WANI kamfanin harkokin nishaɗantarwa da ke London zai karrama babban furodusa a Kannywood, Alhaji Abdulkareem Mohammed, a watan Yuli.
Kamfanin mai suna SRTV Media Limited ya faɗi haka ne a takardar da ya aika wa Abdulkareem ɗauke da kwanan wata 26 ga Maris, 2024 wadda mujallar Fim ta samu kwafen ta.
Kamfanin ya sanar da shugaban na Moving Image Communication Limited, Kano, cewa zai karrama shi a taron Makon Nijeriya (Nigeria Week) da lambar girmamawa ta Nasarar Rayuwa (Life-Time Achievement Award).
A takardar gayyatar mai ɗauke da sa-hannun shugaban kamfanin, Ogbevire Christian Ashaiku, kamfanin ya ce, “Abin alfahari ne da jin daɗin mu mu sanar da kai cewa ƙungiyar mu ta yanke shawarar karrama ka da lambar yabo ta Nasarar Rayuwa a Makon Nijeriya, London, 2024, wanda aka shirya gudanarwa a Prestigious Lighthouse Theatre, 262/274 Camberwell Road, London SE5 0AY daga Yuli 22 zuwa 28, 2024.
“Wannan karramawa ta kasance don kyakkyawan jagorancin da kake bayarwa yau da kullum, ƙwararrun ɗabi’u da rawar da ka ke takawa don nuna kishin ƙasa da kuma cigaban masana’antar finafinai ta Nijeriya.
“Za mu yi amfani da wannan dama wajen sanar da kai cewa an tantance ka a cikin waɗanda za su halarci taron finafinai na Birtaniya da Nijeriya da aka tsara don magance ƙalubalen kuɗaɗe, baje koli, rarrabawa, samarwa da haɗa kai tsakanin Birtaniya da Nijeriya a Makon Nijeriya, London 2024.
“Bikin karramawa na SRTV Recognition Awards wani muhimmin ɓangare ne na Makon Nijeriya, London, wanda aka tsara musamman don a karrama tare da yaba wa ‘yan kishin ƙasa, musamman na Nijeriya, da kasuwancin Nijeriya a Nijeriya da kuma ƙasashen waje.
“Makon Nijeriya a London wani haɗaɗɗen taron nishaɗi ne da harkokin kasuwanci da aka tsara domin baje kolin al’adun Nijeriya masu tarin yawa.
“Ana gabatar da shi a matsayin taron shekara-shekara na tsawon mako guda wanda zai gudana a Birtaniya.”
A taron za a yi baje-kolin nau’o’in abinci, finafinai, fasaha da al’adu na Nijeriya, kayan kwalliya, da kaɗe-kaɗe.
Haka kuma za a gudanar da taron ƙoli na tattalin arziki da baje-kolin kayayyakin amfanin gona da dama na Nijeriya.
Mashirya taron, waɗanda ‘yan asalin Nijeriya ne da ke zaune a Ingila, su ka ce wa Abdulkarim: “Mu na yi maka gayyata ta musamman zuwa Bikin Bada Kyauta da za a yi a ranar 27 ga Yuli, 2024 a gidan wasan kwaikwayo na Lighthouse da ke Camberwell Road, London SE5 0AY.”