• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kannywood na da ƙarfin taya NDLEA yaƙi da safarar muggan ƙwayoyi – Buba Marwa

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
September 1, 2021
in Labarai
0
Kannywood na da ƙarfin taya NDLEA yaƙi da safarar muggan ƙwayoyi – Buba Marwa
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta bayyana cewa za ta haɗa gwiwa da ‘yan fim ɗin Hausa domin magance matsalar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.

Shugaban hukumar, Birgediya-Janar Buba Marwa (ritaya), shi ne ya bayyana haka a wajen wani taro da hukumar sa ta yi da ‘yan fim a yau a Kano.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa an yi taron a harabar gidan talbijin na ‘Kannywood TV’ da ke Kano.

A taron, Marwa ya jaddada aniyar sa ta ƙulla dangantaka mai ƙarfi tsakanin NDLEA da haɗaɗɗiyar ƙungiyar mashirya finafinai ta Kannywood (MOPPAN) domin a cimma nasara.

Marwa, wanda tsohon gwamnan Jihar Legas ne kuma tsohon jakaden Nijeriya a ƙasar Afrika ta Kudu, ya yi kira ga ‘yan Kannywood da su yi amfani da finafinan su wajen faɗakar da jama’a kan illolin shan miyagun ƙwayoyi idan aka yi la’akari da cewar fim wata hanya ce sananniya da za a iya aikawa da saƙo ga al’ummar Nijeriya.

Mahalartan taron Kannywood da NDLEA

Shugaban ya yi kira ga ‘yan fim da su haɗa gwiwa da hukumar tasa don a kawo ƙarshen annobar shan miyagun ƙwayoyi. 

Marwa ya ce, “Ina alfahari da ku. Lokacin da na zama jakada a Afrika ta Kudu, kun san jakada idan ya zo sabon ƙasa zai miƙa takardar jakadancin shi ga shugaban waccan ƙasar, sannan za a bada dama da shi da shugaban ƙasar su biyu su zauna su ɗan yi magana. Don haka mu na zama da shi, maganar farko da ya yi mani shi ne batun fim na Nijeriya. Ya nuna sha’awar shi da ƙoƙarin da mu ke a nan. Ni kuwa jin daɗi kamar na yi sama saboda irin wannan yabon da aka yi mana!

“Kuma ku ne ku ka kawo irin wannan sunan, da ku da abokanan ku na can, amma kun riga su ai.”

Ya ƙara da cewa abubuwa biyu ne su ka kawo shi Kano, wanda su ka haɗa da ziyara ga ofishin NDLEA reshen jihar don ganin yadda su ke gudanar da aikin su da yadda za a taimaka masu da kuma neman haɗin kan jama’a a fannoni daban-daban.

Ya ce, “Babu yadda za a yi a ce wannan hukuma ta zo neman haɗin kai a Jihar Kano ba mu zo nan ba. Wannan ne abu ɗaya da za ku iya zama duk wanda za ku iya zama duk abin da ku ka ga dama shi ne fim. Mai fim idan ya ga dama zai iya zama Janar Marwa a fim ko likita, da dai makamantan su, kuma dole mu da ba ma cikin wannan abu mu yaba muku saboda muhimmancin aikin da ku ke yi. 

Shugaban NDLEA, Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa, ya na gabatar da jawabin sa a taron

“Daga ƙarshe kuma ku na nisahaɗantarwa, kuma kowa ya na so ya saurari kiɗa ko fim a lokacin da ba wani aiki a gaban mutum. Don haka aikin da ku ke yi ya na da matuƙar amfani.”

Haka kuma shugaban na NDLEA ya yi tsokaci game da wasu abubuwa da su ke ci wa al’ummar Nijeriya tuwo a ƙwarya wanda hakan ya ke neman zama wata gagarumar masifa, wato matsalar shaye-shayen ƙwaya da kuma fataucin ta.

Ya ce, “Abin mamaki, mutum ya san cewa zai auka abin da zai gusar masa da ƙwaƙwalwa, zai kawo mashi matsala a zuciyar shi ko kuma a ƙodar shi, ya fita ya je ya harbe mutane ya karkashe su, kai har iyaye ma masu shan ƙwaya su na kashewa, daga ƙarshe kuma abin ya kashe mutum; abin, abin kaico!

