• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Halacci ne ya sa na auri Hassana – Sahabi na cikin ‘Kwana Casa’in’

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
June 28, 2021
in Taurari
0
Halacci ne ya sa na auri Hassana – Sahabi na cikin ‘Kwana Casa’in’
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ALIYU Hussaini Musa Yarima ya na ɗaya daga cikin jarumai masu tasowa a cikin masana’antar Kannywood. Tashar talbijin ta Arewa24 ce ta fito da shi har duniya ta san shi a cikin diramar ta mai dogon zango ta ‘Kwana Casa’in’ inda ya ke fitowa a matsayin ɗan jarida mai suna Sahabi Madugu.

A hira ta musamman, jarumin ya faɗa wa mujallar Fim yadda aka yi ya zama ɗan fim har ya tsinci kan sa cikin wannan shirin da irin faɗi-tashin da ya yi kafin shigar sa Kannywood da kuma irin tagomashin da ya samu wanda idan ya tuna ba ya iya ɓoye farin cikin sa.

 Har wa yau, ‘Sahabi’ ya faɗi wasu daga cikin ƙalubalen da su ke ci masa tuwo a ƙwarya game da wannan harka, sannan ya yi tsokaci kan ce-ce-ku-cen da aka yi kwanan nan a soshiyal midiya dangane da auren da ya yi, ya ce matar sa, Hassan Gambo Tijjani, mace ɗaya ce tamkar da biliyan.

Aliyu dai haifaffen Kano ne kuma ya yi makarantar firamare da ta sakandire duk a Kano, sannan yanzu ya na karatun digiri a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, inda ya ke karanta harshen Ingilishi.

Ga yadda tattaunawar tasa da mujallar Fim ta kasance:

FIM: Mutane da dama sun san fuskar ka a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’. Shin da man da fim ɗin ka fara a wannan masana’antar ko ka yi wani a baya?


ALIYU: Gaskiya ‘Kwana Casa’in’ ba shi ne fim ɗi na na farko ba, amma shi ne fim ɗin da ya fito da ni. Kafin shi akwai fim ɗin da aka yi mani wanda Ali Rabi’u Ali (Daddy) ya yi min, kuma shi ne fim ɗi na na farko, mai suna ‘Farar Zuciya’. Bayan shi akwai fim mai suna ‘Sakayya’ wanda na fito a ciki. Bayan su kuma akwai finafinai da dama wanda na yi irin fitowa  ta musamman. Ana cikin haka kuma sai ‘Kwana Casa’in’ ya fito wanda na ke ɗaya daga cikin jaruman fim ɗin, shi ne kuma ya fito da ni daga halin da na shiga, alhamdu lillah.

FIM: Ka na karatu a jami’a, ga shi kuma ka na fim. Da man fannin jarida ka ke karantawa?


ALIYU: Maganar gaskiya, ban taɓa yin wani karatu da ya danganci fannin jarida ba. Hasali ma ba ya daga cikin tsarin rayuwa ta da na ke son idan na girma in zama, sai bayan da na fara ‘Kwana Casa’in’ sannan sha’awar sa ta kama ni fiye da kima.

Abin da na ke karantawa a makaranta shi ne asali da ɓangaren kimiyya na ke karantawa amma daga nan na koma ɓangaren koyarwa, wanda yanzu haka ina karanta yaren Turanci. Haka ne ya sa mutane su ke ganin cewar aikin jarida ya kama ni kamar ɗan jarida a gaske. Wannan kuma ya samo asali ne daga irin tarbiyyar da aka ba ni daga kamfanin da na fito na A.R.A. Movies; an nuna mani cewar jarumi ba ya cika jarumi sai in an ba shi kowane irin rol an ce ya koma shi, misali ko makaho, kurma, bebe da sauran duk wani abu da aka ba ka ka taka rawa a kai kawai ka zama. Irin tarbiyyar da mu ka samu kenan. Hakan ya ba ni gudunmawa sosai wajen ganin da aka ban sikirif a Arewa24 a matsayin ni ne ɗan jarida, na je na yi ta kwatantawa.

Abokai na sun ba ni gudunmawa sosai wajen ganin na taka rawa a wannan fanni saboda su da ma aikin su ne, irin su Muzammil Ibrahim Yakasai na gidan rediyon Freedom Kano, Aliyu Alhassan Sufyan na Aminci Radiyo, Saddam Abubakar Ungogo na Nasara Radio da sauran abokai na wanda su ka taimaka mani wajen ganin na samar da abin da ake so a cikin wannan matsayi da na fito ta cikin wannan shiri har ta kai ga wasu su na kallo na a matsayin ɗan jarida.

FIM: Mai karatu zai so jin ta yaya ka shigo cikin wannan masana’anta ta Kannywood.


