• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kotu ta haramta wa Murja Kunya shiga soshiyal midiya 

* Ta ba ta beli bisa tsauraran sharuɗɗa * Ta sa Kwamishinan 'Yan Sanda ya sa ido a kan ta

by MUKHTAR YAKUBU
March 26, 2024
in Labarai
0
Kotu ta haramta wa Murja Kunya shiga soshiyal midiya 

Murja Ibrahim Kunya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAR Kotun Jihar Kano da ke Bompai, Kano, a jiya ta haramta wa fitacciyar jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya yin amfani da soshiyal midiya.

Haka kuma kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta bayar da beli ga Murja kan kuɗi N500,000.

Wasu tsauraran sharuɗɗan belin sun haɗa da cewa ta kawo mutum biyu da za su tsaya mata, waɗanda dole ɗaya daga cikin su ya kasance ɗan’uwan ta na kusa yayin da ɗayan zai kasance ya mallaki ƙasa mai daraja a Jihar Kano.

Kotun ta kuma hana Murja sanya duk wani saƙo ko yin martani a kafafen sada zumunta na zamani kamar su TikTok, Facebook, Instagram da sauran su har na tsawon lokacin da za ta kasance ƙarƙashin zaman belin.

Kotun ta umarci Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar da ya riƙa bibiyar halin da jarumar ta ke ciki don ganin ba ta saɓa wa haramcin yin amfani da kafafen sada zumuntar ba.

Kotun ta halasta wa kwamishinan da ya kama jarumar tare da gaggauta miƙa ta ga kotu muddin ya same ta da ƙeta haramcin amfani da zaurukan na sada zumunta.

Kotun ta kuma bayar da umarni ga Hukumar Asibitoci ta Jihar Kano da Asibitin Kula da Ƙwaƙwalwa na Gwamnatin Tarayya da ke Dawanau su kawo wa kotun rahoton gwajin ƙwaƙwalwar Murja a cikin kwana bakwai.

Tun a makonnin da su ka gabata dai Murja ta shigar da ƙara a gaban kotun, ta na ƙalubalantar Babban Mai Shari’a na jihar.

A ƙarar da ta shigar, ta nemi a yi mata tsakani da su.

Murja ta haɗa da Alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci, Alhaji Nura Yusuf Ahmad, da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da Hukumar Asibitocin Jihar Kano da Asibitin Kula da Masu lalurar ƙwaƙwalwa na ƙasa da ke Dawanau.

Takardar ƙarar tun a wancan lokacin ta nuna cewa Babbar Kotun ta cimma muradu huɗu daga cikin jerin buƙatu bakwai da lauyoyin Murja su ka gabatar wa Mai Shari’a Nasiru Saminu.

Sai dai daga cikin buƙatun da kotun ta yi watsi da su har da ta neman mayar mata da wayar ta ta hannu ƙirar iPhone da kuma katin ATM na banki.

Haka kuma ta nemi kotun da ta sanya Asibitin Muhammad Abdullahi Wase da Asibitin Kula da Ƙwaƙwalwa na Gwamnatin Tarayya da ke Dawanau su ba lauyoyin ta rahoton gwajin ƙwaƙwalwar ta.

Bayan karanta sharuɗɗan belin sai alƙalin ya ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 16 ga Mayu, 2024.

Ana iya tuna cewa a bayan nan dai Mai Shari’a Malam Nura Yusuf Ahmad na Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kwana Huɗu, Kano, ya bayar da umarnin a yi wa Murja gwajin ƙwaƙwalwa.

Mai Shari’a Nura Yusuf ya ba da umarnin yi wa Murja gwajin ne a asibitin gwamnati domin tabbatar da ƙoshin lafiyar ta.

Alƙalin ya ba da umarnin ne bisa zargin jarumar ba ta cikin hayyacin ta a lokacin zaman kotun na farko da aka gurfanar da ita.

Tun da farko dai Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce ta yi ƙarar jarumar kan zargin tayar da hankalin jama’a, ɓata tarbiyya da kuma koyar da karuwanci.

Loading

Tags: kotuMurja Ibrahim Kunyasoshiyal midiya
Previous Post

A kawo ɗauki don magance tsadar kuɗin zuwa aikin Hajjin bana

Next Post

Abin da ya sa tsohuwar jarumar Kannywood Halisa Muhammad take neman agaji

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Abin da ya sa tsohuwar jarumar Kannywood Halisa Muhammad take neman agaji

Abin da ya sa tsohuwar jarumar Kannywood Halisa Muhammad take neman agaji

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!