• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Na san zai iya abin da ya fi hakan, inji mawaƙi Baban Kausar kan kyautar mota da El-Mu’az ya yi masa

by DAGA ABBA MUHAMMAD
May 31, 2022
in Labarai
0
A sama: Sagir Baban Kausar (a hagu) tare da El-Mu'az Muhammad Birniwa. A ƙasa kuma motar da aka yi kyautar da ita ce

A sama: Sagir Baban Kausar (a hagu) tare da El-Mu'az Muhammad Birniwa. A ƙasa kuma motar da aka yi kyautar da ita ce

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SANANNEN mawaƙin nan da ke Kaduna, Sagir Ɗanyaro (Baban Kausar), ya bayyana fitaccen mawaƙin siyasa El-Mu’az Muhammad Birniwa da cewa shi mutum ne da ya ke iya yi wa mutane hidima da duk abin da ya ke da shi ba tare da ya damu ba, kuma “mai irin wannan hali duk abin da ya yi ba zai zama abin mamaki ba.”

Baban Kausar ya faɗi haka ne a hirar da ya yi da mujallar Fim sakamakon kyautar dalleliyar mota ƙirar Ford (samfurin Focus) da aminin nasa ya yi masa a yau.

Baban Kausar da kan sa ya sanar wa da duniya wannan abin arzikin da aka yi masa a shafin sa na Instagram, inda ya rubuta: “Alhamdu lillah! Layi ya zo kan mu, El-Mu’az Muhammad Birniwa ya gwangwaje ni da mota ƙirar Ford Focus.”

Ya biyo sanarwar da roƙon cewa, “Allah ya saka masa da gidan Aljanna, Allah ya ƙarfafa gaban sa da bayan sa, ya ƙara buɗe ƙofofin arziki, ya tsare masa mutuncin sa don mutuncin Annabi Muhammadu (S.A.W.).”

Da wakilin mujallar Fim ya tambayi Baban Kausar abin da zai ce game da wannan kyauta ta El-Mu’az ne ya ce, “To, da farko dai ina miƙa godiya ga Allah maɗaukakin Sarki a bisa doron ikon sa wannan kyautar ta wanzu.

“Sai kuma in ƙara jeranta salatuka ga fiyayyen halitta, Annabin farko da ƙarshe (s.a.w.), wanda bisa gwadaben soyayyar sa mu ka haɗu a matsuguni guda, mu ke rayuwa tare a matsayin aminai kuma abokan sana’a.”

Ya ci gaba da cewa, “Duk mutumin da ka ce ya kawo maka na kusa da El-Mu’az Birniwa a Kaduna, ina da yaƙinin sai ya harsaso ni a cikin mutane ukun farko. A haka mu ke rayuwa tsawon lokaci, har wasu na tunanin ko mu ‘yan’uwa ne na jini saboda kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin mu.

“Allah maɗaukakin Sarki ya fifita shi a kan mu, ko in ce ya ɗaukaka shi sama da mu. Hakan bai sa ya wulaƙanta mu ba; a haka dai mu ke ta rayuwa tare.

“Haka ya sa ban yi mamaki ba da ya ce ya saya min mota saboda na san zai iya abin da ya fi hakan. Ko yanzu ai mu uku ya saya wa motar. 

“Shi mutum ne da ya ke iya yi wa mutane hidima da duk abin da ya ke da shi ba tare da ya damu ba. Mai irin wannan hali duk abin da ya yi ba zai zama abin mamaki ba.

“Fata na Allah ya yi masa jagora a cikin lamarin sa, ya kare gaban sa da bayan sa. Allah ya sa Aljanna makoma gare shi da mu baki ɗaya.

“Allah ya jiƙan magabatan mu, ya sa su na kyakkyawan matsayi, alfarmar Annabi Muhammadu (s.a.w.).”

Ɗimbin mutane sun taya Baban Kausar murnar wannan kyauta da aka yi masa.

Shi da El-Mu’az dai duk mazauna garin Kaduna ne.

Loading

Tags: El-Mu'az Muhammad BirniwaKannywoodkyautamawakamotaSagir Baban Kausar
Previous Post

Yawancin masu zagin mu ‘yan fim mun fi su asali – Hannatu Bashir (Hanan)

Next Post

Rage raɗaɗin fatara ta hanyar ciyar da ‘yan makaranta

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Minista Sadiya Umar Farouq ta na raba abinci ga yara 'yan makaranta

Rage raɗaɗin fatara ta hanyar ciyar da ‘yan makaranta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!