ALIYU: Na shigo cikin Kannywood ne ta sanadiyyar wata ƙungiya mai suna ‘Bollywood fans of Nigeria Kano Chapter’. Ƙungiya ce wacce ta shafi harkar Indiya. A cikin ita wannan ƙungiyar ina ɗaya daga cikin zaƙaƙurai uku. Idan shekara ta zagayo ƙungiyar ta na yin taro, a yayin taron na shekara akwai wasu mutane da ake zaɓa da su ke nishaɗantar da manyan baƙi da irin bin waƙoƙin indiya da yin rawar ta Indiya, kuma ina ɗaya daga cikin mutum ukun da su ke wannan nishaɗantarwa.

To, Allah da ikon sa akwai wani lokaci da aka yi wani taro, an kuma gayyaci manyan baƙi da Indiyawa da ma wasu daga nan gida Nijeriya. Wannan taron shi ne ya zama sila wanda na fito na nishaɗantar da jama’a ta hanyar yin rawa wacce ban taɓa yin irin ta ba sai a wannan shekarar. Hakan kuma da na yi ya jawo hankalin jarumi Ali Rabi’u Ali (Daddy), ya tashi ya yi mani alƙawarin zai yi mani fim, saboda tun kafin wannan ranar taron na sha bibiyar sa a kan cewa ina so na yi fim amma kuma an ce sai na sayi fom, a lokacin ina ɗalibi kuma ga shi an ce fom ɗin (naira) dubu goma ne wanda kuma a lokacin ya yi mani tsada gaskiya, duba da cewa a lokacin ina makaranta, don haka sai na haƙura. Sai ga shi kwatsam sakamakon wannan ƙwazo da na yi sai ya burge shi ya kuma yi alƙawarin fim da ni da wata jaruma mai suna Hafsa Zee Aflam.

Aliyu Hussaini Musa Yarima

FIM: An cika wannan alƙawari da Ali Rabi’u Ali ya ɗaukar maka?


ALIYU: E, ya cika wannan alƙawarin da ya ɗauka wanda kafin shekara ta zagayo a kuma yin taron ya cika, amma kuma ta hanyar shigo da ni kamfanin sa a matsayin memba na Kannywood, domin kuwa sai da na yi rajista aka min I.D. card sannan abubuwa su ka kankama, kuma ta wannan silar na fara yin fim.

FIM: Mai karatu zai so ya ji wai da man Sahabi ya na rawa?


ALIYU: Ai da man can da ita aka san ni. Sau da dama  mutane na tambaya ta shin Sahabi ya na rawa? To idan mutane ba su sani ba, shi Sahabi kusan abin da ya maida hankali kenan a baya kafin na shigo fim. A waccan ƙungiyar tamu ta Indiya na fi maida hankali a kan rawa duk da abin an raba shi ne a kan, wasu za su maida hankali a kai kamar koyon yaren, wasu kuma a kan iya goyon bayan jarumi da jin waƙoƙin Indiya su ka tsaya, to mu kuma mun kasance ne a kan gaba ɗayan, musamman fannin nishaɗantarwa wanda zai jawo hankalin jama’a, wato fannin rawa. 

FIM: Akwai wani jarumi da ya ke burge ka a wannan masana’anta ta Kannywood?


ALIYU: Akwai jarumai ma da yawa. Akwai irin su Sadiq Sani Sadiq, Adam A. Zango da kuma Sarki Ali Nuhu. A ɓangaren mata kuwa akwai Jamila Nagudu wadda ta na burge ni sosai, sannan kuma Zainab Indomie. Idan na koma baya sosai a cikin tsofaffun jarumai akwai su Abida Muhammad da Fati Muhammad.

FIM: Ka taɓa samun damar yin fim da waɗannan jaruman da ka lissafo?


ALIYU: To, ina ganin Ali Nuhu ne kawai mu ka taɓa fim da shi har sau biyu, amma duk sauran ba mu taɓa yin fim da su ba, sai dai kawai mu na haɗuwa kuma mu na gaisawar mutunci da su sosai.

FIM: Ka na da burin nan gaba ka yi fim da su?


ALIYU: Ni dai sana’a ta kawai na ke, ba ni da wani buri na wai na haɗu da wane ko ina so na yi fim da wance; idan sana’a ta ta haɗa ni da shi, to, domin ni ba ni da matsala da kowa. Wannan shi ne a taƙaice.

FIM: Ya ma’amalar ka ta kasance da jama’ar gari lokacin da duniya ta san ka a matsayin Sahabi ?