“Yanzu a ce Nijeriya ita ce a gaba kan shan wiwi? Yanzu wannan ba abin kunya ba ne? Za a nemi cewa ko ku ne a gaba a aktin misali ko a aikin likita ko kuma kimiyya da fasaha, amma yanzu ba a nan mu ke ba; a ce mu ne shugaban duniya a shaye-shaye!

“Masu aikata manyan laifuka irin su garkuwa da mutane, ‘yan bindiga, duk shaye-shaye ne ya ke kawo wannan abin. Mutum dai da hankalin shi ba zai ce, ‘Yau bari na je na kamo yaran makaranta ɗari biyu’ ba; to kun ga shaye-shaye ne.”

Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya na gabatar da jawabin sa a taron

Ya ce, “Kannywood ku na da ƙarfin haɗin gwiwa cikin ayyukan ku. Kuma mu na son ku miƙe tsaye tare da ‘yan jarida ku gyara wannan lamari. 

“A watan Yuni, kwamanda mai kula da wannan shiyya ta Kano ya gaya mani cewa kun yi haɗin kai lokacin ranar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙasa, kun shirya wata dirama. To can Abuja mun yi wannan bikin mu ma, kuma shugaban ƙasa ya ƙaddamar da wani tsari mai suna a tashi a yi yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ya kuma umarce mu da mu tsaya tsayin daka wajen ganin mun kwantar da shaye-shaye a Nijeriya.”

A cewar Marwa, babu wata rana da za ta zo ta wuce a Nijeriya ba tare da jami’an NDLEA sun kama wasu miyagun ƙwayoyi ba tare da masu saida su, wanda hakan ba ƙaramar nasara ce ba ga hukumar.

Ya ce, “Tun daga farkon watan Janairun wannan shekara ta 2021 zuwa yanzu, hukumar ta kama irin wannan ƙwayoyi masu nauyin kilogiram miliyan 2, wanda kuma adadin masu sayar da su da mu ka kama ya fi 8,000, an kuma gurfanar da su gaban ƙuliya wanda zuwa yanzu mutane 1,600 su na kurkuku saboda wannan aikin ba ma wasa da shi.

“Wannan aikin na hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ba iya aikin hukumar NDLEA ne ba kawai, aiki ne namu baki ɗaya.”

Jarumi kuma furodusa Tijjani Asase (daga gaba) tare da mahalartan taron

Marwa ya kuma bai wa MOPPAN shawarar su kafa wata ƙaramar ƙungiya da za ta dinga yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a masana’antar ta Kannywood. 

Ya ce, “Ni na san cewa ku ababen kwaikwayo ne, a duniya gaba ɗaya iyaye su na lura da nasu fannin, amma ku iyayen kowa ne, ba naku kaɗai ba, saboda ana kallon ku a fim. Abin da ku ke shiri za a yi koyi da shi kuma a yi.

“Ku ku ne jakadun mu saboda za ku yi mutane su yi koyi da abubuwan da ku ke yi, kuma ba zai yiwu wasu su na goyon baya cikin waƙoƙin su ko cikin fim ba, dole ku nuna cewa kar a yi wannan abin a cikin waƙoƙin ku ko cikin fim ɗin ku, a faɗakar da mutane kan cewa wannan halin a yada shi.”

Kuma ya ce, “Kamar yadda na faɗa a gaban gwamna, a nan ma zan maimaita: mutanen da su ke amfani da ƙwayoyi a Kano sun kai miliyan biyu. Kuma dole a gyara wannan duk da cewa Kano ba ita ce ta farko ba ko kuma ta uku a kan shaye-shaye ba, akwai inda ya fi muni a Nijeriya, amma ko da mun ce mutum ashirin ne ai ana neman gyara. Kuma abin da ya kawo ni kenan don mu haɗu da ku a faɗakar da jama’a, musamman ku, ta hanyoyin waƙoƙi da fim don mutane su kiyayi shaye-shayen nan saboda a samu zaman lafiya.”

Tun da fari a jawabin maraba da ya yi, shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya bayyana jin daɗin sa bisa ziyartar su da shugaban na NDLEA ya yi tare da yin alƙawarin haɗa kai da hukumar wajen ganin an kawo ƙarshen sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Farfesa Abdalla Uba Adamu ya na gabatar da jawabin sa a taron

Shi ma a nasa bayanin, shugaban kamfanin Moving Image kuma ɗaya daga cikin dattawan Kannywood, Alhaji Abdulkareem Muhammad, a yayin jawabin sa ya jawo hankalin NDLEA da su zuba hannun jari wajen ganin an taimaka wa su kan su ‘yan fim ta yadda za su tashi tsaye wajen nuna wa mutane illar da wannan ɗabi’a ta ke da ita a cikin al’umma da kuma irin cutarwar da ta ke da shi.

