HAMISU Lamiɗo Iyan-Tama shahararren furodusa ne kuma jarumi a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood. Jagora ne, domin ya taɓa riƙe muƙamin zaɓaɓɓen Shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Arewacin Nijeriya (Arewa Film Makers Association of Nigeria, AFMAN), wadda ta kasance uwar dukkan ƙungiyoyin masu shirya fim tsawon lokaci kafin a kafa ƙungiyar MOPPAN.
A matsayin sa na mai shiryawa, ya fitar da finafinai masu yawan gaske kuma masu ma’ana. Yawanci, shi ne jarumin finafinan, ko da yake akwai ɗaiɗaiku waɗanda ba shi ba ne.
Da alama, juyin zamani ya shafi rawar da Iyan-Tama ke takawa a Kannywood, aƙalla a wajen masu kallo. An rage ganin finafinan sa, kuma shi kan sa ya rage fitowa a fim ko da irin masu dogon zango ɗin nan ne waɗanda ake yayin su a yanzu.
Haka kuma, me ya sa Iyan-Tama bai shiga rige-rigen da ake yi na ɗora fim a YouTube ba? Menene ra’ayin sa game da Northflix da Netflix? Ya ya ke kallon irin shugabancin da MOPPAN ke yi wa ‘yan fim? Me zai ce game da salon tafiyar Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano? Sannan me ake ciki ne game da batun nan na farfaɗo da gidajen sinima irin na da a Kano domin a faɗaɗa kasuwancin finafinan Hausa wanda ya faɗi ƙasa warwas a yau?
Alhaji Hamisu ya amsa waɗannan tambayoyin, da ma wasu, a hirar musamman da ya yi da mujallar Fim kwanan baya.
FIM: An samu kamar shekara biyu zuwa uku ba a ji ɗuriyar ka ba. Kafin wannan lokaci, ka nuna cewa ka dawo harkar fim gadan-gadan, har ka shirya finafinai kusan biyar. To sai kuma aka ji ka shiru. Me ya faru ka sake ja da baya?
IYAN-TAMA: Ban taɓa ja da baya a harkar shirya finafinai ba. Da ma tsari na ne in shirya kuma in koma gefe in nutsu in sauya tunani in ƙara zuwa da wani abu sabo.
Gaskiya ne na shirya finafinai har guda biyar cikakku, waɗanda na gabatar da su ga hukumomin Kano da na ƙasa. Waɗannan finafinan kuwa su ne: ‘Uwar Bari’, ‘Wayar Hannu’, ‘Wuta a Maƙera’, ‘Ɗan Baiwa’ da kuma ‘Haƙƙi’ wanda na shirya shi a kan bin diddigin neman haƙƙi da ‘yanci.
Dukkan su ni na shirya su a ƙarƙashin kamfanin ‘Iyan-Tama Multimedia’. Na shirya su a shekarar 2018 da tunanin cewa zan kai su kasuwannin sinima da kuma gidajen talbijin da ‘online platforms’, amma abin bai yiwu ba.
Hakan ta faru ne sakamakon tsarin da na ɗauka cewa dukkan finafinan zan sake su a kasuwa a shekara ta 2020 amma wannan annoba ta ‘Covid-19’ ta zo ta mamaye duniya.
Na samu nasarar shiga gasar finafinai ta ‘AMMA Awards’ a shekara ta 2018 wadda aka yi a Katsina a inda fim ɗin ‘Uwar Bari’ ya samu ‘nominations’ tara, kuma fim ɗin ‘Ɗan Baiwa’ ya samu ‘nominations’ biyar, ya ciwo kyauta mafi tsoka, wato ‘Best Picture’, ya ƙara ciwo ‘Best Supporting Actor’ da kuma ‘Best Costumes’.
A 2019, mun shiga gasar AfrIcan Magic Viewers Choice Awards’ a inda ‘Uwar Bari’ ya samu ‘nomination’. A Legas aka yi.
Haka zalika, ‘Uwar Bari’ ɗin dai ya samu nasarar lashe ‘Best Film’ a gasar da ake gudanarwa duk shekara a birnin London.
A dunƙule, finafinai biyu daga cikin guda biyar da na yi sun samu ‘nominations’ 14 da kuma ‘awards’ huɗu mafi daraja. Ɗaya kuma ya kawo kuɗi, wato ‘Haƙƙi’.
