• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mace-macen da aka yi a Kannywood cikin 2020

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 31, 2020
in Labarai
0
Mace-macen da aka yi a Kannywood cikin 2020
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHEKARAR 2020 shekara ce wadda a cikin ta mutuwa ta yi ragargaza a ko’ina a faɗin duniya, musamman saboda cutar korona (COVID-19). A Nijeriya, ba a taɓa samun yawan mace-macen manyan mutane ba kamar a bana.

A masana’antar finafinai ta Kannywood ma, ‘yan fim guda biyar ne su ka mutu, sannan ga iyayen wasu da su ma su ka kwanta dama, duk sakamakon rashin lafiya daban-daban. Ga sanannun mace-macen da su ka shafi ‘yan fim kai-tsaye mujallar Fim ta lissafo maku su daki-daki:

*Alhamis, 6 ga Fabrairu:Allah ya ɗauki ran Hajiya Maryam Yusuf, mahaifiyar fitacciyar jaruma Halima Yusuf Atete, a wani asibiti da ke Abuja bayan doguwar jinya da ta yi fama da ita.

*Litinin, 2 ga Maris:Mahaifin fitaccen mawaƙi kuma jarumi Umar M. Shareef, Abdul M. Shareef da Mustapha M. Shareef ya rasu. Alhaji Muhammad Shareef ya rasu ne a Asibitin Sultan da ke Rigasa, Kaduna. Shekarun sa 75 a duniya.

*Asabar, 14 ga Maris:Allah ya ɗauki ran fitacciyar jaruma Ladi Muhammad, wadda aka fi sani da Ladi-Mutu-Ka Raba.

*Talata, 21 ga Afrilu:Mahaifin fitacciyar jaruma Sadiya Muhammad (Gyale), ya rasu. Alhaji Muhammad ya rasu a gidan sa da ke unguwar Sagagi, Ƙofar Na’isa, a cikin garin Kano.

*Litinin, 27 ga Afrilu:Allah ya yi wa mahaifin masanin harkokin Kannywood kuma Mataimakin Shugaba (VC) na Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (National Open University of Nigeria, NOUN) rasuwa. Dakta Muhammadu Uba Adamu (Kantoma) ya rasu ne a Asibitin Nassawa, a Kano. Shekarun sa 85.

*Alhamis, 30 ga Afrilu:Mahaifin fitacciyar jaruma Hajara Isah Jalingo ya rasu a ‘Federal Medical Centre’ da ke Jalingo, Jihar Taraba. Shekarun Malam Isah Tidwa Jalingo 67 a duniya.

*Alhamis, 30 ga Afrilu:Allah ya yi wa fitaccen jarumi Ubale Ibrahim (Wanke-Wanke) rasuwa, a gidan sa da ke unguwar Rangaza da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a cikin garin Kano. Shekarun sa 50.

A sama daga hagu: Ubale Wanke-Wanke da Daudu Galadanchi. A ƙasa daga hagu: Ummi Lpllipop, Asma'u Ahmad da Ladi Mutu-ka-raba
A sama daga hagu: mahaifin Hajara Isah Jalingo da na su Umar M. Shareef da na Ali Nuhu. A ƙasa daga hagu: mahaifin Safiya Musa da mahaifiyar Halima Atete da ta Nasiru Auwal (Horo)

*Laraba, 13 ga Mayu:Allah ya ɗauki ran shahararren ɗan wasan Hausa Alhaji Daudu Galadanchi. Ɗan shekara 86 a duniya, ya rasu ne a gidan sa da ke unguwar Galadanchi a cikin Birnin Kano. Ya bar mace ɗaya da ɗan sa ɗaya.

*Lahadi, 24 ga Mayu:Allah ya yi wa mahaifin fitaccen jarumi Nura Hussaini rasuwa.

*Litinin, 8 ga Mayu:Mahaifin fitaccen jarumi Ali Nuhu, ya rasu a Gombe sakamakon rashin lafiya da ya yi. Shekarun Mista Nuhu Poloma 79 a duniya.

*Asabar, 12 ga Yuli:Allah ya yi wa jaruma Asma’u Adam rasuwa. Ta rasu a Asibitin Nassarawa sakamakon rashin lafiya.

*Asabar, 22 ga Agusta:Mahaifiyar jarumin barkwanci Nasiru Auwal (Horo Ɗan Mama) ta rasu a garin Gumel, Jihar Jigawa. Shekarun Hajiya Ladi Auwal 65 a duniya.

*Juma’a, 28 ga Agusta:Allah ya yi wa fitacciyar jaruma Fadila Muhammad (Ummi Lollipop), rasuwa. A cikin motar mahaifin ta ta rasu a lokacin da ake kan hanyar kai ta asibiti. Ta rasu ta na da shekara ta 27 a duniya.

*Allah ya ɗauki ran mahaifin tsohuwar jaruma Safiya Musa rasuwa a Asibitin Sojoji da ke cikin 1 Division a Kawo, Kaduna. Shekarun Alhaji Musa Makka kimanin 98.

Allah ya jiƙan Musulmi, amin.

Loading

Previous Post

Abin da zan yi da ɗaukaka nan gaba – Yusuf Lazio

Next Post

Aure da haihuwa a Kannywood cikin 2020

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Aure da haihuwa a Kannywood cikin 2020

Aure da haihuwa a Kannywood cikin 2020

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!