A yammacin jiya Alhamis, Allah ya ɗauki ran jaruma a Kannywood, Jidda Muhammad Kontagora, wadda aka fi sani da suna Fulani a cikin fim mai dogon zango, wato ‘Labari Na’.
Jidda ta rasu sakamakon jinya da ta sha fama da shi na cutar gyambon ciki (ulcer), wanda aƙalla ta shafe kimanin wata biyu tana jinya.
Marigayiyar ta rasu a wani asibiti da ke garin Kontagora, a Jihar Neja.
Za a yi jana’izar ta a yau Juma’a da misalin ƙarfe 10:00 na safe, a gidan Hajiya Mai Saurin Gama Tuwo, a cikin garin Kontagora.
Kafin rasuwar ta, Jidda tana ɗaya daga cikin jaruman shirin ‘Labari Na’ inda ake kiran ta da Fulani, matar Sarkin Gabas.
Kamfanin shirya finafinai na Saira Movies da ma Kannywood baki ɗaya sun kaɗu jin rasuwar Jidda domin marigayiyar tana ɗaya daga cikin manyan jaruman da ke taka babban rol a shirin ‘Labari Na’.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa kafin rasuwar ta, ta nemi yafiya da kuma addu’ar neman samun lafiya a wajen al’umma.
Allah ya jiƙan ta, ya albarkaci dukkan abin da ta bari.
![]()







