai ƙungiyoyin da ba sa shiri da ƙungiyar ANA a lokacin, amma ni na kira su har ya zama mun yi aiki tare, kuma mun yi gamayyar ƙungiyar marubuta wanda mu ka yi faɗan Abubakar Rabo tare da su, wanda idan babu haɗin kai ba za mu yi nasara a faɗan ba.
“Don haka na ke ganin a tunanin da na yi wannan zai taimaki masana’antar Kannywood nan gaba ko da ba mu ne a kai ba, a samu wasu su ɗora daga inda mu ka tsaya.”
Gidan Dabino ya ƙara da cewa abin da ya ke so ya cimma shi ne ya na fatan ‘yan wannan masana’antar su samu ilimi wanda za su samu hanyar sanin wasu abubuwa. Ya ce, “Na biyu, duk da dai ba ma son mu faɗa, amma akwai abubuwan cigaba da mu ke son kawo wa masana’antar a kasuwancin su, ta hanyar samar musu da tallafi, duk da tsawon shugabancin ba shi da yawa, na shekaru biyu ne, kuma a yanzu mun ci kusan sama da rabin shekara. To amma ka san ita harkar ƙungiya sai a hankali, sai dai mu na da fata da kuma buruka da mu ke so mu samar don ganin cigaban masana’antar, don haka kamar yadda na faɗa lokacin da aka zaɓe mu, ba mu ce mun yi alƙawarin za mu yi wa kowa ba, don haka kada a saka mana ido ko a ce kaza. Sai dai in mun yi a gani.
“Don haka mu na fatan Allah ya cika mana burin mu wanda ko da bayan ba ma nan za a ce lallai su wane sun yi wani abu, kuma wannan shi ne fatan mu da mu ke so mu cika in-sha Allah, zuwa lokacin da za mu bayar da shugabancin zuwa ga wasu.”