• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kannywood: Dalilin yi wa MOPPAN ta Kano kwaskwarima – Jahun

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
July 5, 2021
in Labarai
0
Kannywood: Dalilin yi wa MOPPAN ta Kano kwaskwarima – Jahun
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KITSO da kwarkwata ya sanya haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya (MOPPAN) ta ƙasa reshen Jihar Kano yin kwaskwarima ga shugabancin kwamitin riƙon zaɓen ta na Kano.
 Shugaban ƙungiyar na 3 na ƙasa, Alhaji Adamu Musa Jahun, shi ne ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da ya yi da mujallar Fim kan dalilan da ya jawo sauyin shugabancin kwamitin riƙo na ƙungiyar a yau Litinin, 6 ga Yuli, 2021. 

Dambarwar na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin ‘ya’yan ƙungiyar ke zargin tsohon jagoran da shirin siyasantar da tafiyar ƙungiyar, wanda hakan ya saɓa da manufofin ƙungiyar. 

Da ya ke bayani kan dalilan da su ka sa ƙungiya ta ɗauki wannan mataki, Jahun ya ce, ”Waɗanda aka ba su ragamar gudanar da shirye-shiryen zaɓe, sai ya zama a cikin tafiya da ta yi tafiya a wancan lokaci aka fahimci cewa akwai waɗanda su ke da buƙatar su ma su tsaya neman kujerar shugabancin ɓangaren MOPPAN na Jihar Kano, a tsari idan zai zama cewa akwai wanda ya ya ke a matsayin jagora kuma a lokaci guda zai tsaya a matsayin neman takarar kujerar shugabanci dole zai zamo akwai gyara a cikin hidimar.

“Ba zai yiwu ka na shugabantar kwamitin zaɓe kuma a lokaci guda kai ma ka na ɗan takara ba. Dole ne ka ajiye kujerar ka ta shugabancin kwamitin zaɓe ko kuma ka ajiye kujerar ka ta hukumar zaɓe, ka dawo ka shiga takara.”

Jahun ya ƙara da cewa, “Shugabancin ƙungiya na ƙasa ya lura da irin ce-ce-ku-ce da aka samu tsakanin  mambobin ƙungiyar, wanda idan aka bar hakan ya ci gaba da tafiya a matsayin mu na shuwagabannin ƙungiya na ƙasa, to za a yi kitso ne da ƙwarƙwata. Shi ya sa mu ka yi wa abin togaciya.

Alhaji Adamu Musa Jahun

“Haka ya sa ƙungiya ta ƙara naɗa wasu shuwagabannin riƙo da za su jagoranci wannan kwamitin na zaɓe domin su ci gaba da jagoranci har zuwa lokacin da za a gudanar da zaɓe.”

Kazalika ya ce, “Kasancewar Kano ita ce kan gaba wajen gudanar da wannan harkokin namu, don duk wanda ya ke harkokin fim a ƙasar nan in dai a Arewa ya ke to dole ya na tutuya ne da Jihar Kano, duk inda aka je aka zo nan dai Kano ɗin shi ne cibiya, a nan kuma ake harhaɗa komai da komai, ko da a ce ana buƙatar abubuwa daga nan Kano dai ake ɗaukar miƙati. Shi ya sa mu ka ga cewa ya za a yi mu gyara yadda wannan zaɓe na Kano zai zamto ya tafi cikin nasara ba tare da an samu tasgaro ko kuma ce-ce-ku-ce ba duk da hidindumun zaɓe ba ka isa ka ce ba za a samu irin wannan ba domin a yayin da ka ke ƙoƙarin tsara abubuwa su ta fi daidai, a yayin ne kuma wasu su ke ganin su ba a musu daidai ba.

“Kuma dalilin da ya sa mu ka yi duba ga mutanen da su ke jajirtattu, waɗanda su ka zamto sun hidimtu kuma su na kan hidima da wannan masana’antar tamu, mu ka ga ya dace mu ba su ragamar gudanar da jagorancin wannan zaɓe domin za su iya.”

 A ƙarshe, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba uwar ƙungiya ta ƙasa za ta miƙa wa sababbin shugabannin riƙon ƙwarya jadawalin yadda za su gudanar da ayyukan su domin gudanar da zaɓen su cikin nasara.

Sababbin shugabannin riƙon ƙwarya da za su jagoranci kwamitin sun haɗa da  Nasir B. Muhammad a matsayin shugaba da kuma mataimakin sa Ishaq Sidi Ishaq.

Loading

Tags: Adamu Musa Jahunhausa filmsKannywoodMOPPAN
Previous Post

Babban Hafsan hafsoshi ya ba jarumin dirama Samanja agajin naira miliyan 2

Next Post

Kiran Ɗangambo ga marubuta: Ku tsare gaskiya, ku kare al’adun mu

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Kiran Ɗangambo ga marubuta: Ku tsare gaskiya, ku kare al’adun mu

Kiran Ɗangambo ga marubuta: Ku tsare gaskiya, ku kare al'adun mu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!