• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Manufar aikin kwarmato da na ke yi wa Gwamna Ganduje – Nabraska

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
November 14, 2022
in Labarai
0
Mustapha Badamasi Nabraska

Mustapha Badamasi Nabraska

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMIN barkwanci Mustapha Badamasi (Nabraska) ya bayyana cewa muƙamin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya ba shi na mataimaki na musamman a kan harkar farfaganda muhimmin aiki ne a gwamnatance, ba kamar yadda wasu ke kallon abin ba. 

Tun bayan lokacin da gwamnan ya naɗa shi wannan matsayi dai wasu jama’a su ke ta tambaya kan ainihin manufar matsayin da aka baya shi. Wasu ma su na ganin kamar an mayar da shi wani shashasha ko wawan sarki ne fagen siyasa.

Sai dai a tattaunawar da mujallar Fim ta yi da shi, jarumin kuma ɗan siyasa ya fayyace yadda aikin nasa ya ke. 

Ya ce: “Ita wannan kalmar mutane sun san ta amma sai ya zama kamar ba su fahimce ta ba, domin ita kalmar ‘farfaganda’ ko ‘kwarmato’ ana nufin isar da saƙo ne ga jama’a. Don haka ni an ɗana ni a matsayin mataimaki na musamman a gwamnatin Jihar Kano domin yaɗa abubuwan da gwamnati ta ke so ta isar ga jama’a. 

Nabraska ya je yi wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje godiya

Saboda haka aiki na wayar da kan jama’a a kan manufofin gwamnati da kuma wayar da kan jama’a a kan ayyukan ta da kuma kare muradun ta don kusanto da jama’a ga gwamnati.”

Da mu ka tambaye shi ko menene ya bambanta shi da waɗanda ake kira ‘yan midiya kuwa, cewa ya yi, “To ai su ‘yan midiya wasu za ka same su a cikin gwamnati, amma ba su da ofis; wasu kuma da yawa ba sa cikin gwamnati, kawai dai su na yi a matsayin ‘yan sa kai, sai kuɗin ‘data’ da ake ba su. 

“Amma ni ka ga a matsayin ma’aikaci ne wanda na ke da ofis. Don haka ni fa ma’aikata kawai da ba ni da ita wadda ta ke ƙarƙashi na, amma ina da ofis kamar sauran ma’aikatan gwamnati. 

“Don haka ina da shafi na da na buɗe na S.A. Farfaganda a YouTube da sauran kafafen sada zumunta don tallata manufofin gwamnatin Jihar Kano a matsayi na na S.A. Kwarmato.”

A matsayin sa na ɗan fim, ko wanne alfanu masana’antar Kannywood za ta samu ta ofishin sa? Sai Nabraska ya amsa da cewa: “Ai kuwa ta na samu, domin idan ka kula abubuwa da dama wannan gwamnati ta Abdullahi Umar Ganduje ta yi mana mu ‘yan fim ta hanyar ofishi na, kamar ɗaukar nauyin zaɓen shugabannin ƙungiyar MOPPAN na ƙasa, samar da gurbin karatu ga ‘yan fim a ƙasar waje, ga kuma na kwanan nan da aka yi taron horas da ‘yan fim na tsawon kwanaki biyar wanda tuni an gama kowa ya karɓi shaidar sa. 

Nabraska a ƙofar gidan gwamnatin Abuja

“To, ka ga wannan ai duk daga ofishi na aka same shi. Kuma mu na nan mun ci gaba da samar da hanyoyin da gwamnatin za ta rinƙa kulawa da masana’antar Kannywood a duk wata harkar cigaban jama’a idan ta taso.”

Jarumin ya yi kira ga masu harkar fim na masana’antar Kannywood da su bayar da goyon bayan su ga tsare-tsaren gwamnati yadda za ta riƙa tafiya da su a cikin harkokin ta.

Loading

Tags: Abdullahi Umar GandujefarfagandagwamnatiKannywoodKanokwarmatoMOPPANMustapha Nabraskasiyasa
Previous Post

Rikici tsakanin jarumin barkwanci Ali Maɗagwal da surukan sa ya janyo an hana shi shiga asibitin da matar sa ta haihu

Next Post

Kakar darakta Falalu Ɗorayi, mai shekara 110, ta kwanta dama

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Falalu A. Ɗorayi tare da kakar sa, marigayiya Hajiya Nene (Amina)

Kakar darakta Falalu Ɗorayi, mai shekara 110, ta kwanta dama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!