ALIYU: Ma’amala ta ta canza sosai, amma bari na fara da ɓangaren abokai na duk da cewa ni ba ni da wasu abokanai wanda zan ce mun taso da su tun daga yarinta saboda yanayin gidan mu ba a bari ka ka yi abokanai in ka na yaro, sai dai a ce a bari in ka malllaki hankalin kan ka ka samu. 

Akwai abokan da na yi wanda tun kan na fara harkar fim mun shaƙu da su sosai har ake kallon mun zama kamar ‘yan’uwa. To a cikin su sai wasu su ke mani kallon kamar na ɗaukaka na guje su saboda da zan ɗau ƙafa na je inda su ke mu yini tare, idan ba ni da makaranta kenan, amma yanzu yanayin aiki bayan da na fara harkokin fim sai labarin ya canza, ba ni da lokacin da na ke samun damar zuwa mu gaisa kamar da. Amma duk da haka wasu su na yi mani uzuri, wasu kuma ba sa yi mani.

A unguwar mu kuma da man ban cika fitowa ba amma in dai na fito ba wai nasa takunkumin fuska na rufe fuska ta ba, komai zan saka sai ka ji mutane su na yi mani ɗan kira. Wasu unguwannin ma idan na shiga ba da suna na su ke kira na ba, sai dai a kira sunan wani ɗan fim amma kuma wai da ni su ke.

FIM: To ya ka ke da masoyan ka idan ka shiga taro?


ALIYU: Alhamdu lillah, ni ba abin da zan ce da Allah sai godiya domin matakin da na kai ko na ke kan kai wa shi ya kai ni, ba ni na kai kai na ba, ban iya ba kuma ba zan iya ba. Har gobe haka na ke ji a rai na. Mutane duk inda na je su na nuna mani ƙauna da soyayya. Wannan abu kuma ya na min daɗi ƙwarai da gaske kuma ina gode musu. Allah ya saka da alkairi. Sannan ni a ko da yaushe ina faɗa: ko maƙiyi na ma ina son sa!

FIM: Tun bayan fara fitowar ka a fim akwai wani abu da ka taɓa yin karo da shi wanda ba za ka iya mantawa da shi ba?


ALIYU: Tafiyar dai yanzu aka fara, sai dai godiya kawai. An samu nasarori; tun kafin ma na fara fim na ke samu, tun a waccan ƙungiyar da na gaya maka ta ‘Bollywood Fans of Nigeria’, na taɓa cin gwarzon wanda ya fi kowa iya rawa a Kano, wato ‘Best Kano State Dancer’ na harkar Indiya. Nasara ce ni a guri na. Sannan ita kan ta a cikin masana’antar Kannywood a shekarar da ta gabata na samu lambar girmamawa ta gwarzon jarumin da ya fi kowa taka rawa a shirin fim ɗin ‘Kwana Casa’in’ na tashar Arewa24. Ita ma wannan nasara ce kuma su ne dai abubuwan da ba na iya mantawa da su, sai dai ko nan gaba in mu na da rai da lafiya.

FIM: A ‘yan satittikan da su ka shuɗe an samu ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta tun bayan da ka yi aure, wanda wasu daga cikin al’umma ke ganin a matsayin ka na jarumi bai kamata ka auri wacce ka aura ba. Shin ko me za ka ce kan wannan batu?

Aliyu Hussaini Musa Yarima da Hussaina Gambo Tijjani a lokacin bikin auren su


ALIYU: Ni ba na ganin wannan a matsayin matsala, kawai dai mutane ne su ke ta ce-ce-ku-ce ko in ce saɓani, ni kuma a gu na yadda na ɗauki abin na danganta shi da rashin ilimi. Idan mutum ya na da ilimi, mutum ba zai auri mace wadda ya ke ganin ita ce mahaɗar rayuwar sa kuma ta dace da shi ba kai kuma ka zo ka ce ba ita ce ta dace da shi ba. Kawai ina ganin wannan a matsayin jahilci ko rashin hankali a cikin wannan maganar.

Sannan kuma duk maganar da mutane su ke yi ko a kai na saboda ba na damun kai na. Allah na ke nema a gun sa ba agun mutum ba, kuma ba kai za ka gaya min cewa wance ita ce ta fi dacewa da ni ba. Abin da na ke faɗa ko da yaushe shi ne wadda na aura ina son ta ina ƙaunar ta, kuma in Allah ya yarda har abada mu na tare da ita; mutuwa ce za ta raba mu da yardar Ubangiji.

Wacce na aura ta nuna min halacci, ta so ni tun kafin na zama ‘Sahabi’, yanzu kuma na zama ‘Sahabi’ bai kamata na yi mata butulci ba ko don ina ganin wasu ‘yan mata masu kyau ko wani abu makamancin haka. Don haka ban juya mata baya ba, na ke son aba ta, ga shi har ta kai mu ga aure. Kuma har yanzu ina son ta sosai da sosai. Don haka babu wani dalili da mutum zai ce ba ita ya dace na aura ba. 

