• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kamal mai zane ya shawarci ‘yan ƙungiyar mawaƙa mata da su tuntuɓi Iyan-Tama

by DAGA ABBA MUHAMMAD
April 8, 2023
in Labarai
0
Kamal Y. Iyan-Tama

Kamal Y. Iyan-Tama

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHAHARARREN mai zane, Kamal Y. Iyan-Tama, ya ba ‘ya’yan ƙungiyar Muryar Mawaƙa Mata A Yau shawara da su samu tsohon shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN), Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, don neman shawawari da ci-gaban ƙungiyar su.

Kamal, wanda ke yawan zana hotunan ‘yan fim, ya ba da shawarar ne a Facebook bayan mujallar Fim ta fitar da hirar da ta yi da mawaƙiya Fati Kawo.

Sarkin Yaƙin Iyan-Tama ya ce, “Haƙiƙa daga farko har zuwa ƙarshe na karanta dukkan abin da Fati Kawo ta bayyana abin bai yi min daɗi ba gaskiya. A ce a matsayin ku na mata, ‘ciwon ‘ya mace ai na ‘ya mace ne’.”

Ya ci gaba da cewa, “Ya kamata a ce haɗin kan da za a gani a wurin ku, sai dai maza su kwaikwaya. Wato harka in dai ta kuɗi ce gaskiya ta na da wuyar sha’ani, ba wai a wurin ku mata ba, a’a, har maza ma, balle kuma batu na ƙungiya. 

“Tun da na fara ganin wannan yunƙuri ta wurin yaya ta Maryam A. Baba na yi farin ciki da jin wannan abin alheri. Duk da ina namiji, a matsayi na na mai son ganin rauni ko ciwon da ke damun ku ya warke, ina ganin shawara ta cikin ladabi, ku tashi ku taka zuwa wurin matashin dattijo a masana’antar Kannywood, wato Alh. Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ku gabatar da abin da za ku yi, ku nemi shawarwarin sa, a ƙarshe ku ce ku na so ya zama uban ƙungiyar ku, sannan ya zama tsani ko jagoran ku.

“Haka dukkan wani lamari da ya shafi tsarin Tafiyar da kasafin kuɗi, wallahi ba ni shakkar sa, domin wannan bawan Allah mutum ne.

“In-sha Allah kwalliyar ku za ta biya kuɗaɗen sabululluka, saboda mutum ne da ya goge a fannoni da dama na harkar kasuwanci da kasafin kuɗi tare da kowace irin tafiya ta shugabancin ƙungiya da ƙungiyoyi.”

Loading

Tags: AFMANFati KawoHamisu Lamiɗo Iyan-TamaKamal Y. Iyan-TamaKannywoodMaryam A. Babamawaƙa mataMurja Baba
Previous Post

Abin da ya sa na ke ciyar da yara da azumi – Daso

Next Post

Ya kamata ‘yan fim mu ɗauki darasin watan Ramadan, inji A’isha Tafida Gombe

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
A'isha Tafida Gombe

Ya kamata 'yan fim mu ɗauki darasin watan Ramadan, inji A'isha Tafida Gombe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!