A YAU 7 ga Disamba jarumar Kannywood Rahama Sadau ta bayyana cewa ta cika shekara 30 da haihuwa tare da wallafa wasu zafafan hotuna a soshiyal midiya.
Fitaccen mai ɗaukar hoton masu harkar nishaɗantarwa ɗin nan da ke Abuja, shi ne ya ɗauke ta hotunan a situdiyon shi.
Ta yi hotunan da shigar tufafi iri biyu. A ɗaya, ta saka tsanwar doguwar riga mai walƙiya, a ɗayar kuma ta sanya riga da wando ba ɗankwali, tare da ƙaton takalmi samfurin sakadale irin na da.
Bayan haka, ta wallafa bidiyo guda biyu tare da kiɗa da waƙar mawaƙin ƙasar Indiya da ake yayi mai suna Tanishk Bagchi.

Kamar ko yaushe, waɗansu masu bin shafukan ta sun yabi shigar tata, amma wasu na suka tare da nuna mata cewa ta yi shigar da ba ta dace da Musulunci ba.
Kyakkyawar jarumar ta kuma yi rubutu inda ta bayyana murnar ta dangane da wannan rana.
Rahama ta yi la’akari da cigaban da ta samu a shekarun nan da ta yi a doron ƙasa tare da bayyana godiyar ta kan dukkan soyayyar da ake nuna mata da irin damarmakin da ta samu.
Haka kuma ta yi addu’ar Allah ya sa wannan shekara da ta shiga da ma shekaru masu zuwa su kasance cike da so da ƙauna, farin ciki mai ɗorewa da kuma lafiya, sababbin hanyoyin ƙarin arziki da al’amurra.
Da Turanci ta yi rubutun, ta ce: “THIS IS 30. HAPPY BIRTHDAY RAHAMA SADAU.
“I’m grateful for all the love & opportunities I’ve had to grow and develop these past years.
“I pray for this year & the coming ones to be full of love, eternal happiness, good health, good fortune, new opportunities experiences.
“May Almighty Allah in his infinite mercy grant everything I’ve ever wished for and more.
“May HE continue to shower his countless blessings on me & mine. Ameen thumma Ameen.”
Ga hotunan da ta wallafa ɗin nan.