• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Matan Kannywood sun yunƙuro domin mallakar gidaje ta hanyar bankin Mortgage

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
May 29, 2021
in Labarai
0
Matan Kannywood sun yunƙuro domin mallakar gidaje ta hanyar bankin Mortgage
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A ƘOƘARIN ta na ganin ta sama wa ‘ya’yan ta ingantacciyar rayuwa, ƙungiyar matan masana’antar finafinan Hausa (Kannywood Women Association of Nigeria, K-WAN), ta sha alwashin samar wa mambobin ta muhallin zama a ƙarƙashin tsarin bada bashin banki don mallakar gidaje.

Wannan hoɓɓasan na zuwa ne bayan wata ziyara da ƙungiyar ta kai wa shugaban Bankin Bada Lamunin Mallakar Gidaje na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria, FMBN), wato Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa, a ranar 27 ga Mayu, 2021 a ɗakin taro na ‘ R and K’ da ke Kano.

Da ta ke yi wa mujallar Fim ƙarin haske kan maƙasudin zuwan nasu, shugabar ƙungiyar, Hajiya Hauwa A. Bello (Edita), ta bayyana cewa wannan yunƙuri da su ke yi ya na ɗaya daga cikin abubuwan da su ka saka a gaba domin ganin sun samar da walwala a tsakanin jama’ar da ke cikin ƙungiyar. 

Ta ce, “Mun yanke shawarar zuwa domin mu tattauna kan yadda za mu yi haɗaka da wannan banki domin samar wa da ‘ya’yan ƙungiyar mu gidaje, wanda da iya ma’aikatan gwamnati ake ba wa bashin gidajen amma tunda aka ce ƙungiyoyi ma za su iya karɓar wa mambobin su ya sa mu ka ga dacewar mu ma mu gwada sa’ar mu domin samar wa da namu ‘ya’yan.”

Ta ƙara da cewa tun kafin su tattauna da shugaban, sun samu gurbin mutane goma da za a ba bashin waɗannan gidaje a ƙarƙashin jagorancin babban furodusa Alhaji Sani Sule Katsina, kuma hakan ya sa ba iya wannan ƙungiya ta K-WAN kaɗai ba domin duk masana’antar Kannywood sun rungumi wannan tsari hannu biyu-biyu.

Kazalika a hirar, Hauwa Edita ta bayyana wa mujallar Fim yadda tsarin biyan bashin ya ke inda ta ce, “A tsarin biyan bashin shi ne matuƙar daga shekarun ka na rubuce ba a so ya wuce shekara 60 wanda kuma shi ne ƙarshe, misali idan mutum ya na da shekara 30 ana sa ran nan da shekara 30 zai biya kuɗin gidan, idan kuma ka na da shekara  40 ana sa ran nan da shekara 20 za ka biya, sai kuma shekara 50 wanda ake kyautata zaton nan da shekara 10 mutum zai biya bashin gidan. To wannan haka tsarin ya ke.”

Shugaban bankin FMBN, Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa, tare da shugabar K-WAN, Hajiya Hauwa A. Bello (Hauwa Edita) a lokacin ziyarar

Da mujallar Fim ta tambayi Hauwa yadda ‘yan ƙungiya masu son cin gajiyar shirin za su samu, sai ta ce  “Matuƙar ka na cikin ƙungiya kuma ƙungiyar ta yi rajista da wannan banki na Mortgage, akwai wata takarda da za a ba wa mutum ya cike ta ƙarƙashin ƙungiya, sannan a je a miƙa zuwa inda ya kamata. Kuma ya zamanto ka buɗe asusu a bankin na Mortgage, wanda kuma akwai tsarin da su ke bi wajen yi wa mutane rijista da ƙungiya.

“Bayan ƙungiya ta gama tattaro takardun da aka cike, sai ƙungiya ta ɗauka ta kai wa banki.

“Kuma abin burgewa, a yayin da ake wannan abu ko sisi mutum ba zai biya ba, sai dai ma amfana da mutum zai yi.”

Shugabar Edita ta ƙarƙare bayani da yaba wa shugaban bankin na Mortagage na ƙasa da cewa, “Ya yi ƙoƙari wurin nusar da ‘yan Kannywood, ƙarƙashin Alhaji Sani Sule Katsina, wanda mu ma har mu ka samu damar zama da shi mu ka tattauna abubuwa kuma mu ka gamsu da yadda tsarin ya ke. Mun shiga mun karɓi wannan tsarin dumu-dumu domin mambobin mu waɗanda ba su da ƙarfi su amfana, tunda abu ne da kullum ake barin ‘yan Arewa a baya, ya kuma kamata a ce idan irin wannan cigaba ya zo mu dinga ƙoƙari mu na cin gajiyar sa, kar a bar mu a baya. Kuma ya kamata idan akwai dama irin wannan, kamata ya yi mu dinga amfana da ita tun da wuri.”

Waɗanda su ka halarci zaman sun haɗa da Asma’u Sani, Maryam CTV, Fati Yola, Fati Al-Amin da Hadiza Sani.

Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa tare da fitacciyar jaruma Hajiya Maryam CTV a lokacin ziyarar
Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa tare da fitacciyar jaruma Hajiya Asma’u Sani a lokacin ziyarar

Loading

Previous Post

Sau 41 aka kai wa ofisoshin INEC hari cikin shekara 2 — Yakubu

Next Post

Tijjani Muhammad Musa ya zama shugaban marubutan Kano

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Tijjani Muhammad Musa ya zama shugaban marubutan Kano

Tijjani Muhammad Musa ya zama shugaban marubutan Kano

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!