Babu inda aka nuna waɗannan finafinan sai a (tashar talbijin ta) ‘African Magic Hausa’. Sun nuna guda huɗu har tsawon shekaru biyu, sai kuma fim ɗin ‘Haƙƙi’ wanda shi kaɗai aka nuna a Film House, Kano, na tsawon sati biyu, amma an ƙaddamar da shi tare da Ƙungiyar Ƙwadago ta Jihar Kano a ƙarƙashin jagoranci da sahalewa ta Mai Girma Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda aka yi a farfajiyar Gidan Gwamnatin a Kano a bikin ‘May Day’ na shekarar 2019.
FIM: Lokacin da ka shirya waɗancan finafinan, ka yi ƙoƙarin dawo da harkar shiga sinima, har ka jagoranci yunƙurin dawo da haska finafinan Hausa a sinimu irin su Marhaba, amma da alama wannan ƙoƙarin naka bai cimma nasara ba. Waɗanne matsaloli ku ka samu?
IYAN-TAMA: Haƙiƙa ni ne na shugabanci kwamiti wanda aka kafa a ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai ta Kano don kawo gyara a kasuwancin finafinan Kannywood da kuma samo sababbin hanyoyin kasuwancin zamani da daƙile satar fasaha da farfaɗo da sinimu na Jihar Kano.
Wannan kwamiti ya yi kuma ya kammala aikin sa bisa sharuɗɗan da aka ba mu. Mun gyara kasuwar ta ‘downloading’ a inda mu ka ƙulla yarjejeniyar za su dinga sayen fim daga hannun masu shi a ƙungiyance, kuma dukkan su za su dinga saya a dunƙule, su biya masu fim kuɗin su.
Sannan kuma mun shirya taro gagarumi wanda mu ka gayyaci kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano da Daraktan SSS da shugaban gidajen yari da kwamishinan shari’a na jiha da shugaban lauyoyi na jiha da duk masu ruwa da tsaki da ‘yan ‘downloading’ domin a gabatar da jawabai a kan illar satar fasaha.
An yi wannan taro a ‘Murtala Muhammad Library’. Daga nan ne mu ka fara aiki ba dare ba rana. Mun samu nasarar aiwatar da ƙudirorin taron.
Kwamitin ya farfaɗo da sinimu; ba Marhaba kaɗai ba har da duk manyan sinimu da ke Kano kamar Eldorado, Queens Cinema da Lale da Farida da Orion Cinema da wata sinima cikin Birged da Dakatsalle da kuma Marhaba da wata sinima a Panshekara.
Mun shiga yarjejiniyar karɓar duk wani fim da ya samu sahalewar kwamitin a manyan sinimun Kano, sannan mun yi rubutu, wato MOU, domin tabbatar da ci gaba da dawo da nuna finafinai na Hausa a waɗannan sinimu. Ni na nuna fim ɗin ‘Ɗan Baiwa’, kuma na san cewa akwai wasu furodusoshi kamar Maishadda da Falalu Ɗorayi, idan har ban manta ba, da su ka kai su ka nuna a sauran sinimun. Kuma har yanzu wannan yarjejeniya na aiki. Amma ban san dalilin da ya sa ba a kaiwa domin a nuna ba.
FIM: Har yanzu akwai shirin nuna finafinan a sinima ko kun haƙura?
IYAN-TAMA: Ai har yanzu ƙofa a buɗe ta ke, duk wanda ya kai fim ɗin sa za su karɓa su nuna bisa yarjejeniyar da mu ka yi ta ‘percentage’.
FIM: Kafin zuwan annobar korona (COVID-19), yayin da aka yi shi ne haska finafinai a gidan sinima na Film House da ke Ado Bayero Mall. Amma kai ba ka kai naka finafinan can ba. Ba ka yarda da tsarin ba ne?
IYAN-TAMA: Na yarda da tsarin mana domin na kai fim ɗin ‘Haƙƙi’ an nuna a Film House kuma na kai ‘Ɗan Baiwa’ Lale da Farida an nuna. Ina tunanin da a ce mun dage mun ci gaba da kaiwa, da abIn ya ɗore, amma saboda gajen haƙuri na ƙara farfaɗo da sinimu sannu a hankali ina zaton shi ya yi tasiri a zukatan mutane.