Sarari ya ce, “Ya kamata NDLEA ta ware wasu kuɗaɗe domin sanya gasa ga mashirya finafinan Hausa don su zo da wani fim da zai faɗakar da mutane sosai kan illolin shaye-shaye.”

Haka kuma ya bayyana cewa akwai hanyoyi da yawa da ya kamata a ce wannan hukuma ta bi wajen ganin an wayar wa da mutane kai kan illolin da harkar ƙwaya ke haifarwa. 

Da ya ke jawabi, wani fitaccen malami a Jami’ar Bayero, Kano, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya bayyana cewa idan har akwai wani saƙo da ake so ya isa ga mutane yadda ya kamata, to kuwa Kannywood ba ta da sa’a wajen mabiya da masu kallon ta a Nijeriya.

Ya ce, “Domin kuwa akwai wani lokaci da aka fitar da wata ƙididdiga da ta ke nuna cewa Kano ita ce cibiyar shan ƙwayoyi a Nijeriya, kuma ƙididdigar ta na nan, mun san da haka, amma waɗannan mutane da ku ke gani su na ɗaya daga cikin mutanen da su ka sanya hannun su wajen tallata al’adun mutanen Kano, kuma maganar haka ta ke.

Janar Marwa da Dakta Sarari su na gaisawa a ƙarshen taron

“Don haka aiki tsakanin ‘yan Kannywood da hukumar NDLEA wani abu ne mai matuƙar muhimmanci domin zai samar da hanyoyin da za a tura saƙo zuwa inda ake da buƙatar aikawa, kuma mu na matuƙar farin ciki da yiwuwar haka.”

Farfesan ya kuma ce, “Abu mafi muhimmanci da ya kamata a sani shi ne Kannywood ita ce farkon masana’antar shirya finafinai a Nijeriya saboda mun fara tun a shekarar 1990 da ‘Turmin Danya’. Ita kuma masana’antar shirya finafinai ta Kudu, wato Nollywood, ta fara ne a 1992. Abin burgewa shi ne Kannywood ita ce ma’aikatar fim ta farko da ta bai wa ɗan Afrika aikin yi.

“Idan aka yi duba za a ga cewa Kannywood ita ce ta farko kuma gwarzuwa a Nijeriya.”

Ya ƙarƙare jawabin sa da cewa ya na fatan fim zai maida shugaban NDLEA na ƙasa wani jarumi a cikin wannan masana’anta.

Janar Marwa da Alhaji Abdulkareem Muhammad su na gaisawa a ƙarshen taron

Mujallar Fim ta ruwaito cewa taron tattaunawar ya samu halartar manyan baƙi da su ka haɗa da Farfesa Umar Faruq Jibril, tsohon shugaban MOPPAN na ƙasa, da mataimakin shugaban MOPPAN na ƙasa, Alhaji Sani Sule Katsina, da shugaban ƙungiyar dattawan Kannywood, Malam Shu’aibu Yawale, da kwamandan NDLEA, reshen Jihar Kano, Alhaji Isa Likita, da shugaban Hukumar Tace Finafinan ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), da kuma shugabar ƙungiyar hana sha da fataucin ƙwayoyi ta LESPADA, Jakadiya Maryam Hassan, da jarumai maza da mata da marubuta, daraktoci da mawaƙa.

Copright © Fim Magazine
All rights rights reserved
www.fimmagazine.com

Loading

Tags: Abdalla Uba AdamuAbdulkareem MuhammadAhmad SarariBuba marwahausa filmsKannywoodMOPPANNDLEASani Sule KatsinaTurmin DanyaUmar Faruq Jibril
Previous Post

‘Yan Kannywood za su yi taro da Buba Marwa da jami’an yaƙi da safarar ƙwayoyi

Next Post

KAI-TSAYE: Taron NDLEA da Kannywood

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
KAI-TSAYE: Taron NDLEA da Kannywood

KAI-TSAYE: Taron NDLEA da Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!