DUK da halin ha’ula’in da aka shiga a cikin wannan shekara mai shuɗewa ta 2020, rayuwa ba ta tsaya ba a fagen finafinan Hausa, wato Kannywood, musamman a ɓangaren iyali. Wasu ‘yan fim sun yi aure, wasu sun samu ƙaruwar ‘ya’ya.
Mujallar Fim ta binciko maku aure-aure da haihuwar da su ka shafi ‘yan fim a cikin shekarar. Ga su kamar haka:
AURE
* Juma’a, 14 ga Fabrairu:Fitacciyar jaruma Maryam Isah Abubakar (Ceeter), wato ƙanwar Mansurah Isah, sun yi aure da Alhaji Isah Usman Babba, a Kano.
* Asabar, 15 ga Fabrairu:An ɗaura auren makaɗi kuma mawaƙi Nafi’u Abdulhamid da Nana Firdausi Rilwanu, a masallacin unguwar Mahuta da ke kusa da Asibitin Ido (Eye Centre), Kaduna, a bisa sadaki N60,000.
* Afrilu, 2020:Labari ya ɓulla cewa fitaccen jarumi a shirin diramar nan ta ‘Kwana Casa’in’, Abdul Sahir, wanda aka fi sani da sunan Malam Ali, ya auri wata ‘yar siyasa mai suna Hon. Hajiya Bilkisu Shibah, wadda tsohuwar ‘yar takarar zama Sanata ce a Jihar Kaduna. Labarin ya haifar da yamaɗiɗi a soshiyal midiya, shi kuwa angon ya faɗa wa mujallar Fim cewa bai damu ba.

* Juma’a, 30 ga Oktoba:Jarumi Haruna Shu’aibu (Ubalen Danja) ya auri Nana A’isha Isah a masallacin Ɗanfodiyo da ke Unguwar Sanusi, Kaduna a kan sadaki N80,000.
* Lahadi, 29 ga Nuwamba:Fitaccen jarumi Mustapha Musty ya zama angon Ghadir Mahmud Shareef, bayan an ɗaura auren su a gidan Alhaji Ibrahim D.O. da ke Titin Jakara, kusa da Goron Dutse, cikin birnin Kano, a kan sadaki N50,000.
* Juma’a, 4 ga Disamba:Fitaccen jarumi Nuhu Abdullahi da Jamila Abdulnasir (Siyama) sun zama ɗaya, domin an ɗaura auren su a masallacin Juma’a na Alfurƙan da ke Alu Avenue, Nassarawa G.R.A., Kano, a kan sadaki N100,000.
* Lahadi, 20 ga Disamba, 2020:An ɗaura auren mawaƙiya kuma marubuciya Sa’adatu Isah Muhammad (Sa’a Vocal) da sahibin ta mai suna Haiwatu Sa’id Daud da misalin ƙarfe 11:15 na rana a babban masallacin Juma’a na Umar Bin Khaɗɗab da ke shataletalen Dangi kusa da Titin Gidan Zoo, a Kano, a kan sadaki N50,000.
HAIHUWA
* Talata, 7 ga Afrilu:Allah ya azurta jarumin barkwanci Aminu Baba Ari da samun ƙarawar ‘yan biyu.
* Asabar, 11 ga Yuli:Allah ya albarkaci tsohuwar jaruma Abida Muhammad da mijin ta da ke aikin soja, wato Mustapha Abubakar, a Legas. An raɗa wa yaro sunan mahaifin sa, wato Al-Mustapha.
A wannan ɓangare na Ranar Murna, babu abin da ‘yan fim za su ce sai Allah maimaita mana. Mu kuma mun ce amin.