FIM: Da annobar korona ta hana shiga sinima kuma, sai masu shirya finafinan Kannywood su ka maida akalar su zuwa nuna finafinan ta hanyar manhajar Northflix. Shin ko hakan wata maslaha ce ga matsalar kasuwancin finafinan Kannywood?
IYAN-TAMA: Ba aibu ba ne ‘yan fim su kai fim ɗin su duk wata manhaja da ke ‘online platforms’ in har su na ganin akwai mafita da samun riba kamar yadda ya kamata.Amma ni ban kai ba saboda ganin mun ƙirƙiri ‘Kannywood Distribution Network Online’ ne, shi ma kuma a ƙarƙashin wancan kwamiti da na jagoranta ya ke amma rashin masu zuba jari da kuma su waɗanda su ka kafa kwamitin ba su damu ba, sai abin ya samu tasgaro. Amma a yanzu mu na nan mun yi nisa da za mu fitar da sabuwar manhaja ta ‘online’ ga duk mai buƙata, fim ne ko ‘TV series’ ko waƙoƙi ko ‘documentaries’ da sauran su, duk su kawo a yi yarjejeniya a watsa wa duniya a samu kuɗi. Za mu gabatar da shi nan ba da jimawa ba.
FIM: Ko za ka iya bada fim ɗin ka a nuna shi ta Northflix kuwa?
IYAN-TAMA: Me zai hana idan har sun yarda da tsarin? Na yarda da su. Ai kasuwa ce, ni kuma ɗan kasuwa ne; ina da haja, ina neman inda zan kai in sayar. Idan kasuwar za ta yi min adalci sai in ruga a guje in je can, idan kuma ina tunanin anya? sai in dakata domin gudun kar a yi uwar watsi – ba riba, ba uwar kuɗi.
FIM: A yanzu, ‘yan Kudu, wato Nollywood, sun sake yi wa ‘yan Kannywood nisa wajen nuna finafinan su a manhajar Netflix ta ƙasar Amurka. Me ya sa babu fim ɗin Kannywood ko guda ɗaya a Netflix?
IYAN-TAMA: To, ina ganin wannan tambaya na da alaƙa da irin sharuɗɗan da Netflix ɗin su ka gindaya. Idan duk ‘yan Nollywood sun cika ƙa’idojin, za su samu a karɓi finafinan su a saka; idan Kannywood ba mu cika sharuɗɗan su ba, ka ga babu yadda za a yi a ga finafinan mu a wajen.
Saboda haka ina ganin ya na da kyau mu tabbata mun yi duba ga sharuɗɗan su, mu bi yadda su ke so, sannan sai mu jarraba ba su.Za su karɓa domin su ma kasuwanci su ke yi kuma su na da buƙatar ‘content’ irin namu, amma fa sai mun yi yadda su ke so.
FIM: ‘Yan Kannywood sun yi wa YouTube rubdugu; duk wanda ya shirya fim ko waƙa sai ya ruga can ya sake shi. Kai me ya sa ba ka rungumi YouTube ba? Ko ka ga babu riba ne?
IYAN-TAMA: Tun cikin 2011 na buɗe ‘YouTube channel’. A yi ‘searching’ “Hamisu Iyantama”, za a gani. Yau shekaru goma kenan, amma ban maida hankali na ba sosai daga lokacin.
Kuma waɗanda su ke sakawa ban ga aibun su ba domin ita ma kasuwa ce kuma da dama sun ce su na samun ‘yan canji daga wajen, ka ga kuwa tunda babu wata hanya da su ka yarda da ita fiye da wannan ai kuwa sai a yi ta shagali.
Sannan kuma idan aka yi la’akari da yadda duniya gaba ɗaya su ka raja’a da amfani da YouTube ɗin, to mu a su wa da za mu ce a’a?
Hollywood, Bollywood, kai da ma duk wani ‘wood-wood’ da waɗanda ba ma ‘wood’ ɗin ba ne su na kan YouTube. Saboda haka ya na da kyau sosai Kannywood a ce an gan ta a wajen, yin haka ƙara faɗaɗa sunan masana’antar ne kuma hanyar samun kuɗin shiga ne.

