TSOHON shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Abdullahi Maikano Usman, ya yi tsokaci game da hirar furodusa Abubakar Anka kan batun farfaɗo da zumunci a tsakanin ‘yan fim.
Maikano ya yi tsokacin ne a daidai lokacin da ya ga wasu daga cikin ‘yan Kannywood a cikin wani guruf mai suna ‘MOPPAN Associates’ su na muhawara kan hirar ta Anka.
Kafin Maikano ya ce wani abu, sai jarumi Nura Mado ya fara magana bayan tura hirar da wakilin mujallar Fim ya yi a cikin guruf ɗin, inda ya ce, “Ai ko yanzu ana zumunci, musamman ma in mutum ya na da kuɗi ko wata dama.”
Duk da cewa lallai ya karanta labarin ba, ya dai ga kanun ne ya yi magana. Sai wakilin mu ya ba shi amsa da cewa, “Ba irin wannan zumuncin ya ke magana ba.”
Sai ya ba da amsa da cewa, “Kowane irin zumunci ya ke magana, yanzu dai kuɗi ko wata dama su ake wa zumunci, zumuncin da an yi shi da, kuma ba zai taɓa dawowa ba sai dai a kamanta.”
Nan wani Ambasada Abdul Ismael ya yi dariya, sai Nuran ya ce masa, “Ah to, ai gaskiya ne Amb, zumuncin nan fa na industiri na da ɗin da mu aka yi, haka yanzun ma ga mu ana yin na yanzun ma da mu, ka ga kuwa ai mu na da ta cewa a kai.”
Sai Ambasada ya ce masa, “A gaskiya ni na yarda da zancen ka, saboda daga ranar da ka gani a jarida Buhari ya yi mun ‘S.A. Petroleum Down Stream’ kullum sai kira na ka ke yi mu na zumunci da ko ba ka yin hakan hhhhh.”
Mado ya amsa masa da cewa, “Ah to ai ko ina ne not only our industry, but kawai dai mu na mu ya fi worst of capitalism.”
Ya yi dariya, ya ce masa “Sure?”
Nura ya ce, “Sosai, ka sani, na sani sun sani, mun sani.”
Wannan muhawarar ce ta sa Abdullahi Maikano shi ma ya tofa albarkacin bakin sa, inda ya ce, “Salamu alaikum ‘yan’uwa. Na leƙo wannan zaure mai matuƙar muhimmanci sai na ga ana tattaunawa kan zumunci, muhimmancin sa da kuma yadda alamarin ya ke a masana’antar mu a da can baya da kuma yadda abin ya ke a halin yanzu.”
Maikano ya ci gaba da cewa, “Ni kai na a matsayi na na ɗan wannan masana’anta, na kasance a lokuta da dama ina jimamin yadda zumunci ya yi ƙaranci tsakanin mu musamman idan aka kwatanta da yadda abin ya ke a da can baya.
“Na san lokutan da ɗan Kano zai yi takakkiya zuwa Kaduna don taya ɗan’uwan sa aiki ko wata murna a Kaduna.
“Ina da masaniyar yadda ake cika mota daga Kaduna domin ba da gudunmawa ko taimako ko murna ko jimami ga wani ko wasu a Kano ko Zariya ko Sokoto, kai har ma da Jos da sauran wurare.
“Wani abin mamaki ma shi ne wani daga cikin waɗanda ake kai zumuncin da shi bai ma san wanda za a je wajen na sa ba. Zallar ƙauna ce kawai.”
Ya ƙara da cewa, “Dalilai biyu ne na ke ganin su ka haifar da haka. Na farko ƙaunar juna da son cigaban juna, sai kuma na biyu, yi domin Allah. Ina sane da lokacin da Hajiya Balaraba Ramat da Hajiya Umma su ka yi wo aiken turame ga wani biki da aka yi a Kaduna. Duk wani mai tsohuwar mujallar Fim ya zaƙulo su ya duba ya ga yadda ake tururuwar zuwa bukukuwan juna da sanya alhairi da taya juna murna. Ni ina ganin kamar abin ya ja baya. Ban sani ba ko ni kaɗai na ke kallon abin ta haka.”
Maikano ya kawo mafita, inda ya ce, “Son juna da taimakon juna da yi wa ɗan’uwa fatan alhairi na ɗaya daga cikin abubuwan da ke janyo nasara. Shin ka san yi wa ɗan’uwa addu’a ba tare da ya san ka yi masa addu’a ba wata hanya ce ta tsira da karin arziki?
“Mu so juna mu taimakawa juna. Sannan ka yi wa kowa fatan alhairi na ɗaya daga cikin mabuɗan alhairi.”
Nura Mado ya ce, “Wannan gaskiya ne ran ka ya daɗe, Allah ya saka da alkhairi ya ba mu ikon gyara zumuncin mu.”