Manzon Allah (S.A.W) ya bayyana mana irin kalar macen da ya kamata mu aura, to ni kuma dukkan waɗannan alamomi da Ma’aikin Allah ya zayyana mata ta ta na da su.

FIM: Wace tambaya ce Sahabi ya gaji da amsawa daga masoyan sa?


ALIYU: Bayan shigowa ta Kannywood tambayar da na gaji da amsawa kuma ba na so ma a yi mani tambayar har ma a shafukan sada zumunta na ba na son na ga wani ya yi min ita ita ce: yaushe za ka auri Salma? Ita ce tambayar da na gaji da amsa ta daga masoya na.

A har kullum ina faɗa, Salma tsakani na da ita mutunci ne da kuma dangantaka mai kyau saboda mu na mutunta juna.

A yanzu kamar yadda ka yi mani wannan tambayar a kan biki na, akwai waɗanda su ke zuwa su ce min ban kyauta ba, na yaudari Salma, ya ba zan auri Salma ba? To kuma matar mutum kabarin sa, kuma iya fahimtar su kenan.

Wannan tambayar ta yaushe zan auri Salma ita ce tambayar da na fi amsawa, har ma na gaji da ita.

FIM: Menene burin ka a cikin wannan masana’ana ta ta Kannywood?

ALIYU: Ba ni da wani buri a cikin wannan masana’antar face Allah ya ci gaba da rufa min asiri. Sana’a na shigo yi ni, ba neman ɗaukaka ba; idan a ciki Allah ya ɗaukaka ni ya kai ni inda ba na zato, da man shi Allah ba a iya masa kuma ba a tambaya don zai yi wa bawan sa. Don haka ni sana’a na zo yi, Allah Ubangiji ya ci gaba da rufa min asiri a cikin sana’a ta. Idan Allah ya ɗaukaka ni ya kai wani matsayi falillahil hamdu, idan kuma ya bar ni a haka a yanzu da mu ke magana da a kai, alhamdu lillah, ina ƙara gode masa.

FIM: Da me za ka ƙarƙare a ƙarshe?


ALIYU: Masoya na ina son ku sosai, ina ƙaunar ku, maza da mata. Wallahi yadda na ke faɗar wannan abu har cikin zuciya ta na ke faɗar sa, ba wai a iya baki na ba, saboda idan da da kai na ke yawo za ka ga yadda ake nuna min madarar soyayya, kuma ba ga yara ba, ba ga manya ba, ba kuma ga tsofaffi ba, kowa da kowa ya na nuna min so da ƙauna. Wannan abu ya na yi mani daɗi ƙwarai da gaske. Ina son ku masoya na, ina ƙaunar ku ko a ina ku ke a faɗin duniya.

Saƙo na gare ku masoya na shi ne ku bi iyayen ku. Duk lokacin da su ka nuna wani abu su ka ce ba sa so, to mutum ya haƙura ko da kuwa mutum ya na tsananin ƙaunar abin. Idan kuma iyaye sun zaɓa wa mutum wani abu da iyaye su ke so ka yi, to ka yi haƙuri ka yi ko da kuwa aure su ka samar ma.

Sahabi tare da jaruma Salma
Aliyu Hussaini Musa Yarima

Loading

Tags: Ali Rabi'u Ali DaddyAliyu Hussaini Musa YarimaArewa24 TVHassana Gambo Tijjanihausa actorsHausa drama seriesKannywoodKwana Casa'inSahabi Madugu
Previous Post

Lawan Ahmad ya sa gasar karatun Alƙur’ani

Next Post

Zama lafiya da mahaifiya ta ne jigon nasarar rayuwa ta – Daddy Hikima

Related Posts

Amal Umar:  Abin da ya sa na kai inda nake yanzu
Taurari

Amal Umar: Abin da ya sa na kai inda nake yanzu

June 15, 2026
Yadda mutane suke kallon harkar fim daga waje ba haka take ba – Hafsat Ja’afar
Taurari

Yadda mutane suke kallon harkar fim daga waje ba haka take ba – Hafsat Ja’afar

June 5, 2026
Shiga ta fim ta sa wanda zan aura ya ce na zama karuwa ba zai aure ni ba – Bilkisu Umar Aliyu
Taurari

Shiga ta fim ta sa wanda zan aura ya ce na zama karuwa ba zai aure ni ba – Bilkisu Umar Aliyu

June 2, 2026
Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Next Post

Zama lafiya da mahaifiya ta ne jigon nasarar rayuwa ta - Daddy Hikima

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!