FIM: Akwai wata furodusa wadda ta ce tunda kasuwancin finafinan Kannywood na Hausa ya durƙushe, ita za ta koma shirya finafinan Kannywood ɗin amma da Turanci tunda su ne masu ciniki a YouTube da African Magic Hausa ke bukata. Shin ka goyi bayan yin hakan?
IYAN-TAMA: Shan koko ɗaukar rai! Kowane ɗan’adam ya na saka riga ko zani daidai da yadda ya ga za su yi masa kyau. Ita wannan furodusar da ma kuɗi kawai ta zo nema kuma mai yiwuwa da ma ba Bahaushiya ba ce ko kuma ba ta damu da tallar adabin Hausa ba. Ina zaton ba ta damu da sana’ar ba ne ko kuma da ma al’adun Hausawan ne ba ta yarda da su ba. A duba irin finafinan da ta yi a baya, za a samu amsa daga gare su.
Amma shi ilmi na fim ai ba ruwan sa da Turanci. Idan har mutum ya isa gwani, ya yi fim da kowanne irin harshe zai karɓu idan har shi gwanin ne, kuma za a gane saƙon da ya ke so ya tura ko babu ‘dialogue’.Fim ‘moving image’ (hoto mai motsi) ne; so ake yi a yi fim babu magana aƙalla kuma a gane ko da kuwa ya kai awa biyu.
Maganar yin fim da Turanci, ni ba Bature ba ne, ban kuma iya Turanci ba, bakuma wani Turanci da zan yi in burge Bature.
Mu Hausawa ne, harshen mu mu ke tallatawa, shi mu ka iya, mu ka ƙware; da shi za mu burge Bature da duk (mai jin) wani harshe a faɗin duniya.
Ku bincika, anya kuwa da ma ita wannan furodusa ɗin Bahausa ce ko kuma dai…
FIM: Me za ka ce game da wakilcin da shugabannin MOPPAN na yanzu su ke yi wa ‘yan Kannywood tun da aka zaɓe su? Abin nasu na tafiya daidai da muradin ‘yan fim a yanzu kuwa?
IYAN-TAMA: Na kan yi wa kowane irin shugaba uzuri har ya kammala shekarun sa na shugabanci kafin in ce wani abu. Haka ɗabi’a ta ta ke. Saboda haka a yanzu mun zura ido mu na kallon kowa da ido biyu.
FIM: A taƙaice, ba mu alƙalancin ka game da rawar da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ke takawa a Kannywood a ‘yan shekarun nan kamar biyar da su ka gabata. Ko ka gamsu da matakan da hukumar ta ɗauka wajen haɓaka harkar finafinan Hausa kuwa?
IYAN-TAMA (dariya): Kar ka sa a zo a kama ni a kulle a kurkuku fa! To, amma dai bisa gaskiyar magana ka san dole ne a samu kurakurai, kuma dole a samu daidai; akwai a inda zan ce shugaban ya yi iya ƙoƙarin sa, akwai kuma inda aka tafka kurakurai, kuma ko ni ne a kujerar sai an samu hakan.
Amma abin da aka fi so ai shi ne a ce alheri ya fi saɓanin haka yawa. Saboda haka zan ce ba dan laifi duba da kasancewar akwai ƙarancin kusantar masu sana’ar da kuma yadda sana’ar ta koma ‘online’ zan ce gaskiya sai a hankali. Amma ta fannin shugabanci akwai kurakurai.
Alƙalanci na shi ne shi mulki idan ba shigar sa ka yi ba, ba ka sanin yadda ya ke. Mulki kamar ƙwallon ƙafa ne, ɗan kallo ya fi ganin cin ta fiye da na cikin fili mai taka leda.
FIM: Wane albishir za ka yi wa masoyan finafinan ka game da inda ka dosa a fagen shirin fim a nan gaba kaɗan?
IYAN-TAMA: To, a wannan karon dai albishir guda ɗaya ne: idan mun yi nasarar kammala ‘online app’ ɗin mu, to za a sha kallon fim na da da na yanzu.
FIM: Alhaji Hamisu, mun gode.
IYAN-TAMA: Ni ma na gode.

Good luck my Chairman