• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Raliya, ɗiyar tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan, ta cika shekara ɗaya

by ABBA MUHAMMAD
November 6, 2025
in Ranar Murna
0
Raliya, ɗiyar tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan, ta cika shekara ɗaya

Hajiya Fati Ladan rungume da Raliya a wurin taron murnar zagayowar ranar haihuwar yarinyar tare da ɗimbin yara mahalarta

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAU Alhamis, tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Fati Ladan, ta shirya wa ƙaramar ‘yar ta Raliya (Ihsan) bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta, inda ta cika shekara ɗaya a duniya.

An gudanar da bikin a farfajiyar gidan su da ke Yerima Close, kan Titin Jinya, daura da Titin Kanta, Kaduna.

Bikin, wanda aka fara da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, ya samu halartar ƙawayen Fati da kuma matan abokan mijin ta, Alhaji Yerima Shettima, da ‘ya’yan su.

Da yake bikin na yara ne, mai gabatarwa, wato kakakin magana (MC), Ibrahim Alhassan, ya gabatar da gasar rawa a tsakanin yaran inda ake kiran namiji ɗaya, mace ɗaya a saka masu waƙa su yi rawa. Wanda ya fi iya wa, shi ne zakaran.

Sai dai fa mata sun ba maraɗa kunya, domin su ne suka lashe gasar da kusan kashi 95 cikin ɗari, ciki har da babbar ‘yar Fati, Humaira.

Bayan nan, sai kuma aka shiga fagen goge wuya, cin maƙulashe, inda kowa ya ci gasashhen naman rago da sauran abubuwan sha.

Daga nan kuma sai aka yanka kek tare da yin hotunan Ihsan da mahaifiyar, yara da kuma iyayen su.

Raliya Shettima (Ihsan) a hannun mahaifiyar ta a wurin bikin

Bayan kammala hotunan ne Fati Ladan ta yi jawabin godiya ga dukkan mahalarta taron inda ta ce, “Ina godiya matuƙa da irin ƙaunar da kuke nuna min. A duk lokacin da zan yi abu, kuna ƙoƙarin halarta. Na gode sosai. Allah ya maida kowa gidan sa lafiya.

“Iyayen yara da yara sun nuna farin cikin su da wannan bikin, domin sun cashe sosai.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa an haifi Raliya a ranar Talata, 5 ga Nuwamba, 2024, a asibitin sojojin sama (Air Force Base) da ke Mando, Kaduna.

Allah ya raya Raliya, ya albarkaci rayuwar ta.

Yara suna cashewa da rawa a wurin bikin

Loading

Tags: Fati LadanRaliyaYerima Shettimazagayowar ranar haihuwa
Previous Post

Khadijatul Iman Sani Musa Danja ta burge mahalarta bikin zagayowar ranar haihuwar ta

Next Post

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

Related Posts

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa
Ranar Murna

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa

September 28, 2026
An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff
Ranar Murna

An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff

September 7, 2026
Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya
Ranar Murna

Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya

September 5, 2026
Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Yadda marubuciya Aunty Baby ta yi bikin cikar shekara 51
Ranar Murna

Yadda marubuciya Aunty Baby ta yi bikin cikar shekara 51

August 19, 2026
Next Post
Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-'yan-bori a kasuwa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!