‘Yan kallo sun yayyabe Aisha Tsamiya
CINCIRIDON mutane ne su ka yi tururuwa a gidan sinima na Film House da ke cikin rukunin shagunan Shoprite da ke Ado Bayero Mall, a Kano, wurin shiga kallon fim din ‘Kalan Dangi’ wanda fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (‘Tsamiya’) ta dauki nauyin shiryawa. Fauziyya D. Sulaiman ce ta rubuta labarin, yayin da Abubakar Bashir Maishadda ya shirya shi kuma Ali Gumzak ya bada umarni. Wannan dai shi ne fim na biyu da A’isha Tsamiya ta shirya, wato bayan fim din ta na ‘Burin Fatima’, wanda ya fito kasuwa kwanan baya.
Kannywood ta kasance masana’anta wadda ta fi kowace a arewacin Nijeriya samar da ayyukan yi ga matasa cikin kankanen lokaci, amma kasuwanci a cikin ta ya gurgunce a tsawon shekaru sakamakon dogaro da hanya daya ta samar da kudaden shiga (wato kasuwar sayar da fayafayen sidi da dibidi). A lokuta da dama mutane sun yi yunkurin kawo canji a tsarin kasuwancin, amma abin ya ci tura.
Da alama cewa a wannan karon haka za ta cimma ruwa. Dalili kuwa shi ne yadda aka maida haska finafinai a gidajen sinima kafin a sake su a faifan dibidi.
A ranar Juma’a, 1 ga Satumba, 2017, wadda ta zo daidai da ranar Babbar Sallah, aka haska ‘Kalan Dangi’ a sinima. An fara haska fim din da misalin karfe 12:45 na rana, amma a lokacin ba a samu yawaitar mutane ba saboda gabatowar lokacin sallar Juma’a. Sai bayan an taso daga sallar ne, wajen karfe 3, sannan mutane maza da ’yan mata su ka yi tururuwar shiga kallon.
Kafin a fara haskawar, A’isha Tsamiya ta ba masoyan ta dama su dauki hotuna da ita, wanda hakan wani salo ne da aka bullo da shi don a kara jawo mutane zuwa kallon fim. Lokacin nuna finafinan su a sinima bias wannan tsari, Ali Nuhu da Rahama Sadau ma sun yi hakan.
Da yawa daga cikin jarumai da daraktoci sun halarci kallon ‘Kalan Dangi’. Daga cikin su akwai jaruman shirin, wato Ali Nuhu da Fati Washa, da daraktan shirin, Ali Gumzak, sai kuma su Kamal S. Alkali, Aminu Shariff Momoh, Maryam Isah Abubakar (Ceeter), Hafizu Bello, Fauziyya D. Sulaiman, Baballe Hayatu, Mansurah Isah, Hassan Giggs, da sauran su.
An kammala haska fim din karo na biyu da misalin karfe 5:40 na yamma. Fim din ya samu karbuwa saboda irin yadda makallatan sa su ka yi ta Allah-sambarka da tare da ihu yayin da su ke kallon.
Lallai fim din ya samu mahalarta sosai. An yi ittafakin cewa idan aka cire fim din ‘Gwaska’ da aka haska a bara, babu fim din da ya tara ’yan kallo kamar ‘Kalan Dangi’.