• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 24, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Maimuna Beli ta lashe gasar BBC Hausa ta rubutun mata

by DAGA WAKILIN MU
November 8, 2017
in Marubuta
0
Maimuna Sani Idris Beli

Maimuna Sani Idris Beli

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Fitacciyar marubuciyar nan da ke Kano, Maimuna Idris Sani Beli, ita ce ta lashe Gasar Rubutun Kagaggun Labarai ta Mata mai taken Hikaya Ta, wadda gidan rediyon BBC Hausa ke shiryawa a duk shekara.

A sanarwar da gidan rediyon ya bayar, mujallar Fim ta ga an bayyana cewa alkalan gasar su uku sun zabo labarin marubuciyar ne daga cikin labarai 25 da aka tantance aka mika masu a watan jiya.

Maimuna Beli ta rubuta dimbin littattafan hikaya, wadanda su ka hada da ‘Tun Daga Tushe’ (2004), ‘Rigar Siliki’ (2015), ‘Gwanin Na Iya…’, da ‘Mafarkin Khadija’.

Balkisu Sani Makaranta, wadda ta rubuta labari mai suna “Zawarci Na”, ita ce ta zo ta biyu, yayin da labari mai taken “Sana’a Sa’a” na wasu marubuta biyu –  Habiba Abubakar da Hindatu Sama’ila Nabame Argungu – ya zo na uku.

Alkalan gasar su ne Farfesa Ibrahim Malumfashi, malami a Jami’ar Jihar Kaduna da ke Kaduna, da  fitattun marubuta biyu, wato Hajiya Balaraba Ramat Yakubu da Hajiya Rahma A. Majid.

Malumfashi, wanda masanin adabin Hausa ne, shi ne jagoran alkalan.

Lokacin da ya ke tsokaci kan labarin “Bai Kai Zuci Ba” da ya dau mataki na daya na gasar, Malumfashi ya ce sun zabe shi ne saboda “fasalin bayar da labarin da yadda ya ginu, da yadda aka fita daga duniyar da mu ke ciki aka koma lahira; daga lahirar aka dawo Najeriya, a cikin Najeriyar kuma aka bi wurare daban-daban aka gina labarin.”

Ya kara da cewa alkalan sun tafka muhawara kafin sun yanke shawara a kan labarin da ya cancanci hawa matsayi na daya, saboda duk labaran sun yi kyau.

Bugu da kari,  sun fitar da wadansu labaran guda 12 wadanda su ka cancanci yabo, kamar yadda ka’idar BBC Hausa kan gasar ta ke.

Labaran su ne:  “Garin Neman Gira”, “Hangen Dala”, “Labarin Ladidi”, “Mafarkin Uwa”, “Adikon Zamani”, “Almajiri”, “Matsalar Mu”, “Dubu ta Cika”, “Sanadi”, “Direban Hajiya”, “Tsalle Daya”, da kuma “K’arfin Hali”.

Mujallar Fim ta fahimci cewar gidan rediyon na BBC Hausa zai yi kwarya-kwaryan bikin bada kyaututtuka ga zakaru uku na gasar a ranar Juma’a, 24 ga wannan watan na Nuwamba, 2017 a otal din Sheraton da ke Abuja.

A bara ne dai gidan rediyon ya fara gudanar da wannan gasa ta “Hikaya Ta” inda marubuciya A’isha Mobil ta yi zarra da labarin ta mai taken “Sansanin ‘Yan Gudun Hijira”.

Alkalan gasar a bara dai su ne Dakta Aliya Muhammad ta Jami’ar Jihar Sakkwato, Hajiya Rahma A. Majid kuma Malam Ibrahim Sheme.

Loading

Previous Post

Kannywood ban on Rahama Sadau: MOPPAN to decide this Saturday

Next Post

An fasa yafe wa Rahama Sadau

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Rahama Sadau

An fasa yafe wa Rahama Sadau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!